← Book details Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 30

Sashe 22

Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sulaiman yayi shiru ransa ya 'baci Sadam bashi da mutumci kuma baya jin kunyar ya tozarta shi a gaban ko waye.....Ba tare da yace masa komai ba ya wuce ya barsu a gurin.....Cikin tsawa! yace."Dallah! malamai ku wuce ku bawa mutane guri in banda hauka kawai kun tsaya gaban gardi irin wannan yana muku hoto wai ku kyawawa! mtsssw!!!! Su Mariya suka shige cikin gidan jikinsu duk a sanyaye Sayyada taji haushin wulakancin da yayiwa kawayenta sai ta dinga zumbura baki tana hararasa! tazo zata wuce yace."Dube ta sam bata dace da amarya ba."! "To ai kai ma baka dace da ango ba." Yace."Ke waye ya fad'a miki dama ni ango ne."!? Hararsa tayi yace."Ni kike harara mara kunya." Ta juya tare da fad'in"Duk inda ango yake yana farin ciki amma banda kai kowa yace ka sanja hali ka'ki ji! Ni ba zaka takura min da kawayena ba tunda ai ba da wayarka muke hotonba." Yace "Zo nan ki 'karbi wayar tawa kuje kuyi hoton." Cikin rashin wayo ta dawo shi kuma ya zura hannu kamar zai dauko wayar caraf! ya rike damtsenta! suka kalli juna ita dashi saurin dauke kansa yayi jin wani irin maganad'isu na fizgarsa zuwa gareta....Cikin kasalalliyar murya tace"Sakar min damtse."!
"Idan na'ki fa."? yafad'a cikin wani irin voice hucin numfashinsu ne yake had'uwa sai jikinta ya soma kyarma! shi kuma ya kurawa bakinta ido yana kallo a hankali yace." Su Sayyada amarya." Dauke kanta tayi tana shan kunu. Ya saki murmushi tare da cizan lipls dinsa na kasa yace."Ina fatan kin shirya kar'bar angon naki." Zumbura baki tayi tana dauke kai! murmushi yayi ya sakar mata hannu yace."Ki shirya da kyau! ni ba ragon namiji bane kuma bazan d'aga miki 'kafa ba."
Murguda baki tayi tace"Ai a shirye nake kuma waye ya fad'a maka nima raguwa ce."!? ido ya zare ya bude baki yana kallonta cike da mamaki! fari tayi masa da gadar-gadar din idanunta wanda yasa ya kusa faduwa a gurin ta juya ta shige cikin gidan......''Iyeee! ashe dai 'yan matan 'kauye suna da abun mamaki yanzu ya tabbatar da cewar Sayyada tasan aure tasan abinda akeyi a zaman aure, lallai akwai badakala kenan.....Shifa baya jin zai taki yarinyar a yanzu sai ta zama cikakkiyar mace a ganinsa a sannan ne zata iya d'auke masa dukanin bukatarsa a yanzu yana ganin idan ya kusanci yarinyar zai iya sanyawa ta had'u da yoyon fitsari tunda yawanci masu irin shekarunta ke haduwa da lalurar ya girmi Sayyada da kusan shekaru ashirin kuma karfinsu ba daya bane jarabarsu ba daya bace shiyasa kawai ya yanke shawarar bari ta kara shekuru sai suyi zaman aure mai tsafta

Sayyada na shiga cikin gidan suka ke'be da Mariya tace"Mariya kinji abinda yake cewa kuwa."? Mariya tace"Sai kin fad'a." "Humm! wai cewa yake yi dafatan na shirya masa kaina ni wallahi tsoro nake ji fa." Mariya ta dinga dariya tace"Ke mijikin wayayye ne don Allah ki saki jiki kusha soyayya." Sayyada tace"Mariya kenan baki ga abinda na gani bane shiyasa kike cewa in kwantar da hankalina." Sayyada duk sanda ta tuno da sandar girman Sadam! sai gabanta ya fad'i! domin ba zata ta'ba mance ranar bankadashi a bandaki ba."

To haka aka cigaba da gudanar da sha'anin biki da al'adar garin....Kwana uku bayan daurin aure suka shirya tafiya Sayyada ta cika gidan da kuka tana kukan rabuwa da Baba Ladi baba marka suma kukan suke da kyar dai aka taushe ta tayi shiru aka kaita can gidan iyayenta nan ma sai da tayi kuka sun jima da mahaifinta nayi mata nasiha hakanan maigari ma yayi mata nasiha da fatan zaman lafiya sannan sukayi sallama da juna.

*****

Biyu shaura na rana sun isa garin Kaduna garin gwamna Nan ma jama'a ce cike da gidan 'yan uwan hajiya Fatsima da makota da abokanan arziki sai hidima sukeyi Ango da Amarya na shigowa suka cika gidan da bud'a suna tsokanar Sadam! sai sannan taji muryarsa yana ramawa harda dariya....'yar autar su Hjy Fatsima ce mai suna Zuhura ita ta ja hannun Sayyada suka shige can bedroom dinta ta bude mata lullubin sayyada ta dinga jin kunya tana kauda kai sai da taga zuhuran ba wata babba bace sai ta saki jikinta suna hira haka 'yan uwan hjy fatsima suka dinga shigowa d'aya bayan d'aya suna ganinta tare da sanya albarka Sadam! na kowa ne shiyasa suke kaunar matarsa.

Aunty Luba ce ta shigo tana cire 'kafa d'akyar kana kallonta kasan ta kusa haihuwa tazo ta rungume Sayyada tana fad'in"Sannu da zuwa amaryamu." Sayyada na jin muryar aunt Luba ta bude mayafi rungumeta tayi tace"ashe baki haihu ba." Luba tace"Ina kan hanya Sayyada ku tayamu addua." Tace."Insha Allahu aunty.....Tare suka ci abinci suna hirar yaushe gamo sayyada ta sake da ita sosai dama tuntuni sun saba tunda Sulaiman na kaita *Dabi* tun kafin auransu sannan duk sanda yaje *Dabi* yana bata waya su gaisa shiyasa sukayi sabo da juna.
Anan ne take jin labarin tafiyar Sulaiman din bayan daurin aure tafiya ta kamashi 'kasar larabawa *Qatar* sati biyu zaiyi ya dawo....Sayyada tayi masa fatan alkairi da dawowa lafiya.

***

Sai misalin karfe takwas na dare sannan gidan ya samu sau'ki masu aiki sun gyara ko ina na gidan kowa kuma ya kama gabanshi sai aunty Luba wacce dama tun bayan tafiyar mijin nata ta dawo gidan sai ya dawo tukkuna Hajiya Fatsima tace"Da zuhura ta zauna ta d'ebe mata kewa tunda anyi hutu......Hajiya Fatsima ta shigo dakin ta tarar dasu suna hira ta kalli Luba tace"Ya kamata Sayyada ta shirya sai ku rakata dakin mijinta ko."? aunt luba tace"To Mamah! tana fita Luba tasa Sayyada tayi wanka tas ta gyara mata jikinta kana ta feshe mata jiki da turare masu sanyin kamshi ta bata wani material mai kyau da tsada tasa ta yafa mata mayafi kalar material din takalmi sabo ta sanya suka fito a tare Hajiya Fatsima tayi mata nasiha sosai dangane da zaman aure.........Kai tsaye bangaran Sadam! din suka nufa lokacin yana daf da fitowa sai sukayi kici'bus! fuska ya saki sosai suka gaisa da Luba duk fad'an da sukeyi da Sulaiman bai shafeta ba saboda yana ganin mutuncinta sosai matace mai hankali da aiki da iliminta yace."Da kin bari ma nazo na dauki amaryarta da kaina ai ba wani abun bane." Tace"Oho dai naji ai komai zaka fada sai dai ka fad'a ni bana kishi tunda dai nasan nice uwar gida." Yace."Ai kuwa yanzu na daina yayinki tunda na samu amarya." Dariya tayi tace"Ai dama wannan halinku ne." hanya ya basu suka shige yace."To ni dama fita zanyi amma ba zan dade ba." Hararasa tayi tace"Kana da amaryar zaka fita yawo ko aiki ne da kai ya kamata ka dauki Uziri." Yace."Karki damu yanzu zan dawo insha Allah....Gurin aiki zan nufa yanzu amma bazan wani dade ba tunda nasan akwai amarya ke dai kawai ki zauna kiyi min gadinta." Tace."Baka isa ba nima ka barni da kishin dake damuna." Dariya ya dinga 'kyakyatawa ya kama hanya ya fita....Sayyada ta dinga mamakinsa dama haka yake sai dariya yake har da kyakyawata lallai ma Yaya Sadam! ita sai yayi ta sha mata kunu yana mata tsaawa.
Aunty Luba ta d'an zauna mata amma da taga dare yayi sosai sai tayi mata sallama ta koma can sashen su Hajiya......Sayyada tayi tsuru kamar mayya motsi kadan ta duba agogo karfe goma sha biyu da rabi tayi bai shigo ba sai ta kwanta kan gadonsa tana kuka haka bacci ya dauketa bata tashi ba sai asubah!!! tana kokarin sauka daga gadon ne taji motsin shigowa cikin palon ta koma ta kwanta nan taji ya turo kofar dakin ya shigo ya jima tsaye a kanta yana kallo duk a tunaninsa bacci take yaje yana jan kafafunta" Taki bude ido mugun haushinsa takeji ta dauka zaiyi ta rawar kai a kanta kamar yanda angwaye keyi shi sai yayi wanka ma yayi ficewarsa saboda bata da matsayi a gurinsa.....Da ta gaji da jan kafar ta da yake sai ta fuzge da karfi ta jiyo muryarsa yana fadin"Tashi kiyi sallah." Toilet ya nufa ta bishi da harara! Taji ciwon abinda yayi mata ya nuna bai damu da ita ba shiyasa yaje ya kwana a waje....jin motsin bude kofa yasa ta dauke kanta da sauri ya fito ya sauya jallabiya duk tana kallonsa ya dauki carbi ya fita....Nan ta mike ta nufi bandakin domin daura alwala.

10/6/2020

*BINTA UMAR ABBALE*

_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga duk mai bukatar karantawa sai ya tura kudinsa ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank idan kuma katin waya mutun zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din zan fad'a masa yanda zai biya kud'in....08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar littafin to sai ku tura dala dari ta wannan numbars.....90899076 _88137740 katin airtal ko orange.....Dala dari itace a madadin dari uku na najeria.*_
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*
Chapter 22 · 0% Book details