← Book details Nida Dalibata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 42

Sashe 15

Nida Dalibata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

""""Murmushi yyi yace Aisha kenan ,to insha Allah nanda 2weeks zaikoma ,lokacin Yasami sauki,wannan umarnin governor ne ba nawaba kin fahimta?""";;;

Ahankali tace alh gsky... da sauri yakatseta yace banason yawan magana kiyimasa addua ,na yadda da dana,inbarcin da tsautsayi ke kanki kinsan Aliyu zarumine.

Ahankali tace hakane shikenan Allah yabashi,lfy .

Daddy yace yauwa kokefa,abinda zaki fad'a kenan.

Shikuwa sir Aliyu murna fai aransa dan dama yana fargabar kada iyayansa suce bazai koma askul din yacigaba da bincikensa.

""""Tashi yyi yanufi part dinsa yyi wanka yafeshe jikin sa,da body spray kala kala yakwanta,yanata tunani,har bacci yyi gaba dashi.""";;

Washe gari, tun 1230:yashirya cikin farar shadda,yarciki da babbar Riga tasha aiki da bakin zare ,yasaka hula,agogo,takalmi sawu ciki,duka bak'i,yafeshe jikinsa da turere ,masha allah abinsai Wanda yagani yawaku iya wankuwa,sai zuba kamshi yake yanashek'i sajennan na fuskarsa yak'ara masa kyau sai zuba kamshi yake.

Ya fito dg part dinsa yanufi waiting parlour.

Anan yasami mommy da sa,ada dasauri sa'ada tadauki wayar mommy ta yi ta masu selfie itadashi.

Sai wani xuzutashi take,itakanta mommy yamata kyau saita gansa kamar wani ango.

Sa'ada ta aje wayar takalli sir Aliyu race wow yaya wannan wanka aisaika haukata yan matan layin nan gsky kazo kayi aure musha biki..

Tsaki yaja had'e da cewa ,wai yaushe nafarawasa dakene?

Turo Baki tayi tace yi hakuri dan Allah.

Harararta yyi ,yakalli mommy da hankalinta nagun tb yace mommy na tafi masjid.

Juyowa tyi tace da wuri haka,kaidama baka lfy,kasaka babbar rga bazata shafi ciwonba gunda be ida warkewaba??

Ahankali yace lpia lau mommy kada kidamu ,ai nasaka vest.

Murmushi tayi race to kada kajima adawo lfy indadinku yadawo dasu kabeer nace katafi bakajirasuba.

Bece komai ba yyidai murmushi yakalli ,sa,ada yace autarmu,mezan siyamiki ,inxandawo?

Turo Baki gaba tayi tace niba ruwana dakai,kad'a kai yyi ya fita.

Saida yatsaya ahanya yasiyawa Hafsat ice cream da gasassun kaji ,sannan yadau hanyar skul din su Hafsat.....

Share pls
[1/3, 2:31 PM] El-hajj: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa

🅿45&46

"'''''''Yana isa skul din yyi parking yafito, gaba daya yatafi da imanin yan matan musammun ss3 kowace jitake inama ta mallakesa amatsayin mijinta. Fuska adaure cikin aji ya nufi office nasa ya wuce, bayan yabud'e yashiga gani yyi office din duk yyi kura ,tunani yafara wazai aika yakira masa Hafsat.
Can yahangi wata mate dinsu ,yafito fuska a tamke yace takira masa Hafsat aminu ba musu ta tafi.""""";;;;

Tana zuwa tasami Hafsat ta na saka kaya tafada mata kiran da sir Aliyu yakemata.

Aijitayi kamar ansata aljannah dan farinciki..

Tunda ta zo skul din bata taba kwalliyaba,amma yausaita tsinci kanta da shafa powder da lipstick. Fatima kuwa sai kallonta take tana yaba kyawun datayi,sannan
tasaka hijab iya gwuiwa tafito da sauri ta nufi area class ,murna fal aranta..

Tundaga window yakura mata ido yana kallon yadda tayi wani kyau tundayake da ita betaba ganinta da make up ba,azuciyarsa yace zanso inganta da personal,aisaitafi haka kyau,amma gaskiya ta dena kwalliya haka,wata zuciyar tace kasan ko tanada saurayi qila yazo yau shitayimawa,tsaki yaja afili yace nasanma batada wani saurayi tashi yyi yafita dan beson yawan kebewa da ita gunda jama,a..

"""""" yanafitowa tana isowa da murmushi a fuskarta,ahankali tace gsky yaya nayi farincikin samun lfyarka.

Shima murmushi yyi yace Allah ko?

Tace eh mana,nantagaidashi ya amsa,yace meyasa kika rame ko kinyi rashin lfy ne?

Ah ah ni lfy ta qlau,kallonta yyi yace ,kinta kukan halan aizankira Fatima na tambayeta,inkuwa tafadamun kinyi kuka zamu bata.

Turo Baki tyi tace eh nayarda ,hmmm kawai yace sai kallonta yake.

Can yawani daure fuska yace wakikayiwa wannan kwalliyar ne?

Da sauri ta kallesa dan ita bata fahimci inda yadosaba,shiru tayi.

Hakan yasa yagane bata fahimci shiga hakan yasa yagane yarinyace danya sharaf.

Hafsat yakira sunanta ,da sauri ta kallesa, yakafeta da idanunsa, ahankali yamika mata ledar hannunsa yace ga tsarabarki,mekikeso nasiya miki anjima?

Kin karba tayi ,daure fuska yyi yace, wai meyasa kikemun hakane wai?

Sabida ke nazo skul din nan shine zaki batamun rai bacin kinsan natsani hakan.

Da sauri ta karba had'e da murmushi tace ngd sosae ,ta bude ledar tagani,farinci kwance a fuskarta.

Hakan yyi masa Dadi,kallonsa tayi tace yayaaaaaaa!!

Ashagwabe har cikin ransa yaji sunan yakalleta ,tace towai miyena wani daure fuska ,kayi dariya mana,hararan wasa yyi mata yace bakece daga zuwanaba zakisa mubata.

Murguda Baki tayi tace, nidai kayimun dariya,yace to naji ,amma kalleni,kallonsa tayi suka had'a ido gaba daya suka sakarma juna murmushi da yar dariya.

Sir Aliyu yace,tawan office dina yyi datti ki gyaramun kinji kanwata.

Kallonsa tayi tace to Yayana,amma gun daurin aure zakaje in antshi dg masjid din ko?

Yace ah ah ,kawai masjid zani,azuciyarsa yace bari nagwadata naga ta damu dani ma.

Hafsat yakira sunanta, kallonsa tayi yace dg yau nabar skul din nan.

Da sauri ta zaro idanun tace meyasa yaya,dan allah kada katafi ka barni,nima inkatafi zanbar skul din allah kuwa.

Wani Dadi da farinciki yaji jinta damu tashi sosai,ahankali yace ,family na basaso sbd abinda yafaru.

Aisaitasa masa kuka harda dire dire ita sun bata baruwantadashi harma zata tafiyarta.

Ai tuni sir Aliyu yarude gashi Wannan shagwabar datake yanajinshi cikin wani yanayi.

Ahankali yace yishiru ya isa fadamun me kikeso ayi yanxun,?

Shiru tayi taki kulasa,rarrashinta yyi yace haba mana tawan kifadamun mana da zankawomiki sa,ada amma nafasa.

Da sauri ta ce ah ah dan Allah ka kawo mun ita,yace to kigaidamun me kkeso kinji tawan.

Kallonsa tayi tace kabasu mommy hkuri allah zasu hkur,ahankali yace hkane nima inaso ina askul din harkiyi ssce kici waek da neco insha Allah.

Murmushi tayi tace to allah yasa, dan Monday ma za,a,ba mate dim mu Shadows Kuma yanzun befi saura3 weeks mufara exams ba.

Wani irin haushi yaji axuciyarsa dan yasan da wuya ba,aba Hafsat Pripet ba kodan sbd kok'arinta.

Amma be nuna mata ba,afili yace ok ai baninanma za,a bada amma ke kinaso ne abaki Pripet.

Da sauri ta ce ah ah wlh, yace meyasa?

Tace yo yaya mutum bewani samun lokacin karatu koda yaushe kune ringing yin kora bi classes karbar noise, zuwa dinning raba abinci da sauran su.

Ajiyar zuciya yyi yace hakane, amma azuciyarsa yadau niya ko anbata zaisa acireta sbd suma malamai haka kawai sai sutura akira Pripet aclass tazo kawai suyita fira abun ba tsari ,yalurada teachers din sunada son mata da yawa,bayaso subata ma Hafsat dinsa tarbiyya.

Kallon agogonsa yy yace bara naje nayi sallah lokaci yakusa,kigyaramun office din yanzun zandawo abude yake.

To tace ta nufi office din, da sauri yace bazakimun adduarba yauma saina roka ko?

Juyowa tayi tace Allah yakiyaye adawo lfy ,karok'a dani a ardduarka.

Murmushi Yy yace insha Allah tsintar kanta tayi da cewa allashi yarda, nan yatafi itakuma tashige office insa.

Cikin 30minit tagyare ko ina a office din, tafeshe shi da air freshness.

Sannan ta zauna taja ledar dayyi mata tsaraba tasha ice cream, roba 2 sai tandar Baki take ta ragema Fatima sauran .

""""" tana nan har bacci yafara kwasarta ,taji kamshin turaren sa dasauri ta farka aiko tagansa yyyimata kuri da sexy eyes dinsa.
Kallonsa itama tayi tace yaya kadawo ,bara nima naje nayi sallah, tamike tsaye dan tafiya,ahankali yace to ngd sosae nima bari naje gd amma dawa dawa zan gaishemiki dasu?

Murmushi tayi cikin kunya tace sa'ada da mommy, kadai.

Dariya yyi yace to shikenan banda sauran yan gidanko?

Tace ai sukawai nasani,yace ai mommy Baki Santaba.

Murmushi tayi zatafita,yace yauwa dg yau kada nasake ganin kinyi kwalliya ko kunshi a skul kinajina?

Ahankali tace eh ,yaya bazankoma ba sai anjima da sauri ta fita.

Shikuwa tausayi tabasa dan yalura inyabata umarni kobataso tayimasa biyayya.

Da wannan tunanin yarufe office din sa yanufi inda yyi parking, yashige mota yaja yadau hanyar gidansu...

Share pls
[1/3, 2:31 PM] El-hajj: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa

Naga comments da godiya had'e da fatan alkhairi agareni, Wanda bantaba ganiba,sbd hakan zanmuku typing dan farincikin Ku,amma bana lfy kusani a addu arku,inamaku fatan alkhairi 🌹🌹.

🅿47&48

"""""" haka Hafsat ta isa daki cikin farinciki,taba Fatima ledar da sir Aliyu yyi mata tsataba. Nan tabude tace wow yau zamu yi shagali akwanarmu har natuna gd gsky mungode sosai. Nan suka haucin abinsu suka ba kawayensu sauran, sannan Hafsat ta yi sallah, tana idarwa tazo tanata ba Fatima labarin irin yadda sir Aliyu yasami sauki da irin kyawun data ga yyi mata yau,tana dariya,kallonta Fatima ta yi tace kai sis wannan wasawa da kod'awa da kkewa Sir Aliyu kodai kodai ne?"""";;;

Yatsina fuska Hafsat ta yi ta harareta tace, bangane kodai kodai ba mekike nufi ne?

Dariya sosai Fatima ta yi tace kai sis maida wukar wasa nike miki..

Tsaki Hafsat ta yi tace kekika sani ta tashi tafita.

"""""" yau yakama Monday Kuma yau akabada shadows, ciki kuwa harda Hafsat da Fatima, dukda Hafsat ba tasoba ta hakurane dan ba yadda zatayi ne,gaba daya Pripet din sai wani hauka suke suna Ciro bulalin dazasu daki yara in anyi ringing din break, Hafsat da Fatima suna gefe abinsu suna kallonsu, danko da akayi ringing din break basu dau bulala ba bakomai ahannunsu sundaibi Pripet din ana kora,hakan dasukayi yaba sauran haushi dandai suna tsoron batawa Hafsat rai sir Aliyu yyima mutum wankin babban bargo dole suka kyalesu basu tankasuba."""";;;

Haka suka cigaba da kula da skul din amma su Hafsat babu ruwansu da yara ko shiga harkar su,karatun exams kawai sukeyi,hakan yasa gaba daya yaran ke sonsu suna yabonsu.

***************
""'''' sir Aliyu ne zaune kan resting chair a compound din gidansu."""'

daga shi sai t shart da 3 quarter,idonsa alumshe yyi shiru.
Tunani yake azuciyarsa yana kirga yau 10 days kenan rabonsa da Hafsat, yakudurta gobe ko xe koma skul din tunda yasami sauki. Tunawa yyi da ambada shadows yanzun,tsaki yyi afili yace dolema acireta indai ambata.
Kamshin turare yaji da sauri yadago kansa, Zakiyya ce yagani yar k'anin daddy ce ta na mutuwar son sa ,shikuma bayasonta yatsaneta dagashi harsu daddy da mommy sbd batada tarbiyya..

Fuska a tamke bataredaya kalletaba yace kecewai ko sallama babu saidai aganki kamar dg sama?

Murmushi tayi cikin kisisina had'e da iyayi tace kai ne karufe ido inata magana bakajiba.
Be kalletaba yace ina wani nazarine mai mahimmanci ne yah gida dasu Mami?
Chapter 15 · 0% Book details