Sashe 17
Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ko wacce ta shige 'kofae su." Sayyada ta kalli Amina tana mata gwalo Amina tayi rau! rau! da ido tana kallon Sadam din da ya juya baya da niyar barin gurin tace"Yaya Sadam! idan anjima akwai wata magana da zamuyi da kai." Sayyada tayi saurin juyowa tana kallonta Amina ta dauke kanta Sadam din yace."To babu laifi Allah ya kaimu lafiya." Fita sukayi shida Captain Habu, Ita kuma Amina ta juya zata shiga kofar su Sayyada tace"Banza jaka mayya kawai Wallahi duk nacin ki sai dai ki hakura banza kawai."!!!
Amina ko waigowa ba tayi ba ta shige kofarsu tana addua Allah yasa hakanta ya cimma ruwa.....Sayyada ta jima a tsaye a gurin tana sake sake daga bisani ta nufi babbar kofa aifa ba zata basa zuwa gidansu Ummi ba sai dai kome zaiyi sai dai yayi.
7/6/2020
*BINTA UMAR ABBALE*
_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga duk mai bukatar karantawa sai ya tura kudinsa ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank idan kuma katin waya mutun zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din zan fad'a masa yanda zai biya kud'in....08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar littafin to sai ku tura dala dari ta wannan numbars.....90899076 _88137740 katin airtal ko orange.....Dala dari itace a madadin dari uku na najeria.*_
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*
_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________
*Free Pege14*
Koda Sayyada ta fita can ta hangosu tsallake kan wata katuwar tabarma tare da matasan samarin garin irin su malam Bashir, dauke kanta tayi tazo ta wuce ta gabansu Sadam! ya bita da kallo yana girgiza kansa kafin ya ankara ya hango Talle ya tare mata hanya harda dogare hannunsa a jikin bango magana yake mata kasa-kasa ita kuma sai waiwayen bayanta take tsoro take ji kar yayiwa Talle ilah! dan ga dukanin alamu Talle ya mance karonsu dashi......"Haba baby yawa kikeyi karfa ki manta da cewar ni masoyinki ne me kaunarki a cikin ko wane hali.'
Sayyada ta juya tana kallon bayanta aikuwa sai ta hangoshi yana tafiya tamkar wani zaki har ya kusa riskarsu....."Wai baby kallon me kikeyi ni nefa Talle masoyin......Yana ganin Sadam! sai ya sunkuyar da kansa kasa hanyar fecewa yake nema
Sadam ya 'karasa gurin tare da tare masa hanya fuskarsa babu annuri yace."Kai tsami guy ya kake? wato ka manta gargadin da nayi maka kwanakin baya da suka wuce ko."?
Talle yayi kasa da kansa tsoro duk ya dabaibaye shi mussaman da ya lura da wandon sojojin dake jikin Sadam! Baki na rawa yace."Ayi hakuri yallabai soyayya ce ta jawo."
Sadam! yayi murmushin takaici yace."To kaje ka nemi dai-dai da kai domin wannan dake tsaye a gabanka ba sa'ar auranka bace."
Baki na rawa Talle yace."Insha Allahu na daina kulata daga yau na fahimci komai." Sadam! yace."Kai dai ka sani na fad'a maka duk ranar da na sake ganin ka nuna ka santa ranar zaka 'bakunci lahira." Talle ya dinga bashi hakuri kokari kawai yake ya bashi hanya ya wuce.
Talle na barin gurin ya mai da hankalinsa kanta.
Kasa tayi da kanta gabanta na fad'uwa yace."Ina zakiji ba cewa nayi ki koma gida ba."? Baki na rawa tace" Gidan su Ummi zani." Ya watsa mata kallon banza "Wuce cikin gida ko ranki ya 'baci! Kafin ya ankara tayi gaba ta barshi a tsaye a gurin.....Baki a sake yake binta da kallo waigowa tayi tana kallonsa sai ta gumtse baki tana dariya ta juya ta cigaba da tafiyarta.
Ya jima a tsaye yana mamaki! Wato yarinyar nan ta raina shi da yawa amma yasan maganinta zai daina shiga sabgarta tunda bata jin maganarsa.
Majalisarsu ya koma cike da takaicin abinda Sayyada tayi masa.
***
Can cikin gida kuwa Amina na shiga kofar su ta rushe da kuka Baba Iya na tatar gasara ta dakata tana kallon 'yar tata tace"Ke kuma lafiya? kin shigo kina kuka menene ya faru naga hannunki da hijab dinki da jini.
Amina na share hawaye ta sanar da mahaifiyarta abunda ya faru tsakaninta da Sayyada Baba iya ranta ya 'baci ko wane lokaci Sayyada itace take cin galaba akan Amina amma ba'a ta'ba d'aukar mataki ba ana kallo Sayyada nayin abinda ta gadama a cikin gidan ba'a yi mata fada ita da take ma 'yar mace ba 'yar namiji ba gaskiya wannan karon ba zata yarda ba.
Tana gama tatar gasarar ta dauki mayafi ta yafa ta nufi kofar su Sayyada.....Baba Ladidi na gaban murhu tana dahuwar kazar amare ita kuma Baba Marka na gyara kayan miyan da za'ayiwa su Sadam! farfesu Baba Iyatu ta shiga suka amsa sallamar ta Baba Iya taja ta tsaya tana fad'in"Baba Ladidi a gaskiya na gaji da irin wannsn abun da yake faruwa a gidan nan, Kullum Sayyada ke cin galaba akan Amina ba'a ta'ba daukar mataki ba haba abun yayi yawa gaskiyar magana ya kamata a gyara al'amarin yanzu gashi Sayyada ta farfasa mata hannu da kwalbar lemo jini sai zuba yake."
Baba Ladidi tace"Subahanallahi! abinda ya faru kenan? Baba Iya tace"Kwarai kuwa baba gaskiya a jawa Sayyada kunne abinda takeyi yayi yawa."
Baba Marka tace"To in banda abunki ma ai Sayyada ba maxauniya bace nan da 'yan kwanaki ta bar gidanan kuyi hakuri kan abinda tayi kuma za'a ja mata kunne."
Baba Iya ta kama hanya ta fita tana bala'in jin takaici Sayyada zata riga 'yarta aure don dai babu yanda zatayi ne ta hakura shiyasa take so ta tayar da hankalin kowa a gidan kafin lokacin bikin.
Ummi tace"Wai don Allah da gaske kikeyi Yaya Sadam! yazo." Sayyada tace"Lallai Ummi dama ina yi miki karya ne."? Ummi ta mike da sauri tana jan hannunta tace"Tashi muje na ganshi don Allah." Sayyada ta kalleta tace"Wai don Allah wannan rawar jikin da kikeyi na menene? ni bana son rashin kamun kai fa."
Ummi tace"Wane irin rashin kamun kai mtwsss! dan ma kin samu zanje na ganshi na fasa zuwa."
Sayyada tace"Yi hakuri tashi muje amma don Allah kiyi komai a nutse karki ta washe masa baki."
Ummi tace"Wallahi Sayyada baki da mutunci." Dariya sukayi sannan suka fito tare Sayyada tayi wa babarsu Ummi sallama suka fita.
Tun daga nesa Sayyada ke nuna mata shi Ummi sai kallon majalisar take tana so ta tantance waye Sadam! din Sayyada tace"gashi can me koriyat riga a jiki da wando irin na sojoji." Ummi tace"Na gane shi wai! gaskiya Sayyada kin dace da miji dan gayu dan birni gashi kuma soja." Sayyada akayi dariya,
Sadam! takaici kamar ya kashe shi yana daga inda yake yana hango sayyada na nuno shi da hannu sai kace wata 'yar kauye dauke kansa yayi saboda tsabar bakin ciki Shi kuwa Captain Habu dariya kawai yake musu.........Garin kallon sa kafarta guda ta subce ta fad'a ramin kwata ihu!! ta kurma ta riko hannun Ummi! Yana kallon abinda ke faruwa yace"Allah shi 'kara dauke kansa yayi kuma baiyi niyyar mikewa ba....Habu ne ya mike da sauri ya isa gurin.....Yayi yayi ya jawo 'kafar Sayyada ya kasa sai kuka takeyi Ummi duk tayi kalar tausayi.
Captain Habu ya isa inda yake zaune yace."Haba aboki ka tashi mana kaje ka ciro mata kafar Yarinyar nan fa garin son da take maka ne yasa ta fada cikin ramin haba mana."
"Rabu da ita Habu idan ta gaji zata fito da kanta naji dadi data fad'a cikin ramin." Habu yace."baka da imani wallahi." komawa yayi gurin yana janyo hannunta ta ma'ke hannun kuka takeyi harda majina Captain habu ya koma gurinsa sai da ya nuna masa 'bacin ransa sannan ya mike ya iski gurin.....Tana ganinsa ta sake lanjarewa tana kuka kafar wandonsa ya tattare ya afka ramin Ba tare da wani bata lokaci ba ya sa'bata a kafad'arsa ya kama ya fito Sayyada rike shi tayi gam! tana sauke ajiyar zuciya....Ko da yayi nufin sauke ta sai ta'ki ta cikwikwiye masa riga hade da rike masa wuya dole haka ya hakura ya nufi cikin gidan da ita a kafadarsa.
Baba Ladidi ta saka salati tana fad'in me zan gani Sayyada kwata kika fad'a."? Ya dure ta kasa ya kama hanyar bakin rijiya.
Ruwa yaja ya wanke jikinsa ya nufi masaukinsa ya sanjo kaya, ya fito hannunsa rike da kayan da suka 'baci gabanta ya zubesu fuskar nan a murtuke yace."Gashi nan ki wanke min su tas! maganin mara jin magana kenan ni naji dad'i ma da kika fad'a rami da karyewa ma kikayi da kowa ya huta."
Baba Ladi da baba marka suka sanya salati jin abinda ya fad'a! da sauri ya fice daga gidan yana dariya yasan idan ya zauna to zasu caccake shi
Baba Ladi tace"Haba jama'a wannan 'kiyayya tayi yawa yarinya tsautsayi ya sameta amma kace dama karyewa tayi aikuwa ba fata akeyi ba ko karyewar tayi sai an daura auran nan in yaso sai ka ajiye aikinka kayi jinyar ta wannan ai mugun nufi ne kuma ka jibgo mata wanki kaya masu nauyi irin wannan kace ta wanke saboda rashin son gaskiya ni kam jikina ya soma sanyi da al'amarin nan." Baba Marka tace"Ai kin gani da yake ya san bashi da gaskiya ai ya gudu hummm! Allah dai ya kyauta shine abunda zamu ce."
Ummi ta dinga matsawa Sayyada kafafunta har ta dan ji dadi kana ta zuba mata ruwa ta wanke jikinta ta sanjo wasu kayan ta fito tana fad'in"Baba banu Klein din da zanyi masa wankin."
Baba Ladidi ta bude baki tana kallonta cike da mamaki tace"Ashe da gaske wankin zakiyi masa."!? Sayyada ta zumbura baki.Baba tace" Oo! ai ba hanaki nayi ba duba kan tagar can zakiga sabon omo ki dauko kiyi masa wankin dashi.
Sayyada ta dauko Omo ta zuba ruwa tas! ta wanke masa t_shart dinsa da wandonta ta shanya su sannan ta wanke nata kayan da suka 'baci.....Ko da Baba ta gama dahuwar kazar amare Sayyada bata sha wahala gurin sayyada ba a take ta cinye rabin kazar baba ladidi taji dadi sauran da ta rage tace"Zata d'umama mata da safe.