← Book details Nida Dalibata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 42

Sashe 26

Nida Dalibata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba musu tazo gab dashi tayimasa,ta kallesa hawaye na zuba murya na rawa tace yaya ka kulamun da kanka sannan kaji tsoron Allah aduk inda kake kaji?

Yah salam yafada azuciyarsa ganin batadena hawayeba,ahankali yace insha Allah tawan matso kiji ba musu ta Dan matso yarad'a mata wata magana wadda nikaina banji komai yace ba sbd yyi maganar k'asa k'asa. Da sauri Hafsat ta fashe da dariya tana kallonsa tanacewa allah yaya,shima dariyar yake yi yace eh mana,murmushi tayi tace to shikuma kaje kada kayi latti.ba musu yashiga hade da Jan motar ,Hafsat dake tsaye tarika daga masa hannu harya fita get ta nufo hostel cike da kewar sir Aliyu.

Bayan ta dawone take labartawa Fatima sir baya gari yayitafiya ,Fatima tace allah yadawo miki dashi lfy dan wlh sis ko kiso ko kada kiso keda sir Aliyu kunason juna sbd alamomi sun nuna hakan.

Harararta Hafsat ta yi tace gsky sis ba kanki dayaba,malaminane.

Fatima tace hmm allah yabamu rai da lfy ko Ku menene amma dai kuna son juna.

Hafsat bata sake cewa komaiba ,amma maganar ta tsayamata arai da tunanin maganar ta kwana.

Washe gari haka ta yini sukuku,jira kawai take taga mlm rabe yakirata yace ga sir Aliyu yakira su gaisa amma shiru har dare.
*****************

Bayan kwana4 yakama sir Aliyu lwamansa 5da tafiya Lagos,Hafsat ce zaune a bed dinta tanata tunanin sir Aliyu, kodai ba lfy har yanzun shiru be kirataba.tunawa tayi da keys d'in da yabata da sauri taje ta d'auko taja Fatima suka wuce office dinsa,bayan sun bud'e suka shiga,suna shiga Hafsat ta ji gaba d'aya office din k'amshin sa yakeyi,jitarik'ayi kamar zata gansa ,duk abin nan Fatima na lura da ita sbd itama tayi nisa asonAl-ameen dinta dan jitake in akarabasu zata iya rasa ranta,Hafsat ce ta katse mata tunani da cewa sis ki gyara office nikuma na gyara bed room,ok Fatima ta ce ta koma office Hafsat ta cigaba da gyara bed room din cike da tunanin sir Aliyu had'e da kewarsa.

"Bayan sun gamasuka fito,Hafsat ji take kamar karta fito."

Nan suka koma hostel abinsu.

Bangaren sir Aliyu kuwa da gangan yak'i kiran Hafsat dan acewarsa soyake yagwada zuciyarsa kozai iya yin wasu kwanaki beji muryarta ba ko be ganta,sbd yasan SSCE zatayi ba jimawa dole yabar ganinta kullum,dan aganinsa yyi mugun sabo dakuma shak'uwa da ita, amma me?adaddafe yyi5days yaji bazai iya jurewaba sannan ga yawan mafarkinta dayake yawan yi,dan jiya da kyar yyi bacci sbd tunaninta,bbu shiri yakira mlm rabe yace yaje yabata wayar zai kira ne yabata wani sak'o bbu musu mlm rabe yace to nan yanufi hostel dan kiran Hafsat.

Hafsat kuwa dawowarsu kenan daga gyarama sir Aliyu office mlm rabe ya Aiko tazo,da sauri ta fita dan ranta yabata sir Aliyu ne keson magana da ita away a.

Tana isa taga mlm rabe tsaye bayan sun gaisa yace mata dama gashi yanzun mlm Aliyu zai kira suyi magana .

Nanta karb'a tadan matsa bayan staffroom, nanko wayar tayi ringing saida ta k'osa tsinkewa ta d'aga shikuwa bawan Allah jin ta d'aga wayar yyi wata ajiyar zuciya dabesan yyiba.

Hafsat najin haka tasaki kukan shagwaba kamar tana agabansa.

Shikuwa gaba daya ta susutashi da shagwaba rta,lumshe idanunsa yyi murya k'asa k'asa yace I'm sorry kinji yi shiru kifada mun me kikewa rigima ne?

Cikin turo baki tace bakaineba tunda ka tafi baka kiraba sai yanzun meyasa kayi hakan?

Cikin wata kasalallar murya yace my Hafsat bahaka bane wayana ta fadi saida na canxa layi Nayi welcome back shiyasa .

Murmushi tayi tace to nayarda bakada laifi to ina wuni?

Murmushi yyi dan yalura akwai k'uruciya da yarinta atare da ita,lfy ykk ya karatu?

Ahankali tace alhmdllh.

Nandai sukayi ta fira daga karshe sukayi sallama,taje taba mlm rabe wayarsa ta koma daki cike da farinciki.

____________________
Bari mu lekasu kamal muji awane babin suke........

Share pls
[1/7, 11:20 PM] El-hajj: NIDA D'ALIBATA

Story & written by mmn fareesa

🅿77&78

Bari mu lek'asu kamal muji awanne babi suke..

"" zazzaune suke bayan sun gama shan aiki sun gaji",kamal dake tsakiyarsu kallo daya zaka masa kasan yaji jiki duk yarame yyi bak'i sbd wahalar dasuke sha shi ne yyi gyaran murya yace wlh wlh naga rayuwa kuma na yarda duniya makaranta ce ,lallai xuwana gidan jarin nakoyi darasi.insha Allah aka sakemu zanje har gun mlm Aliyu na rok'i yafiyarsa dakuma yarinyarnan hafsat.
d'ayan dake gefensa yace nima haka na shiryu dama Kaine oganmu kuma ka shiryu,dayan dke gefe yace nima haka amma kai kamar basunsaka anbata maka ta karduba? Kamal yace eh Wannan ba matsala bane sbd abbana kamfaninsa yaso na zama manager amma naki na nuna ni sai teaching zanyi ,amma inmunfito zanje narok'esa gafara yamayardani a camfaninsa.baki dayansu sukace ameen Allah yashiryu masu Hali irin namu.

Bangaren su hafsat kuwa sundage da karatu ,kuma tunanin sir Aliyu yana nan dank'are axuciyarta,yanzun haka tunaninsa take tana tunanin yau ko gobe zai dawo.shiru tayi can kuma sai takama kuka sakamakon mahaifiyarta data rasa ina take tana Raye kota mutu? Fatima ce taji kukanta ta taso tana tambayarta lfy?nan cikin kuka tace mamana sis bansan inatakeba banson kowa nata ba yazanyi da rayuwata? Ahankali Fatima ta ce kada kidamu Allah yana tare da mai hakuri kuma duk tsanani yana tare da sauk'i ki dage kiciga ba dak'ara addu a insha allah za'a ganta dan inajin hakan ajikina kinji da haka dai Fatima ta rarrasheta da irin Wannan nasihar har tayi shiru.

**************
Sir Aliyu ne tsaye gaban mirror yana taje sumar kansa yyi wani kyau na musammun ,sai sauri yake sbd dawowarsa kenan dg Lagos yanaso yaje yaga hafsat dan bazai iya kwana be gantaba.

Yana gama kimtsawa yafito awaiting parlour yasami mommy zaune tana ganinsa tace baba ga abincinka can dining yana jiranka.

"Ahankali yace mommy na k'oshi".

Da sauri yyi waje ,murmushi mommy ta yi afili tace hmm tunda kana zumudin kaje kaga hafsat ai bazaka tsaya cin abincin.

" Sir Aliyu be tsaya ko inaba sai skul dinsu hafsat ko office be budeba straight area hostel yanufa."
Cikin sa'a Fatima zata skul shop ta hangosa ya nufo nan ,danshi bema lura da ita ba ,ai dagudu ta koma ta kaiwa hafsat labari.

Da gudu hafsat ta fito dan murna tanufi get ,tana fita get sir Aliyu yana kawowa zai shiga saura kad'an hafsat ta fad'a ajikinsa.
Cikin murna had'e da farincikin ganin juna suka tsurawa juna ido suna kallo ko k'iftawa bbu.

"Ahankali sir Aliyu yace my Hafsat nasameki lfy?"

Lumshe idanunta tayi tace lfy lau Yayana Nayi kewarka da yawa .

Murmushi yyi yace nima haka, amma ai gashi nadawo kinga mahakurci mawadaci ko?

Ahankali tace eh,inasu mommy da sa,ada ?

Murmushi yyi yace wato ni ba'a wani tambayata yanike ko wani abu saidai ki tambayi su mommy da sa'ada ko?

Marairaicewa tayi tace lah yaya ba haka bane ,ba yanzun nace Nayi kewarka ba kuma kasan ai nadamu dakai, amma tunda ma kishi kake dasu mommy da sa'ada shikenan ,zandunga yin mafarkinsu sai murika gaisawa cikin mafarki ko?

Yatsina fuska yyi yace eh naji ,ni kingama tafiyata ,murgud'a masa baki tayi had'e da masa gwalo .

Murmushi yyi nidaiko ?yanzun nazo shine kkemun haka ,kinsan dama inatara laifukanki ko gashi yanzun kin sake ,gobe zankarbi bulala gun mlm rabe na zaneki da ita.

Cikin shagwaba hade da marairacewa tahau basa hkuri,shikuwa kamar gaske sai yawani sake d'aure fuska, shi adole da gaske yake.

Ai tuni hafsat ta rud'e tafara zare ido dan ta dauka da gaske yake.

Shikuwa dama haka yake so sbd hafsat tafi masa kyau a haka in tana atsorace,shagala yyi da kallonta harta lura ga murmushi kwance a fuskarsa.

Turo baki tayi ta kafesa da ido tana kallo,cikin shagwaba tace shine ka tsoratani ko?

Murmushi yyi yace hafsat dina kenan aikinfi kyau ahakan ne shiyasa na tsorataki.

Yar dariya tayi tace yaya kaje kayi aski duk wannan kasumbar ta ragemaka kyau kaje agyara maka .

Murmushi yyi dayaji tace tarage masa kyau wato hafsat ta na ganin kyawunsa kenan,kallonta yyi yace to my Hafsat duk abinda kikeso shi za'ayi kinaso insaka a askemun ita duka?

Da sauri tace ah ah anbar sajenka kafumun kyau ahakan kawai dai agyaramaka naga duk fuskar ta cika.

Murmushi yyi yace hmm garin ne banyarda damasu gyaran fuskansu ,nabari sai nazo nan nagyara da kaina,kuma dawowata kenan nace sainazo naganki.

Murmushi tayi mai sauti tace hakane yaya nah wlh kana ji dani sosai nagode .

Ahankali yace kada kidamu kinfi haka aguna ,abinda nikeso dake ki maida hankali kiyi karatu kinga final year kuke kinjiko?

Ahankali tace insha Allah ,kallonta yyi yace ni zan wuce maraice yyi ,kije kiyi alwalla kiyi zikiri kafin magarib.

Ba musu ta ce to yaya jagaidamun dasu mommy.

Kallonta yyi yace nak'i bake kikace zaku gaisaba amafarki ,murmushi tayi tace eh ai namantane,batajira amsarsaba tayi cikin area hostel.

Shikuwa yar dariya yyi yawuce get yadauki motarsa yanufi gida.

_________________
Haka rayuwa taci gaba da kasan cewa ,inda shakuwa mai karfi ta sake shiga tsakani Sir Aliyu da Hafsat dakuma tsanani son junansu inda har yanzun bbu Wanda yasan yana son dan uwansa dan duk atunaninsu shakuwa ce sukayi da juna.
Kwanci tashi bbu wuya gun uban giji harsu hafsat sun kammala exams dinsu ta first term anbasu Hutu yau sun nifo gida cike da murna dukda wani gefen na zuciyar hafsat batason rabuwa da yayanta wato sir Aliyu dukda yace zai dinga xuwa yana kawo mata Sa,ada.

Washe garin dasuka koma gida Hutu Yakama satday ne ,tun safe hafsat ta keta aikatuwa kasancewar baba yana kasuwa gun aikinsa dan in gabansane bazai bariba yanzun haka uban wanki ne tasha na Laure da yaranta,ta zauna tana hutawa baba yashigo da ledar fura guda biyu hafsat daya Laure da yaranta daya .

Bayan hafsat ta yi masa sannu da zuwa yabata ya nufi dakinsa,bbu jima aka Aiko wai wasu mutane nayin sallama da Mlm aminu.

A k'ofar gida kuwa alh Suleiman rabone wato senator da body guards d'insa, governor yaturasa a anguwanni yasami me anguwa yaji matsalolin anguwarsa,shine suka shigo nan anguwar kasancewar gidan mlm aminu ne bakin hanya kuma farkon layin hakan yasa senator yace sutsaya nan akira me gidan yyimusu magana da mai anguwar ,anguwai.
Chapter 26 · 0% Book details