← Book details Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 30

Sashe 4

Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadam! Ya kalli talle dake tsaye tirmin danya shi ya'ki tafiya yana sanye da wani yadi fari yayi masifar daud'a duk yayi jirwaye mussamam hamtar sa da bakin aljihunsa sai wata shegiyar hula da ya kwafa a kansa sai kace kwano sa wani tabarau wanda yayi masa yawa.Shi nan bai yarda ba yayi gayu.

Sadam! mutum ne mai 'kyamkyami sosai shiyasa kallo guda yayi wa Talle da yaga bakinsa dagaje-dagaje yayi saurin kauda kansa yana ya mutsa fuska......Yace."Kai wuce ka bawa mutane guri dallah."! Talle ya ya hau ya'ke yana sosa 'keya yace."Ya asalin na wuce muna hira da masoyiyata."

Sadam! yaji wani bala'in takaici ya kamashi jin abinda Talle ke fad'a ba wai yana kishi bane kawai tsabar kauyancin da sukeyi shine yake bashi haushi.....Bai iya ce masa komai ba ya kalleta tana tsaye sai tauna gefan dankwalinta take yace."Dauki kayan tallan ki wuce gida."! Shiru tayi tana kallonsa tare sa zu'baro baki.

Kwata kwata baya son dukanta shiyasa ma kafin ya isa gurin ya saisaita tunaninsa domun a yanda zuciyarsa ke masa zafi da yarinyar yana gani zai iya yi mata mugun rauni saboda duka shiyasa taushi zuciyarsa akanta bayan haka kuma yanajin tausayinta saboda maraicinta gaba da baya.

Talle yayi wani 'kas! da hannu irin na gayu na 'kauye yayi wani juyi da kafafunsa da suke sanye da wani fatattakaken kambos yace."Baby sai gobe zamu had'e naga wannan gayen shima kamar yana sonki to karki damu da komai baby tunda ni kike so nima ina sonki."

Talle Ya fad'i wannan maganar ne domin ya cuzgunawa Sadam!! saboda a tunaninsa son Sayyadar yakeyi......Sadam! kam kallo ya bishi dashi cike da tsabar takaici ya ma rasa bakin magana ya dawo da kansa kanta "Dauki kayan tallan muje gida."

"To ai gyadar bata 'kare b......." Wani bahagon mari ya kai mata! Allah yasa bai same ta ba don da ta sake marin nan ya same ta to sai tayi jini da majina! da sauri ta dauki farantin gyadar ta kama hanya tana waiwayen sa.

Ya biyo bayanta cikin yanayi tafiyarsu ta sojoji.

"Allah ya isa ban yafe ba mugu azzalimi d'an iska." ! Ire iren surutan da takeyi kenan tana waiwayensa Sadam! na gani tana motsa bakinta amma baya jin abinda take cewa saboda kasa kasa take maganar.

Tana shiga kofar ta sa kuka a guje ta shiga ciki tana fad'in "Allah ya isa."!! Baba Ladidi! Kinga Ya Sadam! ya koroni ya hanani na siyar miki da gyadar ki kuma sai cini ki akeyi ya kori mutane."

Baba Ladidi dake kishingid'e kan tabarma ta mike zaune tana gyara daurin dankwalinta tana kokarin magana ya shigo gidan.

Kai tsaye inda suke zaune ya nufa ba tare da ya zauna ba yace."Baba ashe dama tallah kike d'orawa Sayyada yanzu don Allah me kika nema kika rasa da zaki dinga dora mata tallanta gyada da daddare tana shiga tsakiyar maza ke kin san sayyada ba nutsuwa ce da ita ba kike dora mata tallah."

Tace."Haka kawai sai na zauna 'kuda yabi bakina ba zan nemi na kaina ba kenan? meye laifi don na dora mata tallah ai ko babu komai kudin cinikin yana toshe mana wata kafar saboda haka daukar tallah yanzu Sayyada ta fara idan kaga ta daina to tana dakin mijinta."

Yace."A haka kike cewa in aureta kenan."!? Tace"Kwarai kuwa wai me kuke nufi ne? duk wanda zai ga Sayyada na zama gindi bishiya tana saida gyada sai ya fassara da wata manufar ni nasan halin sayyada baza ta aikata abinda kuke nufi ba ku kyale mu kawai mu nemi na kanmu."

Cike da tsabar takaici yace."Babu rashin ci babu rashin sha babu rashin gurin kwanciya kike wata maganar, A gaskiya to kan wannan al'amari muna iya 'batawa dake domin wannan ba tarbiya bace da daddare kawai ki kasa mata tallah ta shiga cikin maza ke kina kwance a gida ba fata nake ba idan wata matsalar ta faru me zaki ce mana saboda haka kome zakiyi daga yau Sayyada ta daina daukar tallah."

Baba tace"Sayyada ba zata daina daukar min tallah ba sai dai idan aure nayi mata wai ina ruwanku ne? kai kake wata magana idan kaji haushi yau ka turo sadakin auranta sai a daura muku aure ka dauke kayar ka amma matukar muna tare da ita baza ta daina tallah ba."

Yace."Ai ni na gama magana ba zan aureta ba kuma tallah sai ta bari domin yanzu idan na fitar daga wannan kofar zan nufi gurin Sarkin 'kofa in shigar da 'korafina akanki."

Ai sai Baba tasa kuka tana fad'in"Ni za ka kai 'kara gurin Sarkin 'kofa saboda baka da mutunci."

Yace."To kece ai kin'ki ki zauna ki fahimci mutane kawai kina bin son zuciyarki."

Tace."To naji zauna sai mu fahimci juna."

Ya samu gefanta ya zauna tace"Maganar dai ta kare idan kana so sayyada ta daina tallah to ka yarda a daura muku aure kafin ka koma amma kar ka sake ka kai maganar gurin Sarkin 'kofa to kaji."!

Yace."Shikkenan zanyi tunani kan maganar ki amma don Allah ko bayan na tafi karki 'kara dora mata tallah." tace"Haba ai magana ta 'kare bari na kawo maka abinci."

Yace."Bari dai naje can kofar Kawu Tanko naci a can."

"To babu laifi ai duk d'aya ne."

Yana fita Sayyada tace"Baba yanzu da gaske kike kin daina soya gyada kuma na daina daukar tallah? kinga fa yau dari da ashirin nayi sannan Talle ya bar min sanjin talatin d'insa kinga d'ari da hamsin kenan."

Baba ta kar'bi kudin tana lissafawa tace"Rabu dashi zai tafi ai sai mu cigaba da abinmu a kan wane dalili zasu hanani neman kudi."

Sayyada tace"Nima dai abinda na gani kenan." Mikewa tayi taje ta zubo abinci ta zauna tana ci tana tunanin abinda ya faru tsakaninta dashi da safe duk sanda ta tuno da lokacin da ya dora hannunsa a kan nononta sai tsigar jikinta ta tashi wanda tunda suka fara fitowa bata taba jin wani yanayi a jikinta ba sai a wannan karon da sukayi ita dashi.

****

Washe gari da safe dake tana riga kowa tashi a gidan Baba Ladi da Baba Marka na cikin dakin suna bacci ta share gidan ta had'e kwanuka ta wanke ta nufi bandaki domin ta wanke tana tura kofar bandakin lokacin shi kuma yana daure igiyar wandonshi karf suka had'a ido a razane! ta sauke idonta 'kasa ta saki kofar jiki na 'bari ta bar gurin....."Wayyo Allah wannan meye a mararshi kamar gashin jinjiri a kwance bakikirin a jiki dama haka jikin maza yake da gashi to me ya kawo gashi a marar sa.

Jiki a sanyaye taje bayan Baba Ladi ta kwanta ta rintse ido tsigar jikinta sai tashi takeyi.

Sadam! kam yaji takaicin ganin da tayi masa yana daure tazuge wato Allah ne ma yaso shi ya riga ya gama uzirinsa da yarinyar nan ta cuce shi.......Ya fito ya dauki brush dinsa inda ya aje ya goge bakinsa tsaf ya koma masaukinsa cike da takaicin yarinyar.

27/5/2020

*BINTA UMAR ABBALE*
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________

Free Pege 5

Sayyada shiru tayi a bayan Baba Ladi tana zare ido rintse ido tayi sai kuma ta bud'e da sauri ta mike zaune ta hau sosa kai a hankali ta mike taje ta d'aga labule tana le'kensa yana goge bakinsa ta jima a tsaye a bakin kofa sai da taga ya mike tayi saurin sakin labulen ta dawo ta zauna tare da zabga tagumi tana tunanin abinda ta gani.

Can ta saki ajiyar zuciya da taji tafiyarsa da alamu ya koma masaukinsa sai ta fito ta d'ibi ruwa cikin bokiti taje ta wanke bandakin.....Tana fitowa shima ya fito daga dakin da yake suka had'a ido tayi saurin dauke kanta tana gumtse baki dariya take so tayi amma tana jin tsoro.

Sadam! ya girgiza kansa ya wuce dakin Baba bacci take sosai ya hau tashinta bude idonta tayi tana salati tare da hamma da alama tana jin dadin baccin yace."Baba ruwa nake so me zafi nayi wanka zan fita da wuri domin in zaga 'yan uwa kwana biyu kacal zanyi na koma."

Baba Ladidi na d'aura d'ankwalinta tace"aikuwa babu ruwan zafi sai dai na dora maka idan na dama kunu."

Yace."A'a ki fara d'umamin ruwan zafin kafin ki d'ora kunun." Tace"To haka za'ayi." Sai ta hau kiran Sayyada.

Ta shigo tamkar wata mai hankali tace"Gani Baba."

"Ki d'orawa Mijinki ruwan wanka."

Jin abinda tace yasa ta zum'bura baki tare da fad'in"Kai Baba."! Mikewa tayi ta bar gurin.

Duk suka bita da kallo yace."Wallahi baba ladi kina bani haushi wannan wace iriyar magana ce salon kawai ta raina ni yaushe na zama mijinta."

Baba Tace."Yo kwana nawa ne kuma ai gwara in dinga kiranta da sunan matarka yafi armashi."

Takaici yasa ya mike ya fito tsakar gida.....Tana tsugune can wani ke'bantaccen guri da suke girki tana kunna wuta a (kurfoti) ya tsirawa bayanta ido yana ayyana abubuwa da dama kanta shi yanzu ya auri wannan yarinyar ya auri me? yarinya babu fasali babu gaba babu baya sai uban tsayi kamar lisha shi yafi son mace mai brest da hips sosai duk da dai yarinyar bata gama girma ba amma yana ganin anya kuwa sai dai ya lura tana da shafaffen ciki da alama kuma zata yi hips masu kyau.

Duk hannuwansa ya zura a cikin aljihu yana kallonta ta mike da wata butar 'karfe da suke d'umama ruwa taje ta ciko da ruwa ta d'ora kan wuta tana juyowa suka had'a ido.

'Kasa tayi da kanta tana kauda kai tazo zata wuce shi....Sai da tazo daf dashi sannan dariyar da take 'boyewa ta su'bce sai ta rife bakinta da tafin hannunta tana kyakyatawa, idanunta tsaye a kansa tamkar taga mahaukaci.

Shan kunu! yayi sosai saboda ya fahimci abinda takewa dariya yace."Don Ubanki dariyar me kike? wa kika mayar mahaukaci anan gurin."

Baba Ladi ta fito da sauri tana fad'in"A'a ya naji ana zagi kuma."!?

Sayyada tayi bayanta ta 'boya tana ti'kar dariya Baba tace"Ke bana son ja'irci da shashanci dariyar me kikeyi haka."?
Chapter 4 · 0% Book details