← Book details Nida Dalibata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 42

Sashe 12

Nida Dalibata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ayanxun gaba daya skul din suna shakkar taba Hafsat ko a tape taje taga ss 3 da yawa da sauri zasu janye bucket dinsu suce ta Tara nata.

Sbd sun tsorata da abinda yafaru ga Pripet .

Hafsat kuwa hankalinta kwance har yar kiba da haske tayi.

Yau kasancewar ba a yin assembly, duk suna zaune a class. kafin lokacin lesson yyi.

Kamar dg sama Hafsat taji muryar sa ada ,ta nacewa sister Hafsat!

Da sauri Hafsat ta tashi tayi hugging dinta,suka fito dg class din .

Sa ada tace yanzun nazo kawoma yaya break nace kina ,ina yace kina class dinku,shine natambayi wata ta nunamun.

Murmushi Hafsat ta yi tace allah sarki ,rannan nacewa sir yagaidamunke da mommy.

Zaro ido saada tayi tace oh wlh be fadaba aiko zan sanar da ita.

Hafsat tace skul zakima ko? Sa ada. Tace eh nimafa ss2 nake ,Hafsat tace Ashe mu duk mate ne,.......

Shiru tayi jin kamshin turaren sir Aliyu, kafin ta dago taji yace to sarkin surutu oya muje kada ki yi latti.

Murmushi sa ada tayi tace my friend promise in anyi Hutu zakijegidanmu,?

D'agowa Hafsat tayi tasaci kallon sir Aliyu, taga ita yake kallo yanaso yaji amsar da zata ba sa ada.

Kallon ta tayi tace ah ah saidai ke kifara zuwa gidanmu tukum, murmushi sa ada tayi tace ai nacewa yaya yakaini yace besaniba.

Hafsat tace inkin sake dawowa zan kwatantamiki.

Nan sa ada ta c e to shikenan,bara na tafi,nan ta juya harda dan gudunta.

Hafsat ta kalli sir Aliyu tace yaya ina kwana ?

Hararar ta yyi yace bazan amsaba ,da sauri tace meyasa? yace sbd kink'i fadamun maganar da kkikace zaki fadamun.

Dannace miki yar kauye kki fasa ko?

Murmushi tayi tace lah dama godiya zan maku akan....

Da sauri yatari nunfashinta yace ah ah ba godiya atsakanummu.

Ki tafi class maza,jibi zaku fara first C A test kije kiyita karatu,kinji yar kanwata.
Kallonsa tayi cikin shagwaba ta ce yayanah promise,zaka dena cemun bakauya?

Murmushi yyi yace banyiba ,oya wuce har anyi ring in din fara lesson ,ko Kuma nasaka mlm rabe yazanemun ke.

Turo bari tayi ta koma class,shikuma yyi tafiyarsa....

Share pls
[1/3, 2:23 PM] El-hajj: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa

🅿37&38

Bayan ,antashi dg class,sir aliyu yanufi gida,sbd yanaso yajama sa ada kunne ,kada taje tayi ta ba yan gidansu labarin Hafsat.

Bayan ya isa a parlour yazauna suna fira da mommy, saiga sa,ada tadawo dg skul.

Kallonsa tayi tace yaya yanaga kadawo Bacin yau ba week end bane?

Tsaki yaja,yace me ruwanki to? Turo baki tayi tace yau wa mommy ,Hafsat ma tace nagaidake wlh tanada kirki.

Murmushi mommy ta yi tace to ,wacce Hafsat ce wannan?

Sa ada tace dalibar yaya cefa, tanada kirki wlh mommy tama zama kawata....

Wata harara sir Aliyu ya aiko mata da ita ,Wanda mommy na lura dashi,batadaice komaiba.

Afusace ya kalli sa ada yace ke parrot xokiyi serving dina,nan yanufi dining area yaja kujera,yazauna.

Sum sum ta tashi dan taga ba wasa a fuskarsa.

Tana cikin serving dinsa yace dg yau nasake jin kina bada labarin Hafsat agidnnan,sai ranki yabaci Kuma bazan barki tazama friend dinki ba.

Da sauri tace ah ah yaya nabari,wlh inason tazama kawata.

Hararar ta yyi yace naji bacemun dg nan,sum sum tabar gun, shikuma yaci gaba da cin abincin sa.

****** ***** ******
Bayan kwana4 lokacin su Hafsat sun gama , first CA test.

Yau Yakama Friday Kuma duk ranar anayin compound, askul din,Kuma yaune suka gama C A test din.

Gaba daya ss2 murna suke ,duk sunci wanka da kwalliya ,anfito da laker anata kida da wak'a suna cashewa ,itadai Hafsat ta na gefe tana ganin yadda suke rawa aciki harda Fatima kuwa.

Anacikin haka ss3 sukayi ringing din compound, amma ss2 sukayi biris dasu sai casun su suke hankali kwance.

Dan yanzun sun fitsare ganin ankusa basu shadows mulki yadawo hannunsu.

SP ce dataga haka taje a staffroom tasanar da Mlm rabe ,bayan ta fito yaje yasami sir Aliyu suka nufo hostel din dan kora ss2.

Ss2 kuwa sunbada himma cashewarsu kawai suke,kamar dg sama suka ga mlm rabe da dorinarsa ga hannu sir Aliyu na agefensa.

Da sauri wasu zasu arce,mlm rabe yace duk wadda ta gudu tajawa kanta.

Nan yace a rage tsawo,sir Aliyu kuwa, kallon Hafsat kawai yake ganin yadda ta tsorata duk ta rude shidama yafi ganin tafi burgesa intana cikin yanayin tsoro.

Kuma yalura banda ita amasu rawar ,yana cikin masu kallo.

Nan yakalli mlm rabe yace ai masu rawa daban masu kallo daban ,masu kallo abasu,pernashment.

Yafadi hakane dan yakubutar da Hafsat, saidai kuma mlm rabe yace ah ah mlm barni dasu ai laifi 2 sukayi ga rawa ga k'in zuwa compound.

Nan yaci gaba da jibgarsu,anzo kan Hafsat ta tsare sir Aliyu da ido taga kozaiyi wani abu akai kada adaketa.

Sai taga yajuya baya fuska ba walwala,shikuwa mlm rabe saida yazo kanta yagane kanwar sir Aliyu ce gashi agaban student,ba damar yawuceta ace yyi son kai ,haka yadaketa badon yasoba.

Yana satar kallon sir Aliyu, bayan angama dukansu suka wuce compound.

Duk akashare ko ina a makarantar,Hafsat ganin sungama inda aka basu, yasa ta nemi gefen bishiya ta zauna tana kukan kin hanawa da sir Aliyu yyi adaketa.

Tanan azaune ,sir Aliyu yazo zai rufe office dinsa yahangota tana kuka,da sauri ya nufeta.

Tana ganinsa, tarufe ido,ahankali,yace bud'e idonki kifada mun meke damunji kinjiko?

Kin budewa tayi hawaye na zuba, hands chief yabata yace ungo ki goge hawayen, kincika saurin kuka.

Kin karba tayi, kuma takibude iron Balle tayi magana,yah salam yace axuciyarsa.

Kallonta yyi yace wai banace ki bude idonba yaushe nafara wasa dke ne?

Amma tunda dukan kkeso bari tunda ga mlm rabe can nakirasa......da sauri tabud'e idon tace ah ah wlh yaya na bari.

Kallonta yyi yace to fadamun meke damunki to?

Bakomai tace atakaice,shiru yyi can yamik'a mata hands chief yace goge hawayen karba tayi tagoge amma hawayen basu bar zubowa ba.

Rai bace yace wai meyasa bakya ji ne? Bana hanaki kukanba ,Allah nasake ganunki kina Wannan yawan kukan saina bata miki rai.

Oya jeki wanke fuskarki atape,kidawo kifada mun meke damunki.

Tashi tayi taje tape ta wanke fuskarta ,tadawo sai cin magani take tana tura baki,shi in tana hakama dariya take bashi.

Suna had'a ido ta sunkudda da kanta,ahankali yace gayamun kinji ,ko kinaso mubata dke ne?

Da sauri tace ah ah, yace to gayamun cikin tura baki tace bakai bne kabari mlm rabe yadakeni ba.

Kallonta yyi yace to yazanyi kunyi laifi kudayawa kinga ba yadda xa ayi in ce bazai dakekiba ,mutane zasuce nayi son kai kuma hakan ba adalci bne shiyasa.

Amma kiyi hakuri ,kibar laifin,aima ganinku kenan Ku harda kida darawa ko?

Da sauri tace ah ah nifa kallo naje ,tsaki yyi yace Allah duk ranar dana sake ganinki gunda ake wannan sakarcin ko aka fadamun sai nazaneki da hannuna.

Kallonsa tayi ,yace yes,ko zaki jarabane,kiga aiki da cikawa,marairaicewa tayi tace pls yaya kayi hkuri bazan ma sakeba kaji?

Kafeta yyi da ido yace promise,ahankali tace promise.

Murmushi Yy yace good,yanzun ki koma daki ki huta banda yawo ba dankwali kinyi kanwata.

Tashi tayi zata tafi,ahankali yace hafsatttttttt! Har cikin kwakwalwarta taji sunan da sauri ta juyo ta kallesa.

Yace kinbi kin daure fuska to yimun murmushi mana,dariya had'e da murmushi tayimasa shima ya maidamata sannan ta tafi shikuma yawuce step quarters.

__________________

Haka Rayuwar taci gaba da kasancewa ,inda har ss 3 sun fara exam din fita,yanzun a next week za aba ss2 shadows.

Shak'uwa mai karfi ta sake shiga tsakanin sir Aliyu da Hafsat.

Wanda dg shi har ita sun fada tarkon son junansu amma basu saniba.

Ayanxun haka ss3 ne da ss2 ke zaune suna magana akan parach daza ayi na,inter house kowa yashigarma dakinsu.

Bayan sun gama shawara,an aje yadda abin XE kasance ne kowa yakoma dakinsu dan afara koyama waddanda zasu shigarma dakinsu.

A pink house kuwa Hafsat ce 1 commander kuma ita zatayi musu Queen aranar parach din.

Da misalin karfe 5: pm duk suna gaban dakin pink house, Hafsat ta saka yaran agabanta tana koyamusu parach intagaji sai second Commender ta cigaba.

Suna nan har akayi ringin din dining na dare,kuma a ranar sir Aliyu ne ke on duty master.

Da kansa shida mlm rabe suka shigo kora har cikin area hostel.

Kamar dg sama sir Aliyu yahango Hafsat abakin dakinsu tana koya parach.

Azuciyarsa yace Ashe ta iya parach ,amma ai bedaceba budurwar na hakan ai jikinta sai yyita rawa kowa naganinta,wata zuciyar tace to ko itama zata shiga inter house parach din?

Ahankali yace zan tambayeta,amma .

Hafsat naganin anfara kora tace subari agama kitchen sai su karasa,nan akawatse dan bata lurabama da sir Aliyu ake korarba.

Dan haka ta dauki plate ta wuce dining dan karbar abinci,saida taje ta hangi sir Aliyu tsaye yana kallon yadda ake raba abincin.

Bayan anxuba ma su Hafsat har zata wuce sir Aliyu ya kalleta suka had'a ido dashi, yyi mata alama da idonsa tazo.

Nan taje tagaidashi,ya amsa fuska ba walwal,yace naga kina koya ma wasu parach ne yanzun,hardake za ashiga?

Hafsat ta ce eh ,yaya nicema Queen ai......da sauri yace what ke yanzun zaki yadda kishiga ga maza kina wani girgiza jiki,ko ayi miki kwalliya afito miki da gashi duniya tagani kega mai gashi ko me?

Da sauri tace ah ah ,niba bani nace zan shigarmusuba, hause captain dinmu tace ni xanshi kuma ai bazan fito da gashinaba.

Tsaki yaja hade da harararta yace ,nikuma nace bazaki shigaba ko inkuma zaki shiga ki maida hankali ki.

Da sauri tace amma yaya ai kaga ban.. Atsawace yace stop it kiyi duk yadda kk so yabar gun rai bace.

Itama Hafsat cikin damuwa tabar gun ta nufi dakinsu ....

Dan Allah masu bina a PC. Ban kulasuba suyi hakuri inada uxuri,wlh ko a group kukayi magana ina gani kuma inajin dadin hakan.

Love u all 💋💋

Share pls
[1/3, 2:23 PM] El-hajj: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

🅿39&40
Chapter 12 · 0% Book details