← Book details Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 30

Sashe 10

Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dallah malama rufe mana baki banza 'kazama wacce bata waye ba ke idan ke akaiwa haka zakiji dadi? Mijina fa taje tana cusa kanta a gurinsa har sai da ya sa mata zoben da yayi niyar saka min wallahi sai ta cire zoben nan ko kuma ta raina kanta."!Sayyada ce ke wannan maganar tana girgixa jiki....Ai kafin kice komai 'yan ajin sun lullu'be su suna son jin 'karin bayani ita kuwa Ummi 'kawar Sayyada sai fad'a musu take Amina munafukace me 'kwacen saurayi don haka kowa yayi taka tsantsar da saurayinsa.......Aikuwa sai aka fara surutai kowa na fad'in albarkacin bakinsa.

Amina 'bakin ciki ya sanya ta fashe da kuka idanu jage-jage da hawaye take kallon Sayyada tace" Yanzu ni kika tozarta a bainar jama'a Sayyada nifa 'yar uwarki ce."!

"Oho! wannan ke ya shafa ni dai nace a ciro min zobe ko kuma yanzu jiki yayi tsami wallahi."!

Amina tace" Wallahi bazan cire zoben nan ba tunda ai bake kika saka min ba sai ki bari idan wanda ya saka min zoben yazo sai ki saka shi ya cire min da kansa."

Sayyada tayi wani juyi had'e da buga tsalle! sai ta cafki wuyan Amina ta sha'ke cikin hijab tana fad'in"Wallahi sai kin cire min zobe banza shashasha me 'kawacen saurayi."

Amina da Sayyada kokawa suke sosai da sosai Sayyada duk ta ya kushe mata fuska sai 'kwa'kule mata hannu take tana murd'ewa wai dole sai ta cire zoben ita kuma Amina ta dunkule hannunta.

'Yan aji kuwa sai Ihu! suke suna dariya da fad'in"Wallahi babu wanda zai rabaku ku casu ai 'yan gida d'aya ne."

Mariya 'kawar Amina ita ce ta nufi ofis d'in malamai domin ta fad'a musu halin da ake ciki sai suka ci karo da Malam Bashir ya fito daga ofis yana kokarin shiga wani aji tace"Malam Bashir ana fad'a a ajinmu.'' Yace."Waye da waye."!? Tace"Amina ne da Sayyada. Kai tsaye a jin ya nufa da zabgegiyar bulalar sa.

Har yanzu kokawar suke Sayyada ta kusa ciro zoben Taji saukar bulala a bayanta ko a jikinta sai da ta ciro zoben sannan hankalinta ya kwanta ta saki wuyan Amina tana nishi! Amina ta mike zaune sai kuka take ga Sayyada duk ta ji mata ciwo da yakushi.....Malam Bashir yace."Ku same ni a ofis."

Yana fita Sayyada ta mi'kawa Ummi zoben tace"Ri'ke min wallahi komai za'ayi ba zan bayar ba."

Ta kama hanyar fita Amina ta mike da jiki a sanyaye tabi bayanta duk 'yan ajin suka bita da kallo Amina ta tsargi kanta sai rufe fuska takeyi kamar wacce tayi abun kunya.

Suna isa ofis din suka tarar da Malam Bashiri na zaune kan kujera da wayarsa a hannunsa yace."Ku tsuguna ko wacce ta d'aga hannu sama."

Babu musu sukayi abinda ya saka su sai da sukayi minti goma shabiyar a haka sannan yace."Ku sauke hannunku." Suka sauke Sayyada ya kalla yace."Daka gani kece mara gaskiya bari na fara jin ta bakin ki me ya had'aku fad'a."!?

Sayyada ta soma inda inda" Malam nifa d dama ita k.....A gida bama shiri da juna kuma munafuka ce ita."

Malm Bashir yace."Ni ba wannan na tambaye ki ba ina so ki fad'a min ma'kasudin fad'anku." Shiru tayi ya girgiza kai yace."Ko anan ma alamu sun nuna kece mara gaskiya Sayyada nagaji da halin ki yanzu yanzu zan kira Sadam! a waya in sanar masa da abinda kikeyi a makarantar nan."
Sayyada gabanta ya yanke ya fad'i jin abinda yace sai tace"Nifa malam wallahi ba laifina bane itace ta shiga gona ta."

Malam Bashir ya kalli Amina yace."Amina ke fada min abinda ya hadaku fada kafin na yanke hukunci."

Amina ta warwarewa Malam Bashir duk abinda ya faru tsakaninta da Sadam! da yanda akayi yasa sanya mata zoben hannunsa.

Malam Bashir yace."Sayyada kece mara gaskiya don haka a kanki zan dauki mataki ina ruwanki da zoben hannunta tunda dai ba ke kika saka mata ba ko kuma ance miki shi Sadam! din idan ya aure ki dake kad'ai zai zauna to ki shiga hankalin ki wallahi."Sayyada ta kama 'kunkuni hawaye na kokarin zubo mata....Malam Bashir ya fara neman numbar wayar Sadam sai da ya kira sau uku sannan ya dauka hands free ya bude duk suna jin muryarsa suka gaisa da malam bashir din wanda dama tun asali sun san juna abokan juna ne saboda duk lokacin da Sadam! din ya shigo garin a majalisarsu yake zama.

Mlm Bashir ya fad'a masa dukanin abinda ke faruwa tare da fad'a masa hukumcin da ya yanke a kan Sayyada zai korata gida ta zauna sai bayan sati biyu ta dawo."

Sadam! Yace."Yanzu ina Sayyadar take."? Malam bashir yace."Duk gasunan a kusa dani." Yace."okey bata wayar zanyi magana da ita." Sayyada najin haka sai gabanta ya fad'i! da sauri ta aro dauriya da jarumta ta kar'bi wayar da malam Bashir din ke mi'ka mata.

_Afuwa bani da change sosai kuyi manege_

31/5/2020

*BINTA UMAR ABBALE*

_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga duk mai bukatar karantawa sai ya tura kudinsa ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank idan kuma katin waya mutun zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din zan fad'a masa yanda zai biya kud'in....08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar littafin to sai ku tura dala dari ta wannan numbars.....90899076 _88137740 katin airtal ko orange.....Dala dari itace a madadin dari uku na najeria.*_
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________

Free Pege 10

Dakakkiyar muryarsa mai cike da amo taji yana fad'in"Ina Sayyada."!? Baki na rawa tace"Gani." Yace."Wai ke me yake damun kwakwalwar ki ne? don Ubanki! ni da kaina kinji nace zan aure ki da har kike tozarta 'yar uwarki a kaina! ni me zanci dake ai idan aure zanyi Aminar zan aura tunda tafi ki komai da komai.....Tayi saurin katse shi ta hanyar fad'in"Ni wallahi Amina bata fini komai da komai ba."! Yace."Ni nake magana kina katseni wato nima zakiyi min rashin kunyar ko."? Shiru tayi bacin rai da bakin ciki yayi mata yawa, yace."Tun muna shaida juna dake ki cire zobe nan ki bata ai ina sane dake ban baki ba saboda ba ki dace dashi ba sai ita kuma wallahi kinji na rantse kada wata magana ta sake biyo bayan wannan a tsakanin ki da Amina idan kika kuskura nazo garin akace ga wani abu da kika sakeyi makamancin wannan to dama kin san sauran sai jikin ki ya fad'a miki kinji ko baki ji ba."!? Ba tare da ta amsa ba masa ta kashe wayar....Cike da mamaki! ya bi wayarsa da kallo wato yarinyar shi ta kashewa waya ashe haukan banza yake ba sauraransa take ba lallai Sayyada wuyanta ya isa yanka.

Kiran wayar ya sake yi sai tayi saurin mi'kawa Malam Bashir wayar ya dauka tana jin sanda yake cewa malam Bashir din duk sanda ta sakeyin wani abu ya sanar dashi zai zo da kansa ya dauki mataki a kanta.
Sukayi sallama da juna malam bashir ya kashe wayar sannan ya Umarci Sayyada da ta mayar wa da Amina zobenta tana zum'bura baki tace"Zoben baya hannunta tunda ta cire a cikin aji ta neme shi ta rasa. Malam Bashir dai yasan karya take saboda kar yaja maganar tayi tsaho yasa yace su koma aji Sayyada ta duba ko ina mutukar bata ga zoben nan ba to sai ya zaneta.

To koda suka koma aji bata sauya zani ba don Sayyada habaici ta dinga yiwa Amina tana fad'in "Duk abunda xa'ayi sai dai ayi amma ba xata bada zobe ba.

Ita dai Amina bata ce mata komai ba ta zauna cikin kawayen ta kunya duk ta isheta ganin irin kallon da wasu suke mata.

*****

To haka suka cigaba da rayuwa tsakanin Sayyada da Amina babu jituwa kullum fad'a kuma Sayyadar ce ke takalo fad'an har ta kai ta kawo suka daina kula junansu saboda Sadam! wanda shi da suke abun dominsa ma bai san sunayi ba.

" Oyoyo Yayana" Oyoyo sannu da zuwa." Sayyada ke wannan ihun tana tsalle tun sanda taji Sallamar Sulaiman a 'kofar su da gudu taje ta rike hannunsa shi kuma ya dan rungume kafad'anta fuskarsa dauke da murmushi wanda ya kara masa kyau da kwarjini yana mata wani irin kallo yace."Babyna kece kika girma haka.'"! Cikin kunya ta rufe fuskarta tana kokarin kar'bar jakar kayansa....Murmushi ya saki yana d'an shafa siririn sajen sa yace."Masha Allah babu shakka Baba Ladi ta iya raino akwai gwaggwa'bar kyautar da zanyi mata." Baba Marka ta d'aga labule ta fito daga d'aki tana fad'in"Murya wa nake ji ne kamar ta soja." Da Sulaiman tayi tozali tace."Au! ashe bature ne to sannu da zuwa lallai yau za'ayi ruwa da 'kankara *Dabi* tana da babban 'bako." Sulaiman yace."Kwarai kuwa baba yau naso nayi suprise d'in ku ne shiyasa kawai kuka gani ba tare da kunyi tsammani ba." Baba Marka na shimfid'a masa sabuwar tabarma tace"Aikuwa dai munyi mamaki kwarai da alama ma zaka kwana biyu a garin tunda na ganka har da guzirin kaya." Yace."Zanyi sati biyu insha Allahu kafin in koma, wai ina d'aya matar tawa ne."!? Yana nufin Baba Ladidi Sayyada tace"Yanzu yanzu ta tafi sabuwar kasuwa, amma dai nasan yanzu zata dawo."
Yace."Okey. Baba Marka tace"Bari in dama maka fura kafin a d'ora abinci." Yace."Nagode Baba sosai nayi kewar wannan furar taku mai dad'in gaske." tana dariya ta mike ta shiga daki....Sulaiman ya tsirawa Sayyada ido yana kallonta sosai yake masifar son yarinyar a cikin ranshi yana ganin idan da babu maganar aure a tsakaninta da 'kaninsa da babu abinda zai hanashi auranta sonta ya riga ya zama jinin jikinsa.
Chapter 10 · 0% Book details