← Book details Nida Dalibata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 42

Sashe 16

Nida Dalibata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

""""" lfy lau suke naga kasami sauki sosai,amma wai meyasa bakason zuwa gida muna gaisawa."""

Fuska a daure yace inkin ganni gidanku su Abba naje gaidawa dan zumunci amma banasa ran xuwa sbd murik'a gaisawa dke,inafatan kin fahimta?

Fuuuuu tawuce ta nufi gun datayi parking tafasa shiga cikin gidan.

Doguwar tsuka yaja hade da bin bayanta da kallo, yaga English wears ne ajikinta yad'a kafad'a alamar ko ajikinsa.

Afili yace garama dabata da tarbiyya dan datanada ita ,datuni daddy yacusamun ita koda banaso.

Mik'ewa tsaye yyi yanufi cikin gidan"'"";;;

Fatimace tashigo da ledoji a hannunta a kwanarsu tasami Hafsat kwance kan bed fuskarta kwance da farinciki. Tamik'awa Hafsat ledar tana murmushi tace sis yanzun yaya Ahmed yatafi ga abinda yakawo mana,wai Ashe da bikinsa saura2weeks sbd mu akamayar 5weeks dan ayi bikin muna gida tunda saura 2 weeks mufara exams,tashi zaune Hafsat ta yi cikin murna tace kai dan Allah amma dai munji Dadi wlh dayanxun bandamu za,ayi bikin nan. Fatima tace kedai bari, aisaida nasakashi yabani wayarsa nakira umma nace mata dan Allah tasaka ayima na fitted gown kala bibbiyu musaka ranar kamu da deenar.

""" ihun murna suka saka ,hade da rungume juna sunajin dadin su."";;

Hafsat ta ce wlh har na k'agara ayi Hutu wlh ,Fatima tace Allah dai yakaimu.

Washe gari takama Monday, bayan anfito daga Assembly, mlm Habib wato kitchen master yatara Pripet din da aka ba shadows gaba dayansu agaban staffroom, zasu tattauna akan abincin fa suke rabawa yara. Gaba daya shirme ne kawai da surutu kawai suke wasuma sunbiye masa hardasu dariya,sudai Hafsat da Fatima suna gefe, sbd dama mugun haushi yake basu dan yacika kallon mata da yawan yimasu magana..

Sir Aliyu ne yayi horn baba me gadi yabud'e masa get.

Yacinno hancin motarsa cikin skul din, tun kafin yagama parking yahango mata gaban staffroom atsaye,yana parking yafito yafara nufar staffroom, tsaki yyi ganin new pripet da Mlm Habib, dan bema lura da su Hafsat ba Dan inba da dalili ba bbu yarinyar data isa yakalleta,nan Mlm Habib ya matsa sukayi musabiha da sir Aliyu, adedenan Kuma Hafsat ta ganshi,shima jikinsa yaba kamar da a kwaita acikin new Pripet din, da sauri yakalli gun carab idanunsa cikin na Hafsat da ido yyimata alamar tazo,aiko ta kalli Fatima ta ce sis bara naje gun sir nadawo yanzun ,murmushi Fatima ta yi tace ok saikindawo nan ta nufi gun sir Aliyu.

"""" shikuwa mlm Habib ganin Hafsat ta taso ,yakalleta yace ke koma mungama aibangama magana dakuba.""";;;

Dama na lura kincika girman kai tunda akafara magana keda waccan bakuce komaiba, kuna wani shan kamshi ko?

Shikuwa sir Aliyu cikin isa da gadara yace ok Nina kirata ,shiyasa kaga tazo.

Cikin inda inda mlm Habib dashi yamanta ma cewar kanwar sir Aliyu ce ,yace ainadauka bahunka zataba shiyasa.

Ko kallonsa sir Aliyu beyiba ,yad'an matsa nesadasu,Hafsat tabisa ,tace yaya ina kwana?

Lfy yace a takaice dan yaji haushin tarawar da Mlm Habib yyimusu.

Ahankali tace naga kamar ranka abace badai niceba ko nabatama rai ?

Amamakinta taji yace kece mana,!!!

Zaro ido tayi tace, nikuma,to kayi hkuri dukda banson laifinaba.

Kallonta yyi yace kije class kada nakoma ganinki gun wannan shiritai nagayamiki ko? Bejira amsartaba yawuce office din principal bayansun gaisa tayi masa yajikin sa, yabukaci yanaso acire Hafsat cikin wandanda akaba shawos,principal tanuna masa ,Hafsat ce suke son suba SP amma yanuna amatsayinshi na yayanta gd basaso tayi Pripet nan tace to shikenan za,acireta,nan yafita yawuce office din sa.

Mlm Habib be barsu suka koma class ba sai gun9:00 lokacin har first period tafita anshiga second.

Bayan sukomane Fatima ke tambayarta meyasa ta dawo class.

Nan Hafsat ta ce sir Aliyu nacema wa yasa afitar dani dg cikin Pripet,tayimata karya don tasan tunda yace kada yase ganinta cikinsu tasan xaisa a cireta ne.

Fatima tace dama hardani kikace yafitar wlh ,Hafsat tace ,nima dakyarfa ya yarda kinsan bazai yardaba hardake,kihakura kada yansa ido suce muduka munkiyin Pripet Fatima tace eh hakane.

Anatashi break ,Hafsat tayi zamanta class bataje kitchen ba.

Tunawa tayi da sir Aliyu yace ta bata masa rai ,tashi tayi ta fita dg class dinsu.

Cikin sa,a tagansa bakin tape da sauri ta nufi gun amma saitanuna guntape taje tasha ruwa.

Koda yaganta shima yadauka hakane,dan haka saiya tsokaneta da cewa me bakauya!!

Ko kallansa batayiba ,murmushi yyi dan yasan ta k'ulu.

Matsawa yyi yadebi ruwan yawatsa mata a fuskata har yasami hijab dinta.

Da sauri ta murgud'a Baki tace allah saina rama nima.

Dariya yyi yace kodai rame,kin gama tafiyata yyimata gwalo,yyi tafiyarsa.

Murmushi tayi tace hmm nima zan rama nan ta wuce class dinsu.
_________________

Bayan sati daya ss3 har sunyi ssce,Kuma ambada permanent shadows Fatima ce ,assistan SP,gaba daya ss2 sunmaida hankali da karatu ,sbd sunason suwuce ss 3,su Hafsat kuwa har yar rama sukayi itada Fatima dan zafin karatu yanzun ko Sir Aliyu saidai in yashigo class dinsu take ganinsa amma rabon su hadu daga ita saishi su gaisa harta manta,sbd bbu lokaci karatu yariketa..

Shima sir Aliyu anashi bangaren har yyi missing din Hafsat sosai.

Gashi be wuce sati2 sutafi gidaba dukda yasan gari daya suke amma aiba anguwa dayaba.

Bayan kwana 2
Hafsat ce zaune da Fatima bayan sun gama karatu,Hafsat tace sis gobe fa math ce farko sai chemistry.

Fatima tace allah yakaimu tunda munyi karatu komai mai sauk'ine...

Share pls
[1/3, 2:32 PM] El-hajj: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

Fans ina godiya agareku da adduoinku danasha da bakunanku masu albarka ,nagode nagode, nagode sosae Allah yabar zumunci, ina alfaharidaku,love u all💋💋.

🅿49&50

Washe gari,cikin sa,a sukayi exams dinsu bbu wata matsala. Cikin jin Dadi suka koma hostel abinsu.
Haka kullum exams biyu suke har suka gama farinciki fal aransu zasu koma gd su sha bikin yaya Ahmed, duk sunyi parking komai nasu jira kawai suke gobe alhamis abasu report wato result dinsu,suga sakamakon abinda sukayi,Friday sukoma gida.""";;

Washe gari, Thursday Yakama sir Aliyu ne on duty master, tun 10:00am yanufi area hostel dan yasa abada abinci.

Bayan yasa anyi ringing, sukashiga kora shida mlm rabe.

Acikin hostel kuwa Hafsat ta tashi ba lfy amma ba sosaiba ,yanzun haka tana gaban dakinsu sai amai take kwararawa.kamar zata amaye Duka yan cikinta,sir Aliyu da azuciyarsa yakuduri yau sai yaga Hafsat Kuma sunyi magana da ita rabonda yatsaya yyi magana da ita tun kan sufara exams,suna karyo kwana yaganta tana amai Fatima nagefenta namata sannu,ai gaba daya yarud'e ,yama manta datare da Mlm rabe suke da sauri yanufi gunsu,tana ganinsa tawani sake langabewa,hardasu hawaye,koda ya isa gunsu,da sauri yace Fatima meke damunta take amai haka,komuje asibitine? Fatima yace wlh sir zazzabine kedamunta ,matsawa yyi kusada ita yace sannu kinji ,Fatima kawo ruwa ta wanke bakinta,nan tace to ta wuce juyowa yyi amma Hafsat ta k'i bari su had'a ido, shikuwa duk yadamu,ahankali yace hafsatttttttttt! Meke miki ciwo yanzun pls gayamun kinji tawan? turobaki tayi saiga hawaye,da sauri yace oh subhanallahi waibazakiyimun maganaba sai kuka,yi shiru bari kiwanke bakin sai muje hospital ko?girgiza kanta tayi ,ashagwabe tace nibazanje ba nibaruwana dakai tunda yanzun kadaina damuwa dani kawai kayi tafiyarka.murmushi yyi jiyake kamar yayi tafiyarsa din amma bazai tafi yabarta ba lfy ba. Kafin yace wani abu Fatima ta kawo ruwan nan tataimaka mata ta wanke bakin sai hawaye take,shidai sir Aliyu nagefe yana kallonsu,saijin zafin yadda take zubarda hawayenta take,fuska adaure yace bazak I dena kukanba wai? Saurin share hawayen tayi ganin bbu wasa afuskarsa ,yakalli Fatima yace kawomata takalminta muje dispensary ayimata allura,da sauri tace yaya wlh banaso kayi hakuri dan Allah, kaji ,hararan daya aikomata da ita yasa tayi shiru ,bayan Fatima ta je dauko ta kalmi,yakalleta ahankali yace nikuma yanzun munbata dake k'azama yar kauye kawai da,ita,aigaba daya, Hafsat ta kule dashi dan tatsani ace mata yarkauye ko kazama ,amma saitashareshi,takarbi takalmi tasaka Fatima ta kama sir Aliyu yyi gaba suna biye dashi sai nan nan yake da Hafsat,Mlm rabe kuwa begansaba yasan yanagun kanwarsa sai yaje akabada abincin gabansa.

Koda suka isa ,akaduba ta,akabata magani,gun allura ,aka fara daga da ita ,saida taga sir Aliyu yanuna mata Bacin ransa tukum ta yar da akayima tanata kuka.

""" shikuwa yatsareta da ido sai kallonta yake yanajin tausayinta."'""

Itakuwa Fatima kallonsu ,take tanason tabbata abinda take zargi wato akwai soyayya tsakanunsu.

Bayan ta danhuta ,suka fito Fatima tayi gaba ,sir Aliyu yace mekikeso na kamiki yanzun?

Bakomai tace tana turo baki,shiru yyi danyaga dazu ta k'ulu dan haka yace yau za,abada result ko gobe sai gd.

Shiru tayi batace komaiba, dan ta tuna zatayi kewarsa.

Ahankali yace shikenan tunda fushi ake dani ,nayi tafiyata juna kuma munbata dake.

Bejira abinda za,taceba yyi tafiyarsa.

Da sauri ta taddo Fatima sukawuce daki bayan sunci abinci tasha mgani, takwanta.

Cikin bacci taji Fatima na ihun murna,tana tayar da ita tace sis kitashi kiga result dinmu.

Da sauri Hafsat ta bude idonta,tace Mugani,nan Fatima ta ce, kekikayi first position, nikuma nayi forth position.

Nan cikin farin ciki tace alhmdllh.

Kitashi kiyi sallah sis mu ida had'a kaya gobe sai gida.

Cikin farin ciki Hafsat ta tashi ,tafita danyin alwarlla.

**************
Sir Aliyu ne zaune a office insa yana tunanin hanyarda zaibi yatambayi anguwarsu Hafsat,yanajin nauyin yatambayesu,itada Fatima,tunani yake ko yakawo masu sa'ada ta tambayeta tace zataje gidansu,saikuma yatuna sa,ada akwai surutu, gashi yalura Hafsat ta na fushi dashi,murmushi yyi da yatuna tayi first position a class dinsu,afili yace hafsatfa akwai brain.tashi yyi yadauki duk abinda yake bukata yarufe office din ya hau motarsa yafita daga get din skul din ,dan yakudurta gobe da kansa zaizo yakai Hafsat har k'ofar gdansu .bayan ya isa gd har yyi wanka sanyi lunch ,daddy yakirasa,yyimasa bayani yanzun yaje airport ya yankammasa bixa zaije Germany gun wasu kayansa da aka kama,akalla zaiyi 5days ko 7,days,harcikin ransa besoba sbd kudirin dke cikin ransa dande bazai iya musu da mahaifinsaba,nan yaje yashirya yanufi iya Port..

Washe gari farin ciki fal aransu saidai Hafsat taso taga sir Aliyu kobankwana suyi.

Hakadai driver yajasu zuwa gd dan yaya Ahmed ango yanacan gun hidimomin bikinsa dan yau saura8 days.

Bayan sun iso gida Fatima ta ce wa Hafsat sis anjima zanzo inkawomiki dunkunanmu in angama,Hafsat tace to sis nagode bari naje nan sukayi sallama.
Chapter 16 · 0% Book details