← Book details Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 29

Sashe 24

Rufaidah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya tabbatar. Aishatu tace Fadila nasan zan dade ban kara yarda dake ba don na biyu kenan abinda kika yi min. Amma darajar abinda ke cikinki muna rokonka ka taimaka maganar sakin ka janye. Idan ta sake yi maka laifi nayi alqawari bazan shiga ba. Fadila ta rungumeta ta tana ta godiya. Shi kuwa fita yayi. A sanyaye ta bishi daki yana zaune bakin gado ya dafe kai. Aishatu ta zauna a kusa dashi ta dafa masa kafada. Baby ka gode Allah sharrinta baiyi tasiri a kanmu ba da yanzu zuciya ta debe ni kila nice zan nemi sakin. Yayi saurin rufe mata baki. Allah Ya kiyaye Aish...tace to tunda hakan bai faru ba ya kamata mu nuna godiyar ga Allah ta hanyar yafe mata. Ka kara hakuri ko don darajar yara. Yace yanzu kin yarda na dawo da ita. Ta gyada kai don tsakani da Allah tana tsoron Fadila. Amma tana kwadayin ladan da ake bawa mai yawan afuwa idan an cutar dashi. Ya kankameta yana mata magana a kunne Aish it seems kina so sonki yayi min yawa a raina. Ke wace irin mace ce? Ya shafi fuskarta...you are too nice, too good. And Dr Rano loves you so much for that. Ita ma tace and I love you too. Ban taba tunanin zanyi aure namiji yaga darajata ba sai gashi ka zama sanadin gushewar duk bacin ran da na kwaso a baya. Duk da halin da nake ciki baka guje ni ba baby ta yaya zanyi sanadiyar raba maka iyali? Yace Alhamdulillah itama ta maimaita suka manta da Fadila da ke daki tana waya da Fahad. Wasila ce ta turo mata numbarsa ta kira. Cikin isa da gadara tace masa sunana Fadila matar mijin tsohuwar matarka. Idan har kana sonta har yanzu ka zo mu hadu. Fahad yace ke kinsan da wa kike magana kuwa kike nema ki rinka bani order kamar yaronki? Ta tabe baki ba Fahad bane. Yayi wata yar dariya shine, ya kamata ki san ba'a yiwa fahad magana a haka. Idan kin shirya ki sanar dani wurin da zamu hadu. Sai kawai ya kashe wayar. Ta tsaya tana kallon wayar a hannunta tana juyata. Shi kuma wannan waye ta fada a zuciyarta. RASHIN GODIYA ✂ 47 Aishatu ta rude jikinta na rawa tace Anti Sauda me zai sa ya kira ni haka kawai. Anti Sauda tace kinga kwantar da hankalinki in Allah Ya yarda ba komai. Ita dai Aishatu hankalinta bai kwanta ba sai da aka goge mata jiki ta tashi jikinta duk ba kwari. Anti sauda tace kina zuwa gida ki sanar da Dr don daga labarinsa ni ko kadan ban yarda dashi ba. Aishatu tace ai dole anti. Ni sam ban yarda da rufa rufa ba. Fahad mugun makiri ne ga iya hada sharri. Suna magana suka fito waje, dama gidan babu nisa da na Anti sauda a kasa suka je. Fadila tana zaune gaban motar Huzaifa ya daukota daga gidansu tace Abban Aliya mu biya mu dauko Aishatu naga jiya irin lokacin nan ta dawo. Huzaifa yayi tsaki bana son iyayi, ta sanar dake inda zata ne da kike cewa a daukota. Ko kuwa son jin kwaf ne ya motsa kike neman bugun cikina. Fadila ta sunkuyar da kai, nasan duk abinda nayi ne a baya yasa komai nayi yanzu sai ka fassara shi da wata manufa. Shareta yayi don yasan son jan zancen take. Ya dauki wayarsa ya kira Aishatu dama niyarsa kenan su biya a daukota tunda yamma tayi. Ta fada masa ta gama zata jira ta koma gidan anti Sauda. Fadila na jin haka ta dauko wayarta ta tura text. (Tana gidan nan da na kwatanta maka a yan kaba. Kayi sauri muna hanya) Baiyi mata reply ba ya cigaba da kallon gate din gidan da Aishatu ta shiga daga cikin mota. Ta kara kyau da haske...sai yanzu ya kara ganin wautarsa akan yadda yayi treating dinta a gidansa. Yaro ya gani zai wuce yayi saurin fita daga mota ya tsayar dashi. Don Allah kace Aisha tazo inji Huzaifa. Ka fada mata tayi sauri wayata ce ta mutu. Yaron ya shiga ya fadawa Sajida sakon ta shiga dakin mamanta ta fada musu. Aishatu ta tayi saurin gyara fuska Anti Sauda sai dariya take...na dai fada miki amarcin nan sai an gama gyaraki. Na fuskanci Huzaifa ya gama koya miki rashin kunya idan ban kaiki ba zaki kai kanki. Aishatu ta rinka dariya suka fito tare. Anti Sauda tace gori zan masa har yau bai taba shiga gidana ba. Basu ga motarsa a bakin gate ba har Anti Sauda na cewa ko dai tafiya yayi wani wurin kila yanzu zai dawo. Sam bata kula da yadda Aishatu ta sandare a tsaye ba. Hannunta taji ta damka har ta danyi ihu ke lafiya zaki karya ni. Kamar me rada ta nuna mata mutumin da yake tahowa wurinsu. Anti Sauda tace waye wannan? Ko Fahad ne? Aishatu ta gyada kai alamar eh. Assalam alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Anti Sauda ta sha kunu ta amsa da kyar sannan ta rike Aishatu shige muje ciki. Fahad yace don Allah Haj ki daure ku saurare ni. Abinda ya kawoni yana da matukar mahimmanci. Aishatu ta juya a fusace yayi saurin cewa don girman Allah ki tsaya. Ba tare da ta juyo ba ta tsaya. Kan gwiwoyinsa biyu ya durkusa ki yafe ni Aisha. Ni mai dumbin laifi ne a gareki kuma wallahi ban taba jin son mace ba sai da na rabu dake. Nayi nadama mara iyaka kuma tun a duniya naga sakayyar abinda nayi miki tana faruwa a kaina. Sai hawaye suka fara zuba a idanunsa. Ya kalli Anti Sauda ki taimaka ki bata hakuri ko zanga sassauci a rayuwata. Bani da wani burin da ya wuce ki furta da bakinki kin yafe min. Duk maganar da yake kin juyowa tayi. Tana tuna irin wahalar da ya rinka bata ciki harda zubar mata da ciki sau biyu. Anti Sauda tace ni abinda ya bani mamaki ya akayi kasan tana gidan nan. Yayi murmushi ki roketa ta yafe min sai kuji abinda ya kawo ni. Wallahi Aishatu bazan kara cutar dake ba. Ina tsoron lahirata, ina tsoron wutar Allah, ina kunyar haduwa da Mahaliccina. Ta dan juyo na yafe maka amma don Allah ka dena bibiyata haka. Ya tashi yana kade rigarsa nagode sosai Aisha. Sai kuma mu koma ga abu na biyu da ya kawo ni....kafin yayi magana suka ji wani mahaukacin horn. Dukkansu basu tun san lokacin da Huzaifa yayi parking mota yana kallonsu ba. Ransa ya gama baci ji yake kamar ya shake fahad don ya tabbatar shine saboda haduwar da sukayi a kofar gidan su Aishatu. Zuciyar Aishatu kuwa don tsoro da fargaba kamar ta fito waje RASHIN GODIYA ✂ 48 Gaba daya Aishatu ta rikice ta ma kasa motsawa. Huzaifa ya fito daga motarsa a fusace ya janyo hannun Aishatu. Anti Sauda tace Dr kayi mata a hankali bamu san yana wurin nan ba. Tamkar ba da shi take magana ba haka yayi gaba abinsa. Fahad bai ce masa komai ba har ya tada kura suka wuce. Anti Sauda ta yiwa fahad kallon banza. Ince ko kaji dadi ka hada rigima. Aishatu tana fada min sharrinka sai yau �a tabbatar. Mai yasa baka yi masa baya�in abinda ya kawoka ba. Fahad ya�i murmushi tare da dan tabe baki saboda kishi mana. Anti Sauda ta yu hanyar gate din gidanta a fusace Allah wadaran �alinka. Fahad yace please ki saurareni. Maybe na iya fitar da kawarki daga zargi. Na tsaya sauraronka nima nawa mijin ya dawo ko. Sannu mugu to ta Allah ba taka ba. Ta s�ige tare da bugo gate din da karfi. Kana ganin yanayi Huzaifa kasan bashi da kwanciyar hankali. Babu abinda shaidan bai kitsa masa ba a zuciyarsa. Wai garin yaya ma Fahad yasan gidan Sauda? Kuma ya akayi yasan inda Aish take a wannan lokacin? Fadila ta dan juya baya inda take jin sautin kukan Aishatu a hankali. Aishatu wai me ya faru ni kun sani a duhu. Kaima Abban Aliya meye na fushi bayan baka kirata ko kayi mata horn ba tunda muka zo. Ai kaga ba laifinta bane don bata taho da wuri ba. Mtsw kuma maza da rigimarku. Shiru babu wanda ya kula ta. Ta sake cewa Aishatu waye mutumin nan ko dan uwanku ne. Na tuna shi a wurin walimarki yana ta miki liki. A fusace Huzaifa yace to uwar jaraba kina mota har �i� kare masa kallo...tayi saurin daga hannuwa sama yi hakuri na yi tunanin ko dan uwanta ne ko mijin wannan matar. Daidai lokacin da ya shiga gidan mal habu na rufe gate Fadila tace kai amma fa Ais�a j�ninku mai karfi ne don kuna dibar kama da mutumin nan. Hancinku yayi....wani irin burki Huzaifa ya taka saboda yadda ya harzuka. Yace Fadila idan bakiyi min shiru ba zan tattaka ki wallahi. Tayi dariya Aishatu yau angonki sai a hankali bari na barku. Ta fice abinta ta shiga ciki. Aishatu ta dago kai suka hada ido ta mirror din gaba yace kema ki fita. Ta soma magana baby ka saurare ni wallahi...katse ta yayi da tsawa Aishatu ki fita nace, am not in the mood. Bai taba fadar sunanta ba sai yau. Yau ma cikin bacin rai. Ba musu ta fita yayi ribas da motar ya rinka danna horn har mal habu ya fito da gudu daga bandaki ya bude masa gate ya fice. Aishatu ta shiga ciki tana kuka. Komai yayi mata zafi. Ta tabbatar plan Fahad ya hada tunda cewa yayi tazo inji Huzaifa. Komai yayi mata zafi ta shiga daki ta takure akan gado tana kuka a hankali. Ba ita ta tashi ba sai da taji kiran magriba. Fadila tana kallon yadda Huzaifa ya fita ta tafa hannuwa. Wannan karon ko kinfi kuda naci Aishatu sai kin koma inda kika fito. Ta kira wasila suka sha hira hankali kwance. Masallaci daya suka yi sallah. Sai da ya jira ya gama gaisawa da mutane ya fito sannan ya biyo shi waje. Sallama yayi masa mutum ya amsa cike da nutsuwa. Sai yace kamar Dr Rano ko mijin Aishan Sauda? Eh nine ya dan saki fuska. Don Allah magana nake son muyi. Gefe suka koma
Chapter 24 · 0% Book details