← Book details Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 30

Sashe 9

Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahaifin Sayyada ne ya shigo dakin tare da wani likita Ba tare da wani tunani ba likitan nan ya hada ruwan allura ya zurkuda mata a cewarsa allurar zata sanya ta samu saukin ciwon.....Ai ko minti biyar ba'ayi ba jiki ya rikice Indo ta dinga wata iriyar girgiza kumfa na fitowa daga bakinta sai a sannan kuma Bakinta ya bude ta dinga salati ta bude idanunta da suka jirkice tana kallonsu tana kiran sunansu tace"Sadam! ko bayan raina ina so ka auri Sayyada wannan shine burina Baba ku xama shaida na bawa Sadam! Sayyada Mahafin sayyada yace."Allah zai cika miki burinki Indo zaki samu sauki mu cigaba da rayuwa." Sadam! yace."Insha Allah baba kina raye zaki ga aurena da Sayyada nayi miki alkawai." tace"Mutuwa zanyi ku yafe min." Sai ta fara sha'kuwa tana salati a wannan lokaci Rai yayi halinsa.
Wannan mutuwa tayi masifar girgiza zukatan mutane domin indo mutum ce mai shiga rai da barkwanci kowa sai da ya girgiza da jin mutuwar Indo Mussaman mutanan da suke rayuwa da ita a cikin gidan a wannan lokacin akayi mata suttura aka kaita gidanta na gaskiya, Sai bayan an dawo ne mutanan kaduna suka sauka a garin Alhaji Auwal yayi kuka sosai da mutuwar kanwarsa yana kaunar Indo shiyasa duk wani abun data bukata a lokacin tana raye a duniya yake mata......Sulaiman shima yaji mutuwar sosai tare suka dinga jajantawa junansu.

Sulaiman na ganin Sayyada yaji wani tausayi da sonta a zuciyarsa duk girmanta haka yake daukar ta su fita yayi mata siyayyar cizi biskit alawa iri-iri Sayyada ta zauna tana shan abunta bata da wata damuwa saboda da kuruciya a tare da ita a lokacin.

Sadam! kam ido ne nasa sam baya tanka musu watarana dai idan yaga abin yayi yawa sai ya daka mata tsawa idan tana wani shirman ita kuma sai ta fashe da kuka da ruga gurin Sulaiman tana fad'a masa shi kuma a lokacin ne zaka ga 'bacin ransa....Sadam! haushi da takaici ya sanya ya bar gurin sam a ganinsa abunda Sulaiman din yake wa yarinyar bai dace ba zata sangarce ta lalace duk girmanta sai ya dorata a cinya ko ya sa'bata a kafad'a ya fita da ita yana mata kiss a kumatu takaici kamar ya kashe shi.....Sai da sukayi fad'a kaca-kaca da Sulaiman din amma bai daina ba da karshe kawai sai ya daina kulashi gabad'aya to da yake Sulaiman din yafi shi saukin kai shine yake masa magana wani sa'in.

Bayan sadakar bakwai suka shirya tafiya.....Sayyada ta dinga gursheken kuka kamar ranta zai fita Alhaji Auwal yace." A had'a kayanta xai tafi da ita Baba Ladidi tayi tsalle ta dire tace"Bata yarda ba....Sulaiman ya dinga lallabata har da yi mata alkawari zai kaita umara tace"In dai sai ta basu Sayyada zai kaita Umara to bata so.

Sadam!!! 'bacin rai bai barshi yace komai ba shi dai ya zuba musu ido kawai sai da yaga iskancin Sayyadar yayi yawa sannan ya zare blet ya nufe ta yana zare ido......Ta ruga bayan Sulaiman tana kuka shi kuwa Sulaiman hararasa kawai yake yana fad'in"Wallahi ka dake ta da wannan blet din sai na rama mata mutum sai 'bakar zuciya kawai kai koma naka babu imani ka tausaya mata mana."!

Tsaki! Yaja ya maida blet dinsa ya daura a gu'kunsa ya koma ya tsaya shaye da toka sai wani cin magani yake duk suna kallo Sulaiman din ya sa'bata a kafad'a ya fita da ita sunfi 'karfin rabin awa basu dawo ba Sadam!!! sai tsaki yake yana kallon agogo an kira wayarshi ya kai sau biyar ana jiransu a bracck dinsu akwai sabbin sojojin da zasu horar dasu.

Mahaukaciyar siyayya Sulaiman yayi mata ta kayan zako iri iri Ya jibge baba ladidi ta cika da mamaki shi kuma yace."Ko idan sun kare ayi masa waya a sanar masa zai turo kudi." Baba Marka tace"Wannan ai ka siyo mata kayan ciwo haba ai abun yayi yawa za'ki ai ba abun sha bane."
Yace."Baba komai Sayyada take so zanyi mata tausayi take bani." Tace."To dai banda irin wannan siyayyar ta cutarwa kasan halinta yanzu sai ta'ki cin abinci ta dimanci shan alawa da madara.

Alhaji Auwal yace."Sai a kwashe kayan a dinga bata da kad'an-kad'an! Sadam!! yace."Nima dai abinda na gani kenan idan kun tara mata kayan za'ki taci ta sha to ku shirya da sanin cewar zata dame ku da kukan ciwon ciki."!

*To wannan shine tushen labari*

Page na gaba zamu dawo ainihin labari

30/5/2020

*BINTA UMAR ABBALE*

_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga duk mai bukatar karantawa sai ya tura kudinsa ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank idan kuma katin waya mutun zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din zan fad'a masa yanda zai biya kud'in....08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar littafin to sai ku tura dala dari ta wannan numbars.....90899076 _88137740 katin airtal ko orange.....Dala dari itace a madadin dari uku na najeria.*_
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________

Free Pege 9

*Cigaban Labari*
To haka Sayyada ta cigaba da rayuwa a hannun Baba Ladidi tare da kulawar 'bangarori daban daban mahaifinta ma yana iya bakin kokarinsa akanta sai da da yayi aure ne matar da ya aura ta janye masa hankali daga kan Sayyada ya daina kulawa da ita sosai Sayyada sam! bata sha'ku da bangaran mahaifinta ba tafi shakuwa da bangaran mahaifiyar ta shiyasa ba sosai take zuwa can gidan maigarin ba sai Baba Ladidi ta takura mata sannan take zuwa Juma'a Juma'a, shima idan taje bata wani zaman arziki take dawowa gida a cewarta baza ta zauna Hansatu tana yi mata kallon banza ba domin sun sha fad'a sosai da ita da matar baban nata mai suna Hansatu.

Sayyada yanzu haka tana aji shida a karamar makaranta suna dab da jarrabawa makarantar isilamiyya kuwa sun hada izifi ashirin to babu laifi tana gane karatu amma Amina ta fita kokari, kun san dai kowa da irin baiwar da Allah yayi masa.

*****

Karfe uku shaura na rana tana zaune da kwanon abinci a gabanta hijab ne a jikinta kalar ruwan toka gefanta jakar makarantar isilamiyya ce Amina ce tayi sallama ta shigo

Ta gaishe da baba Ladi dake bakin rijiya tana wanke kwanoni kai tsaye ciki ta shige itama ta shirya tsaf da shirin tafiya makaranta.

"Sayyada baki gama cin abincin ba kenan? duba lokaci ya kure da yawa kin san dai yau malam Bashir ne zai shigo ajinmu ko."?

" Yi tafiyar ki malama kar ki dame ni! sai me idan malam Bashir ne zai shigo sai a ka fad'a miki tsoronsa nake."!

Amina jikinta yayi sanyi tace"Kin san dai ko zai barki ki kishiga aji sai ya doke ki da wannan bulalar mai zafi shine abinda nake guje mana."

"To me ya dame ki? kinga nifa bance dole sai na tafi dake ba tafiyar ki daban tawa daban mtwss!

Baba Marka ta daga labule ta fito tana fad'in" Surutun me nake ji Amina."!?

Amina data sha'ka da yawa tace"Baba Wai daga nace mata tazo mu tafi makaranta kar mu makara shine take fad'a min magana."

Baba Marka tace"To bakya ganin abinci take ci ne."

Amina tace"Ai dama cewa nayi tayi sauri baba."

Marka tace"Ke Sayyada maxa ki gama ku tafi karku makara." Sayyada tayi musu shiru tana cin abincinta haushin Amina takeji sosai kuma tayi al'kawarin sai ta kunyata a gaban 'kawayensu na makaranta.

Tana gama cin abincin ta mike ta wanke hannunta jakarta ta dauka ba tare tace Amina komai ba ta kama hanyar fita....Amina tabi bayanta tana fadin"Sai mu dawo." Baba Ladidi tace"To Allah ya bada sa'a."

Ko a hanya ma Sayyada 'kin kula Amina tayi har suka isa makaranta Sayyada ta tsallake can gurin 'kawayenta itama Amina ta zauna gurin 'kawayenta dama gurin zaman Amina a gaba yake ita kuma Sayyada can baya take zama tare da manyan 'yan matan da suka girme ta nesa ba kusa ba suyi ta zancan aure sam basa gane karatu sai maganar aure da hirar samari Sai lokacin jarrabawa yayi idonsu ya raina fata Sayyada ce kawai mai 'kokarin cikinsu ita ke basu amsa ko kuma idan ta rubuta ta basu su kwafa shiyasa suke tsoronta komai tace dai-dai ne."

Sai bayan malam bashir ya fita ne kafin wani malamin ya shigo Sayyada ta kallesu tace "Kun san menene."!? Suka ce sai ki fad'a." Tace"Wallahi na tsani Amina muguwar munafuka ce." Sadiya tace"Ke Sayyada ke da 'yar uwarki kuma me tayi miki."?

Tace"Humm! wai saurayina ko kuma nace mijin da zan aura shi take so har da wani shishshige masa shi kuma har da sa mata zobe bayan fa tasan da al'kawari a tsakaninmu dashi."

Ummi tace"Lallai Amina bata da kunya wallahi to ke wane mataki kika dauka."!?

Sayyada tace"Ku taso muje inda take." babu musu suka mike suka isa inda Amina ke zaune da kawayenta suna bitar karatu.

Aminta taji magana a kanta "Ke Amina ciro wannan zoben dake hannunki."! Sayyada ce me wannan maganar tasha kunu.

Amina ta dago kai tana kallonsu tace" Kamar Yaya na ciro zobe me ya shafeki dashi."

Ummi tace"Lallai Amina baki da kunya au! tambayar ta ma kike meye ruwanta bayan kinsan zoben hannun Saurayinta ne ai tana da iko dashi."

Amina ta mayar da kai kasa tana karatu Sadiya tace"Wallahi tun muna shaida juna dake ki ciro mata zobenta ai itace tafi dacewa dashi tunda ita zai aura amma saboda tsabar shishshigi kin wani shigewa saurayinta wai don ya aure ki mun gane abinda kike nufi."

Daya daga cikin kawayen Amina tace"A gaskiya wannan abinda kukeyi bai dace ba ina ruwanku da Amina ni dai tunda na shigo banga ta shiga sabgarku ba."
Chapter 9 · 0% Book details