Sashe 3
Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sayyada ta mi'ke da kyar tana nuna mata brest din nata wanda yafi ciwo tace"Yaya Sadam! ne ya murd'e min."!! Baba Ladi ta buga salati tana tafa hannu tace"Kika ce Sadam ya murd'e miki nono kan wane dalili? ai wannan mugunta ce kowa ya sani idan mace ta fara 'kirgar dangi sunayi mata zafi idan ba so yake ya kashe ki ba kan wane dalili ma zai ta'ba miki jiki bayan ance ya aure ki ya'ki."!!! Baba Ladi ta shiga sirfa bala'i inda ta nufi kofar d'akinta inda mayafinta yake rataye a kofa ta nan nad'e shi ta d'ora aka sai kace wacce tayi gammo wai ita nan yafa mayafi tayi sai ta nufi hanyar fita tana d'ingisa 'kafa "Wannan ai kafirci wato yaje yayi mu'amula da turawa 'yan bana bakwai sun 'bud'e masa ido da iskanci shine yazo zai dinga latsa yaran mutane to kuwa zai ci ubansa."!
Bayan fitar ta Amina ta Kalli Sayyada dake goge hawaye tace" Wallahi Sayyada 'karya kikeyi kice Yaya Sadam! ya ta'ba miki nono wallahi kiji tsoron Allah meye abinda zai burgeshi a jikinki mutum da yake mu'amula da 'yan gayu yaje 'kasar waje yayi karatu yayi cud'anya da turawa masu kyau da ilimi shine har zaki ce ya ta'ba miki nono ni dai ban yarda ba."
"To kada Allah yasa ki yarda mana dama ai ba so nake ki yarda ba aikin banza kawai kamar yanda yake dan uwanki nima haka yake dan uwana harda zaki wani tare masa ai dake ya ta'bawa ba zakiji dad'i ba ke ko kishina ma bakya yi wallahi nasan irin zaman da zanyi dake."
Amina tace"Ai halinki na sani na sharri da shirya magana sai kiyi ta rantsewa kan abunda ba'ayi ba wallahi Sayyada kiyi hankali ki daina abunda kikeyi."
Sayyada haushi ya sanya ta soma zagin Amina kafin kice kwabo sun kaure da fad'a har da kokawa Sayyada tayiwa Amina lilis ta zaneta tace"Idan kinje kice yazo ya rama miki shi wanda kike tarewa fad'an."
Amina na kuka ta nufi 'kofar su....Ita kuwa Sayyada sai ta kama hanya ta fice daga cikin kofar gabad'aya gidajan amare ta fara bi tana musu wanke wanke da shara yayi al'kawarin ba zata dawo gidan ba sai dare sai ta tabbatar ya bar garin sannan zata dawo.
Baba Ladidi ta nufi kofar su Kawu Tanko saboda tayi ya'kinin yana can aikuwa samunsa tayi zaune kusa da Baba iyatu da Marka suna hira ga 'kwaryar fura a gabansa yana sha.
Tana shiga ta sauke mayafin dake saman kanta ta rataye kan igiya.....Tace."Kai ja'iri gurinka nazo yanzu zan tona maka asiri ehe! wato dama abunda kaje ka karanto kenan iskanci."!
Sadam! Ya aje ludayin dake hannunsa ya had'e fuskarsa sosai yasan hargitsi irin na Baba Ladidi shiyasa yaci mur yana kallonta.
Ita kuma ta kalli Marka tana numfarfashi tace"Yanzu Marka dai-dai kenan abunda Sadam! yayi iye!? Haka kawai saboda son zuciya yarinya na irgar dangi ya kama mata nono ya murd'e wannan ai iskanci ne da yahudanci yarinya kamar Sayyada me ta sani."!?
Marka da Iya suka sanya salati suna tafa hannu." Sai su mayar da hankalinsu kansa......Dake mutum ne mai mutukar 'kwarjini da iya waskewa ko alama basu fuskanci razana a tare dashi ba sai ma wani kwarjini da yayi musu wanda suke ganin kamar ba zai iya aikata wannan d'an yan aikin ba.
Baba Marka tace"Haba Ladi! Wai kin manta halin Sayyada ne? hummm! gaskiya banji dadin jin wannan maganar ba haba jama'a! ai a fad'i abunda zai faru amma wannan dai karya ce Har guda nawa Sayyadar take haba jama'a!!!!
Baba Iya tace"To nima dai abinda na gani kenan Sadam! ba zaiyi wannan al'amarin ba.
Yace."Baba Marka ku kyalesu don Allah ni nasan saboda me yasa ta fad'i haka saboda d'azu ta tisa ni a gaba wai dole sai na auri sayyadar nace bana so a kai kasuwa shine suka 'bullo da wannan zancan to ni me zanyi da wannan mahaukaciyar yarinyar 'kazamiya."
Baba Ladi ta maka masa da'kuwa tana fad'in"Ubanka ni ce nake maka 'karya ko? Wad'annan kafiran idanun naka menene ba za ka iya ba Ai ni na yarda da abinda Sayyada ta fad'a su dai da kayi musu kwarjini sai su 'karata maganar auran Sayyada kuma ni na yanke hukunci."
Murmushi yayi kawai ya sadda kai 'kasa yana me cigaba da 'kur'bar furar sa.
Baba Marka ta kalleshi a nutse tace"Haba Sadam! ashe kana so ka bamu kunya kenan."!?
Ya kalleta a nutse yace."Wace iriyar kunya kuma."? Tace."Naji kana maganar kai ba zaka auri Sayyada ba karka manta da cewar Kaine kayiwa mahaifiyarta al'kawari zaka aureta kafin rasuwarta kayi 'kokari ka cika wannan al'kawari."
Yace."Baba lokacin da nayi alkawarin zan auri yarinyar Baba Indo na cikin halin ciwo lokacin inaso taji sau'ki ta dawo cikinmu mu cigaba da rayuwa kuma a lokacin da 'kuruciya a tare dani amma ni har ga Allah ba wai na amince bane zan auri yarinyar ina me baku hakuri kuma ina mata fatan kan Allah ya bata miji nagari wanda ya fini nutsuwa da komai da komai.
Baba Ladidi ta saka kuka tana fad'in"Wallahi kai ba d'an halak bane Sadam! yanzu meye laifin Sayyada umm? yarinya san kowa 'kin wanda ya rasa yarinyar ma tafi 'karfin ka matar manyar mutane ce amma saboda muna so mu cika al'kawari muna ta binka kana mana wulakanci kar Allah yasa ka aure ta d'in." Ta dauki mayafinta dake rataye a kan igiya ta nufi hanyar fita tana share hawaye.
Amina ce ta shigo tana kuka.
Baba Marka tace"Ke kuma meye kike kuka.
Ba tace komai ba ta shige daki tana share hawaye duk sanda zasuyi fad'a da Sayyada ita take cin galaba akanta ta rasa menene dalili.
Baba Marka ta dinga rarrashin sa kan ya daure ya auri Sayyada kamar yanda yayi alkawari a can baya....Domin ya kwantar mata da hankali yace."Zai yi tunani kan al'amarin.
24/5/2020
*BINTA UMAR ABBALE*
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*_Littafin Ni da Yaya Sadam! na kud'i ne 1 _ 2 ga mai bukatar karanta littafin zai tura #400 kacal ta wannan accont d'in.......0542382124......Binta Umar Gtbank.....Idan kuma katin waya zaka tura to sai ka tuntu'beni ta wannan numbars din nawa zan fad'i yanda zaka/ki biya kudin......08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar karanta wannan littafi to zaku tura katin airtal ko orange na dala dari a wannan numbars......90899076 _88137740.....Dala d'ari itace a madadin d'ari uku kud'in Najeria_*
Free pege 4
Sayyada tunda ta fita daga gidan bata dawo ba sai gab da magariba tazo shigowa sukayi kici'bus dashi ya fito daure da alwala da nufi zuwa massalaci ya kalleta ta kalleshi babu tsoro a tare da ita ta zabga masa tsaki tare da fad'in "Dan iska kawai."
Sadam! ya bita da wani irin kallo na mamaki yanzu shi Sayyada ta kira da d'an iska? Zuciyarsa tace masa ka ta'ba mata nono dole kira ka da wannan sunan.....Tabbas hakane daya sashen na zuciyarsa ya fad'a masa haka.
Girgiza kansa kurrum yayi yayi gaba yana tunani kan al'amarin sam bai ta'ba jikin yarinyar da wata manufa kawai sai dan hukunci yanda ya fahimta yarinyar da kakarta sunyi masa wata fassara ta daban tabbas zai nunawa yarinyar shi d'in 'dan iska ne kamar yanda ta kira shi zai dinga murd'e nono da take ta'kama dashi.
Da 'kyar Baba Ladidi ta tirsasata tayi sallahr magariba sannan ta d'auki kayan tallanta ta fita can bakin wata katuwar bishiyar darbejiya ta nufa ta aje farantin gyadar marau da tibis Baba Ladi ce take soyawa duk daran duniya Sayyada na dauka ta fita dashi cikin ikon Allah sai kiga anyi cini dari dari biyu a cewar Baba Ladi ta siyi kalanzir da sukari na koko sana'a ko yaya take dad'i gare ta.
Tare da Kawu Tanko suka fito daga massalacin suna tafe suna hirar yaushe gamo Kawu Tanko na tambayar d'an uwansa Sadam! yace."Yayi tafiya zuwa Abuja wata uku zaiyi ya dawo insha Allah......Sai da suka zo dab da bishiyar da Sayyada take ya hangota matasan maza 'yan bana bakwai sun kewaye ta sai wasan banza suke d'aya har yana cire mata d'an kwali.
Gabansa ya fad'i sosai! sai yaja ya tsaya yana kallon Kawu Fuskarsa a d'aure yace."Kawu waccan yarinyar ba Sayyada bace."?
Kawu Tanko ya kalli inda yake nuna masa ya hango Sayya tsakiyar maza.
Yace."Itace ai nan ne gurin da take zama siyar da gyada Baba ke kasa mata tallah da daddare."
Sadam! Yaji kamar ya gaura masa mari! wannan ai cin amana ne yarinya marainiya suka zuba ido suna gani ta dauki hanyar lalacewa.
Yace."Haba Kawu! Haba duba fa ka gani Kawu kuna raye wannan al'amari yake faruwa! kar fa ka manta da cewar yarinyar nan amana ce a gurinmu Baba Indo bata cancanci wannan abu ba."
Kawu Tanko jikinsa yayi Sanyi kalau yace."Sadam! wallahi tallahi nayi dukanin iya bakin kokarina kan hana faruwar wannan al'amari Baba ta'ki fahimta akwai ranar dana zubar da gyadar a cikin kwata a ranar Baba sai da ta kusa tsine min kuma tafi sati bata amsa gaisuwa ta wallahi shiyasa nake jin tsoron shiga lamarin saboda gudun bakin uwa amma dukaninmu munyi iya bakin kokarinmu kan al'amarin."
Girgiza kai kurrum yayi ya nufi bakin bishiyar ba tare da yace komai ba.
Kawu Tanko ya bishi da kallo ya riga yasan halin Sadam! da ba'kar zuciya da gudun magana da zai dauki shawara sai yace kawai ya amince a daura musu aure shine zai kawo karshen matsalar.
Matasan samarin na ganinsa ya doso gurin sai suka watse kowa yayi nasa guri ita kuma tana fad'in" Kai Talle mai abin dariya kar'bi canjin ka wallahi ko kuma in had'a dashi cikin lissafina."
Talle yace."Kije na bar miki budurwata ai kin fi karfin komai a gurina."
Kyalkyalewa tayi da dariya tana gyara daurin dankwalinta tace"Talle kenan waye ya fad'a maka ni zan auri d'an 'kauye humm! mijina d'an birni ne kyakkyawa Soja mai aj.........Kafin ta 'karisa tagan shi a tsaye a kanta.
Mi'kewa tayi da sauri! tana mutsika ido ta fara zumbura baki jelar d'ankwalinta ta kamo tasa a baki tana taunawa tamkar wata shshasha! nan kuwa tsabar iskanci ne yayi mata yawa.