← Book details Nida Dalibata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 42

Sashe 42

Nida Dalibata Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Babu musu ko gaddama Hafsat ta biye masa suna mugun romancing juna kamar zasu cinye juna ganin zai wuce iyaka yasa ta tsaidashi,cikin dubara tace naji ana kirana k'ila babynka ne ke kuka bara naje nan ta fita tabar sir zaune yawani lumshe ido.

Tana fita ta had'e da mama zata kawo babyn yana kuka,hamdala tayi dan da mama tasamesu a cikin wannan yanayin ai kashinta yabushe .mama tace ina zaki naga kinfito?"cikin in'ina tace dama yaya ne yaxo yanxun yace na karbosa yagansa mik'amatashi tayi had'e da cewa to wlh kibidai ahankali banda zama gab da juna inma naji shiru zaku ganni ,cikin jin kunya Hafsat ta ce to mama kinsanma hakan bazai faruba. girgiza kai maman tayi ta wuce ,Hafsat ta koma dakinta.
Tana shiga ta azamasa babyn acinya ,had'e da yin ajiyar zuciya ta zaiyyana masa fitarta kenan ta had'e da mama.
dan zaro ido yyi yace oh sulti dataganmu da wlh naji kunya,barama nagansa na wuce ainarage zafi.
Nan yayita kallon babyn yanajin sonsa da k'aunarsa kissing insa yyi yace sulti nah dani da babyn nan wakikafi so?
"Murmushi tayi tace Wanda nafara samu shinake do", ahankali yace nima haka sultina ALLAH yabarmu tare kingama mun komai arayuwata nidake mutu karaba.lallai danabi zugar wata zuciyar dke cemun kada kaso dalibarka,yau gashi NIDA D'ALIBATA har munyi aure mun haihu ikon ALLAH kenan.
Cikin jin dadin kalamansa ta sumbacesa agoshi had'e da karbar yaron tana cewa yaya kaje kada mama tashigo,hancinta yaja had'e da shafa kanta yyi wa yaron da ita kiss yace kikulamun daku sai munyi waya,cikin shagwaba taje yanxun inkafita inazakaje?
" ahankali yace zance",wata harara ta galla masa had'e da cewa kai mijin mace d'aya ne tunda kai subutar baki ka fad'a a first night dinmu.
Murmushi yyi yace to maida wuk'ar ,in inatare dke duk sauran mata kallon maza nikemusu ,insha ALLAH kece anan duniya kuma a aljannah matata kedaya.murmushi tayi mai sauti had'e da dagamasa hannu har yafita.

Adaren ranar sunsha kalaman love awaya ,sun raba dare suna firar su ta masoya har bacci yasace Hafsat,jintayi shiru yagane tayi bacci yakashe wayar ya kwanta cike da farinciki.

********************

Hakafa aka cigaba da zaman jego ,kwanci tashi har yau Yakama suna.

Inda yaro yaci Suleiman ,sunan daddy suna kiransa da khalifa.

Mejego da kawayenta ko ince yan uwanta su Fatima sunsha kyau har sun gaji inda gidan cike yake da jama'a ga mai DJ a compound din gidansu yasaki kid'a.

"Anci ansha me jego tasami kyaututtuka gun ja'ama."

Uban gayyar kuwa har walima yashirya shida friends dinsa.

Hakafa taro yatashi lfy inda akabar me jego tacigaba da wankanta agidansu,tana samun kulawa itada babyn sosai agun mama .

Kullum sai sir yazo sau 2yagansu , safe da dare yakamusu wannan yakamusu wancan,sannan susha romance dinsu.

Koda mama ta lura da yadda sir kedokinsu aisai tashiga tsima yartata da gyarata ,kai harsu dulka akamata .

Aranar datayi40ta koma ,hmmm kada kuso kuga irin rawar kan da sir yyi ai ranar abun ba magana ,har kukan dad'i sir yyi.

__________________
Haka rayuwa tacigaba da kasancewa inda khalifa yyi bulbul dashi dan fari yyi wayo ga yaron da farin jini kamar ubansa.

Ayanxun watansa ukku kuma sir yamaida Hafsat skul yanaso tazama koda nursing ne.

Inda sa'ada,tahaifi yarta mace kafin suna Fatima ta haifi d'anta nmj ,bayan sunyi 40zakiyya tahaihu itama mace.

Haka zamansu yakasance cikin farinci da yadda da juna .

Inda sir yaje har gombe yyi binciken dangin maman Hafsat ,yadawo yahadasu da mama kuma yataimaka musu.

Bayan shekara5

gidan alhj Suleiman rabo na l'eka tun a compound din gidan naga yara sunkai 14suna wasansu ,amma daya na gefe kamar babushi agun.

Wata yar baby gils ce tazo gabansa tana cewa yaya khalifa kaga arfat tana Jana ,yatsina fuska yyi yace to ai ance kudena kunki,bacemun dagani .da gudu tayi cikin babban parlon gidan .

Hafsat ce zaune kan kushin ta aza k'afa daya kan daya tana kallon tb.araina nace masha ALLAH su Hafsat anxama manyan mata tayi k'ara haske da y'ar k'iba jikinnan yyi fresh .yarinyar na xuwa ta fada ajikinta tace many kinga arfat na Jana,nagayawa yaya khalifa yakoreni.

Tsaki Hafsat ta ja tace rabu da shi Yaro sai shegen miskilanci ntsiya har yace ma daddy n Ku be iyaba tun yana yaro inaga ya girma,kiyi hkuri zanzane arfat kinji.....

Sir ne yashigo dakin cikin nutsuwa ,yakara girma yazama babban mutum matashi mai ji da naira had'e da ilimi uwa uba kyau ga shi Dan gata agun matarsa.yara biyune ahannunsa ,wsu sun biyoshi abaya ,zama yyi kusada Hafsat yana murmushi had'e da cewa sulti nah ,gida zamuje yanxun.

Cikin shagwaba ta ce ,um um bamu dadeba fa,kuma mommy ta na ciki tayi bak'i,aibana tafi ba bbu sallama.

Hancinta yaja yace har yanxun bazaki girmaba ko?kinada yara4amma kina shagwaba.radamasa tayi tace aini yar yarinyace agunka.

Murmushi yyi yace eh hakane,aiyanxunma xuwa nayi muje ki sallameni yafad'a had'e da kashe mata ido d'aya.

Yaran dasuka shigo su Tara ,wato 3na kabeer 3na sa'ada,3na Zakiyya, yace my children yanxun kuma ,za azo daukarku.

Khalifane yaja kannensa ,arfat dkeda sunan mommy, minal da kuma yusuk suka wuce gun motar sir suka shiga ,sauran yaron nata wasansu a compound din gidan.

Sir ya mikar da Hafsat yana cewa sulti muje in mommy ta ji shiru tasan muntafi ,murmushi tayi tace to mijina...

TAMAT BI HAMDULIILAHI

Anan nakawo karshen Wannan labari, kuskuren danayi acikinsa yah ALLAH kayafemun.

Ina mik'a godiyata sosai ga....

Nida d'alibata fans grp,1,2&3.

Muhad'a kammu writer's association

Amintattun mata writers association

Tap ten Hausa novels

Sadnaf novels

Mubeenah fans

ramin mugunta fans

Novels &kitchen grp

Yasmin Hausa novels

da duk sauran grps din da ake posting wannan novel na gode sosai.

Afuwan!Afuwan!!Afuwan!!!

Yaro ko babba duk Wanda na batama rai akan wannan novel ina rokan yafiyarku.

Nagode!, nagode! Nagode!

ga dukkan wad'anda suka fara bina tun farkon fara wannan novel harxuwa wannan lokaci, sai mun had'e a sabon novel d'ina mai xuwa insha ALLAH.

Akarshe nasadarkar da wannan littafin gareki,yar uwa k'awa ,aminiya,AMEERA marubuciyar K'ASATA, kinfi kowa son NIDA D'ALIBATA kiyi yadda kkso dashi, mallakinkine halak malak na gode...
Chapter 42 · 0% Book details