← Book details Nida Dalibata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 42

Sashe 41

Nida Dalibata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Masha ALLAH gidan amarya yyi ,nan akayita watsewa dukda Hafsat taso xuwa gidan sa'ada da Zakiyya,amma ba Wanda zai kaita driver yatafi.

gidan duk an watse dg amarya sai kanwar umman su da wata budurwa sai Hafsat kawai suka rage agidan.

Nan Hafsat taji anyi horn da sauri ta fita dan dubawa ko driver ne yakawo wasu.

"Tana xuwa taga shine yakawo kabeer ango,nan tanufesu,adede Sadda ta isa ,kabeer ya fito cikin manyan kaya fuskar nan awashe kamar anmasa bushara da gidan aljanna.yana ganin Hafsat yace gsky antynmu kuma kawar my one dina,kin kyauta dan dama yanxun zanshiga nafito da duk wadda ta zauna mun agd dan yakamata abamu guri hakan.....yar dariya Hafsat tayi dan tasan kabeer yadda yake rawar kan nan yau Fatima zataji jiki,saitaji wani tausayinta.

" mota ta bude had'e da cewa hmmm sannu mai gida to akwaidai Anty kanwar umman su aciki zasuyimata yan gyare gyare sannan su fito inkuma korarsu zakayi ga wuri nan,ta kaiwanan ta shiga had'e da cewa driver gidan sa'ada zai kaita.

Bayan sun isa gidan sa'ada tsaitsaye taje ta rarrashi sa'ada akan tayi hkuri abubuwan sun had'e ne shiya sa amma xataxo mata yini,nan tabarta tana ta shankuka.

Kaitsaye gidan Zakiyya suka wuce can ma tsaitsaye taje ta fito tace driver yamayar da ita gidansu.

Koda ta shiga gida gun mama taje taci tuwo ,tukum ta koma d'akinta tayi wanka da sallah ta kwanta akan bed din ta.babu jimawa kiran sir yashigo awayarta,tana d'agawa tafara sakar masa kukan shagwaba rta,shikuwa cikin rarrashi yace sorry kinji sulti nah wlh ina busy ne duk agajiye nike ,yanxun kina ina nazo mutafi gida?

"Cikin shagwaba ta ce ina gidan mama kuma adakina ."

To yace hade da datse kiran.

Befi minti 15ba yashigo cikin gidan ,besamu kowaba,kawai ya wuce dakin Hafsat .

Ya murd'a k'ofar kwance yasameta ,da gudu ta fad'a jikinsa yarungumeta had'e da juyawa da ita suna dariya.

Hancinta yaja yace oya muje kinxomana gida ko?

Murmushi tayi tace eh din had'e da rikemasa hannu suka fito ,dakinmama sukaje ,bayan sun gaisa sir yace mamanah asamin tuwo !da sauri mama tajawo tiren dke gefenta tana murmushi had'e da cewa oh Aliyu bakagajiya da cin tuwo.

Murmushi yyi yace ai mama tuwanki nadabanne, itakuwa hafsat tasha mamakin yadda sir yayi irin wannan shakuwar da mama.

Bayan mama tayi serving dinsa ,ta tura masa gaban hade da cema Hafsat ta kamasa ruwa ,turo baki Hafsat tayi tace ni mama naga ma baki wani ji dani yanxun.

Yar dariya mama tayi tace eh naga alama kina kishi da aliyu ko?to eh nafi jidashi akanki,tana fad'a tabarmusu dakin.

Shikuwa sir sai dariyar mugunta yakewa Hafsat.

Kwafa tayi tafita yakawo masa ruwan had'e da zama gefensa tana mintsininsa.shareta yyi yagama cin tuwansa yafita gun tape a tsakar gidan yawanke hannu yyiwa su mama da Laure Saida safe dke zaune a tsakar gida.

Nan mama takoma dakin gun Hafsat ,tace bara nabaki wani magunguna ,nan ta shiga bed room ta fito da wata jarka wadda tsumine aciki ,tace ungo maganin basir ne kullum kisha sau3arana koda inkinje gun mijinki kinajin zafi zaki dena ,ta mika mata wasu magaunguna k'ulle aleda tace kirik'a sha da madara insun k'are kimun magana ,kuma kada kibari mijinki yaganikisaka ajikka.

Cikin murya ta karb'a jin harda maganin dena jin zafinnan Wanda dama tanason yiwa mama maganar tana jin kunya.

Nan sukayi sallama tafita gunsir.

****** ****** ******
Hakafa rayuwa tayita tafiya gun sir da Hafsat kullum suna cikin faranta ran juna,dan yanxun Hafsat tuni ta aje kunya tana farantawa mijinta hade da yima biyyaya,kuma yanxun tadena jin wannan zafin kullum suna manne da juna in yafita suna yin waya akai akai.

Bangaren su amarema bbu laifi love kawai suke sha abinsu,musammun su Fatima da kabeer dinta dan kabeer bbu sauki abinda kullum Abu daya tun Fatima bata sababa har ta saba hakan.

Yau Yakama week end ,sir ne zaune Hafsat na tsakiyar jinyoyinsa yana mata tsifa dan komai sir yakemata ko yatayata suyi tare.

daga ita sai wani dan wando iya gwiwa da y'ar Riga iya cibi sai shagwarta take zubawa son ranta.

Can ta kama tari ,daganan sai kakarin amai da sauri ta tashi tashige toilet ta dinga kwata amai,shikuwa sir arikice yabiyota yana tambayarta lfy meke damunta kotace wani abu?

"Ahankali tace ah ah."

Taimaka mata yyi yace ta wanke bakinta sannan yacanja mata kaya yace ,baby muje hospital.

Dire dire tahauyi ita ah ah kada ayimata allura.

Lallabata yyi yace bazai bari ayi mata ba,sannan ta bisa suka wuce hospital.

Wata private hospital sukaje ,nan Sir yabukaci son doctor mace ta dubamasa suntinshi,nan akahad'asa da wata docter ta fara bincikar Hafsat tayi mata yan tambayoyi shikuwa sir yana zaune tana kan cinyarsa ake dubata.

Nan akabata wata yar roba akace tayi fitsari,nanta tashi,har sir zai bits docter tace ah ah yajirata ta fito.

"Bbu jimawa ta fitota mik'amata robar."

Nan aka auna fitsarin atake akagano tana ciki ajikinta ,koda ta fad'a musu wani ihun murnar sir yyi yarungume Hafsat itama cikin murna tace yaya munkusa zama parent muna ko?

Eh yace had'e da cewa ALHMDLLH.

Itakuwa docter sai kallonsu take dan sun bata sha'awa ,nan sir yajata bayan anmata secarning angano cikin wata2ne.

Hannunsa cikin nata suka fito fuskarsu cike da farin ciki,zasu shiga motar ,sukaji wata nacewa bewar ALLAH kece Hafsat?

da sauri sir da hafsat suka juyo.

K'ura ma wadda ta tsaidasu idanu Hafsat tayi atake tagane labor ce wadda suka mata mugun suka suka kuma had'a baki da kamal ,suka kaita step quarters .

"Yatsina fuska sir yyi yace malama fy?"

Duk'awa tayi had'e da bayyana kanta tana rokar Hafsat yafita ,nan tace ta yafe had'e da kallon sir tace my dear mujenan suka shige suka barta gun.

Itakuwa tagane sir Aliyu, kuma ganinsu hakan yatabbatar mata su masoyane kuma ma auratta.

Tun amota sir sai nan nan da Hafsat yake yana tambayarta metakeso na masu ciki yasiya mata?

Cikin shagwaba ta ce muje nidai gun mommy nah ka kaini gunta nike so .

Murmushi yyi yace to my Princess.
Wayarsa yafito yafara sanar da mommy dasu mama bbu ko kunya sannan yakira su Mubarak da kamal,sannan kabeer.

Lokacin dayakira kabeer suna tare da Fatima akicin yana tayata aiki aiko dayaji sir yace Hafsat Nada ciki,aisai yakalli Fatima yace oya muje ALLAH bazai yuyuba muje nima nabada himma ko babyn yaya yasami k'anwa kinga sai ayi yar gida ,abada zumunci ,yafad'a had'e da kashe mata ido.

Itadai murmushi tayi tabisa ,suka wuce k'uryar daki abinsu.

Sukuwa sir gidan mommy suka nufa ,bayan sun isa ,Hafsat na hannunsa suka wuce ciki......

Share pls
[1/15, 11:39 AM] El~hajj: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

🅿121

🔚🔚🔚🔚🔚🔚

Itama Hafsat ba taso xuwa gd ba tafison gun mijinta dandai kawai bata nuna hakanba.
"Koda suka isa gidansu d'akinta aka wuce da ita ", nan jama'a suka cigaba da zuwa yan barka.
Yayinda umman su Fatima ta ja Hafsat domin yin wanka.
Shikuwa sir cikin bacin rai yakoma gd dan baison koda da minti d'aya ne yarabu da sultin shi ,dandai kawai bayason yacika yin musu da mommy ne shiya sa yahakura.
" Hafsat sarkin tsoron ruwan zafi hakadai umma ta gasheta da kyau har aka gama ta fito dg bayin ta nufo dakin", su Zakiyya ,sa'ada ,Fatima duk sun cika d'akin ko waccensu da tulelen cikinta.
Murmushi sukayi dsuka ga Hafsat nan suka fara tsokanarta suna dariya, zama tayi tasaka kaya ta shirya ,yayinda babyn ke gunsu sunata santin yaron .suna dariya dacigaba da tsokanarta . itama dariyar tayi tace hmmm kune abin dariya kuma abin tsokana zakuji yadda haihuwa take tunda har na haihu ai wankan jego bazai bani wuyaba,inkuma kuna dariyar nadawo gd to ko waccenku ita gida zata dawo."nuna Fatima ta yi tace balleke inkindawo mutuminki yazama abin tausayi dan daga gani bayada hakuri",Fatima tace hmmm kedai bari dan my one indai gun harkane ba sauki shiya sa da wuya muyi fad'a ,inma munyi ma shirya wlh kodon sbd in dare yyi z....shiru tayi ganin su ,Mubarak da yaya Ahmed shida Anty salma matarsa da sir yana rik'e da d'ansu,kabeer da kamal abayansu.sunzo duba jariri.
"Fatima ta tashi tana gaidasu had'e da karbar ameer d'an yy Ahmed dke hannun sir", Aida sauri kabeer yace my one yi ahankali kinsanfa da akwai ajiyata jikinki,dariya yy Ahmed yyi yace oh nida sabon shiga!babyn sa'ada tabasu suna kallo suna yabashi Masha ALLAH, suna mamakin rashin kunya irinta kabeer itadai Zakiyya gun mijinta ta matsa tanamasa shagwaba ita ice cream takeso ,shikuma yana lallabata tayi hkuri sbd babynsu kada ta haifeshi da mura ,sir ne yalura da su,murmushi yyi yace oh yarannan ALLAH yashiryaku.
" kallon Hafsat yyi yaga tana dariya",kusada ita yadawo yace sulti mekikewa dariya?"kallonsa tayi tace hmmm my dear su sa'ada mana ,yaya Mubarak yawani jata waje baza'ayi maganar agabanmuba.,fuska kalar tausayi yyi yace ,aini angama dani tunda anmaidominke gd ,tura baki tayi tace yaya harfa wanka sukamin da ruwan zafi kamar zai k'onani,dan zaro ido yyi yace Saida nacewa mommy sumiki ahankali yafad'a had'e da kai bakinsa saitin kunnanta yace zonxo da dare ,amma bazan bari kowa yaganniba,ingaisa da ababena......yaya Ahmed yace oh friend agabana ALLAH zansanar dasu umma ai tana cikin gidan,tsaki sir yyi had'e da mik'e wa yace kadad'e baka fad'adinba.
"Itadai Anty salma sai yar dariya take ,nan yy Ahmed yabata babyn yakalli Hafsat yace kanwata friend yakoyamiki rashin kunyarsa ko?" Sa'ada data shigo taji maganar da sauri tace yaya itamafa wlh takoya masa, hararanta Hafsat ta yi, suka saka dariya,nan suka fice sukabar matansu nan dansu yini anan.

Hakafa suka zauna suna firar su da labarin maxajansu ,har sukaci abinci sukayi sallah, suna like da baby da mamansa,basubar gidanba sai dare.

"da misalin 8:30 pm sir yakira Hafsat yace bakowa dakinki?"

"Tace eh"

In shigowa zakayi ba damuwa dan babyn na part din mama da yan barkan dare shine nafito naga duk manyane,cikin jindad'i yace ok ganinan xuwa ,yana fad'a yakashe kiran yashige cikin gidan .

d'akinta yanufa ,Aida gudu Hafsat ta yi hugging dinsa ,kafin tace wani abu yacafki bakinta yana kissing.
Chapter 41 · 0% Book details