← Book details Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 30

Sashe 20

Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***
Sai bayan motarsu ta hau kan kwalta ne sannan ya sauke ajiyar zuciya Captain Habu ya kalleshi a nutse yace."Don Allah ka dinga sassautawa zuciyarka wani abun mana Abokina nasan akan abunda kake wannan hucin! kar ka manta da cewar yarinyar nan fa bata da waye ba irin ta mutananmu sannan akwai kuruciya a tare da ita zafin zuciya ba shine zai sanya ta dawo yanda kake so ba kai da kanka zaka dinga nusasheta ga yanda zatayi karka ina biye mata ina koya mata mu'amula ne Amma yanzu kishi ba naka bane."

Wata ajiyar zuciyar ya sauke yace."Habu ina kishin yarinyar mutuka bansan meye dalili ba ko da kai naga tana magana sai raina ya 'baci! yau da ban san waye kai ba da sai na d'ora allon zargina akanka to nasan kai ba irinsu bane ba zaka tsare min mutuncina da kyau.....Aboki ina jin tsoron aje Sayyada cikin breeck dinmu yarinyar nada rawar kai sosai kuma kasan akwai ma'kiyana a gurin sannan akwai 'yan iska irinsu Shu'aibu, duk sanda na tuno hankalina na tashi mutuka."!

Captain Habu yace."Kome xakayi kayi da kyakkyawar niyya insha Allahu babu abinda zai faru ai akwai masu gadi kuma nima kar ka manta nawa iyalin na ciki insha Allahu babu abinda zai faru zaka sanya ido sosai nima zan sanya ido. Allah zai tsare mana iyalinmu."

Sadam! yace."Insha Allah amma kasanni kasan bani da sauki kan komai Allah duk wanda yayi gangancin shiga hurumi ranar sai dai uwarsa ta haifi wani."!!!! Captain Habu yace."Insha Allahu hakan ma ba zata faru ba." To da wannan magana ta Sadam suka rufe maganar suka shiga wata.

****

Sulaiman ya dawo daga kasar hindu cike da nasarori na rayuwa, tsaraba yanda yayiwa matarsa haka yayiwa Sayyada akwati biyu cike da kananun kaya Pakistan irin na indiya da irin kayansu na kwalliya Mahaifiyarsa ya bawa akwatinan yace."Gashinan a had'a a lefen Sayyada Hajiya Fatsima taji dad'i sosai tana fatan zumuncin yaranta ya d'ore har 'yayansu da jikoki.

****

Yau sauran kwana uku daurin aure.....Ya dawo gida misalin karfe shida da kwata na yamma yayi parking harabar gidan suka gaisa da mai gadi yana kallon motar Sulaiman yasan ya dawo gari, kai tsaye cikin gidan ya nufa

Yana hakimce kan kujer hannunsa da katuwar waya yana latsawa fuskarsa dauke da murmushi me kyatarwa sulaiman kenan matashin da 'yan mata keso ga kudi ka kyau!!!! Sadam! yayi sallama a nutse ya tsaya daga bakin kofar ya kwance takalminsa, Sulaiman ya dago kansa yana kallonsa bai amsa sallamar ba, ya karasa babu yabo babu fallasa ya mi'ka masa hannu"Barka da yamma."! yafad'a cikin wata baud'ad'ddiyar murya wacce kana jin sautinta zaka san babu wasa a cikinta.

Cikin izzah da hakimcewa ta alhazawan birni ya mi'ka masa nasa hannun "Da fatan na same ku lafiya? Ya aiki ina fatan komai lafiya."!?

Hannunsa ya zare yana d'an ya mutsa fuska yace."Aiki alhamdullahi." Sai ya nemi guri ya zauna had'e da d'aure fuska tamau!! Wannan d'agawar! da girman kan! da izzar! da Sulaiman keyi na masifar bashi haushi wai shi nan me kudi ya dinga wani abu wanda shi a ganinsa wannan abun da yakeyi ba karamin hauka bane. Shiyasa duk sanda yaga yana wannan iskancin yake mugun shan kunu ya hade fuska tamau ya nuna masa shi din banza shi din wofi!!!!

Sulaiman ya aje wayarsa ya kalli Sadam! da murmushi a fuskarsa yace."Lokaci nata matsowa ko? idan nayi lissafi dai-dai yau saura kwana uku daurin aure hakane ko."!?

Ba tare da ya kalleshi ba yace."Tabbas! bakayi makuwa ba hakane ranar juma'a daurin aure insha Allah."

Murmushi yayi ya shafa sajansa wannan sararsa ce shafa saje a kai-kai! minti biyar goma kana magana dashi sai ya shafa sajansa wannan d'abiar ma na masifar bawa Sadam! haushi sai ya dinga wani abu tamkar wani boss!!! mtsssw!!!!

Yace."Wai ke don Allah me yasa bakajin shawara ne yanzu da wannan aikin naka zaka iya rike iyali? tuntuni nace kazo muyi kasuwanci ka'ki wai kai dole sai kayi aikin soja! wanda babu komai a cikinsa sai had'ari da tashin hankali kawai kaje a kasheka a banza a wof..........."Ya isa."!!!!!!! kafin ya 'karasa maganar ya katse shi a mugun fusace! ya mi'ke tsaye....Sautin muryarsa da yanda yayi maganar a zafafe shine ya fito da Hjy Fatsima daga kicin jikinta na 'bari! tace"Meke faruwa ne."!?

"Wai Mama wannan guy ina ruwana dashi ne? me ya dameshi da rayuwata da abinda na za'bawa kaina ina ruwansa da iyalina ina ruwansa da aikina aikin soja na za'bawa kaina ba dan kudi ko daukaka ba ba don nayi suna ko a sanni ba na za'bi aikin soja ne domin na taimaki 'kasata ! Najeria wani gardi! 'katon banxa bai isa ya sauya min ra'ayi ba don haka Mamah tun muna shaida juna ni dashi kija masa kunne babu ruwansa dani ya ri'ke girmanshi idan ya sake ya fad'i a gurina to zan bi takai in tattaka in wuce!!!! maganar Iyalina babu ruwanka da ita meye dameka tunda banzo nace ka taimake ni ba bana fatan zuwan wannan ranar albashina ya isheni na rike matata da 'yayana Kai! kake son duniya da har kake shirya zama a cikinta kana kawatata ni duniyar ma ba a gabana take ba mtwwwws."!!!!! Yana gama maganarsa ya buga hannun kujera fuuuuuuu! ya fita dafa palon.

Hajiya Fatima ta zaune kan kujera jikinta duk a sanyaye ta kalli Sulaiman da ya wani marairaice fuska tace" Meye ya had'aka da d"an uwanka shin ka manta zafin zuciyarsa ne."!? Yace."Wallahi Mama ba wani abun bane me zafi ya hasala kawai ina bashi shawara ne kin san dai saurin daukar zafi irin nashi."
.Tace"Ni narasa me yasa bakwa jituwa da juna kaine babba don Allah ka cigaba da hakuri da halinsa ko bayan raina kuyi zumunci insha Allahu shima ya fara ajiye iyali zuciyarsa zata sassauta."
Yace."Karki damu Mamah! insha Allahu zan cigaba da tausar zuciyata a kansa." Hjy Fatsima ta mike ta koma kicin.
Suleiman shiru yayi yana tunanin abinda ya faru tsakaninsa da Sadam! girgiza kai kurrum yakeyi ransa a masifar 'bace! Ana kallo Sadam! nayi masa abinda yake so savoda tsabar kin gaskiya ace yayi hakuri shine babba to babu shakka hakurinsa ya 'kare zai dauki tsatstauran ma taki a kansa.

*Tofa! Yanzu aka fara labari*

9/6/2020

*BINTA UMAR ABBALE*

_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga duk mai bukatar karantawa sai ya tura kudinsa ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank idan kuma katin waya mutun zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din zan fad'a masa yanda zai biya kud'in....08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar littafin to sai ku tura dala dari ta wannan numbars.....90899076 _88137740 katin airtal ko orange.....Dala dari itace a madadin dari uku na najeria.*_
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________

*Free Pege16*
*_Na kusa gama free Pege ga duk me sha'awar cigaba da karanta book d'in to sai ya garzayo yazo ya biya kudin karatu domin jin yanda wannan bada'kala zata kaya._*
*Yana* fita ya nufi sashensa watsa ruwa yayi ya fito 'kungunsa d'aure da towel kwanciya yayi kan bed dinsa tare da rintse ido yana tunanin maganganun da Sulaiman d'in yayi masa shi a ganinsa wannan ai ranin hankali ne, kan me zai sanya masa ido kan harkokinsa akan me zai dinga kushe masa aikinsa Sojoji nawa ne suka rike iyalinsu da aikin da har yake cewa ya aje aiki ya dawo kasuwanci wato yana so ya zauna a 'karkashinsa kenan! to idan ba haka ba har yaushe zai ce ya ajiye aikinsa ya dawo ya kasuwanci, aikin soja ra'ayinsa ne kamar yanda ya fad'a kuma babu wanda ya isa ya tursashi ya aje aikinsa sai dai idan mutuwa yayi, Haka yayi ta faman Juyi a kwance sai da yaji kiran sallah magariba sannan ya mike ya zura jallabiya mai karamin hannu ya sanya gajeran wando a ciki kana ya fesa turare mai kamshi ya nufu masjid.
Sai bayan sallahr isha'i ya shigo gidan yana cin magani lokacin Alhaji Auwal ya dawo daga kasuwa ya bishi har inda yake suka gaisa da juna Alhaji Auwal yace "Tunda nagan ka anan nasan akwai abinda ke faruwa a brecck din naku." Yace."Kwarai kuwa Abbah aiki ake min a bangarena sunji labarin zanyi aure shine suke min gyare gyare." Alhaji auwal yace."To masha Allah ni kuwa ga shawara ." Yace."Ina jinka Abbah."Alhaji Auwal yace."Me zai hana idan an d'auro auran mun dawo Sayyada ta zauna tare damu sam! bana son zamanta a brecck din nan wallahi." Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace."Nagode Abbah nima na dad'e ina wannan tunanin to kawai bana son in takura muku ne yasa na amince da zamanta a brecck din." Alhji Auwal yace."Kana bani mamaki! Sadam! shin wai su waye iyayenka."!? Yace."Kune Abbah." "To meyasa kake janye jikinka damu ? yanzu dan kazo kace Sayyada ta zauna tare damu sai mu hana kar ka manta fa da cewar dani da mahaifiyar yariyar uwa daya uba daya muke ko babu aure a tsakaninku ni me riketa ne." Yace."Kwarai kuwa Abbah." Alhaji Auwal yace."To don Allah ka daina wannan d'abi'ar taka." Yace."Ayi hakuri Abbah insha Allah." Hajiya Fatsima ce ta fito daga d'aki tana jan akwati ta aje ta dauko dayar tace"Sadam! wannan akwatin d'an uwanka ne ya kawo maka da duk kayan dake ciki yace a had'a a lefe."
Chapter 20 · 0% Book details