← Book details Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 30

Sashe 14

Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin 'yan kwanakin da Sulaiman yayi a garin *Dabi* yayi sune cikin takurewar zuciya gami da tsananin damuwa mutukar zai bud'e ido ya dinga ganin Sayyada a matsayin matar d'an uwansa zai ji kamar zuciyarsa zatayi buga saboda takaici da 'bakin ciki a ganinsa sam! Sayyada bata dace da Sadam! ba dashi ta dace, sai kawai ma ya dinga jin tsanar d'an uwan nasa na d'arsuwa a cikin zuciyarsa a daddafe yayi kwana biyar ya had'a kayansa yayi musu sallama ya tafi......Wannan karon Sayyada bata damu da tafiyarsa ba kamar da inda duk sanda yazo garin to da kuka suke rabuwa da juna, al'amarin sai ya bashi mamaki! mutuka ya lura yarinyar na masifar son Sadam! ganin irin rawar jikin da takeyi kwata-kwata ma bata zama suyi hira kamar da zuciyarsa ta cika fal da takaici da bakin ciki had'e da masifaffan kishin 'Dan uwansa a duniya yana ganin bashi da babban ma'kiyi sama dashi.

****

Sadam! kam tunda ya koma bakin aiki ya manta da wata Sayyada tinda dama can ba itace a gabansa da ita da babu duk d'aya suke a gurinsa babban abunda yafi damunsa shine yanda zai d'aukota ya ajeta cikin brecck d'insu wanda ya tara mutane mabambamta ra'ayi da addini kowa yana yin abinda ya ga dama duk kuwa da cewar wasu daga cikin su akwai iyalinsu a ciki hakan baya hanasu shaye-shayen su da neman mata idan ta kama suje club ranar da suke hutu haka kowanne zai fita cikin mota wasu su dawo wasu kuma su kwana can marasa kunyar cikinsu kuwa har mata suke kawowa al'amarin dai ya 'kazanta babban abinda yake tunani kenan zaman Sayyada a bracck din yasan halinta da shegen rawar kan tsiya kuma duk da ba wani sonta yake ba to dole ne yayi kishin auransa sam! baya so wani shege ya kalleta balle ya 'kyasa....! Sadam mutum ne mai kawaici da kau da kai ga abinda bai shafeshi ba shiyasa suke ganin mutuncinsa shaye-shaye da neman mata duk Allah ya tsare shi kawai ku barshi da busa haya'kin sigari yana shanta sosai mussaman idan yana cikin 'bacin rai! le'bansa ya d'an soma ba'ki kad'an amma sai wanda ya 'kura ido yake ganewa sam baya shan sigari a idon jama'a shiyasa iyayensa basu taba sanin yana sha ba kuma baya ta'ba yarda kaji warinta a jikinsa mutum ne mai tsaftar gaske kuma yana da ri'kon addini dai-dai gwargwado sai dai fa mugun muskili ne wanda baka ta'ba sanin abinda ke cikinsa saboda tsabar zurfin ciki ko yana son abu baya ta'ba nunawa komai yana bi a sannu baya rawar kai.....Ga yanayin 'kwayar idanunsa zaku gane cewar shi d'in mutun ne mabukaci ina nufin mutum ne mai yawan sha'awa shiyasa yake yawaita azimi saboda wannan matsalar amma saboda tsabar cutar kai ya'ki ya tsaya ya kalli mace ma ballanta yayi tunanin aure....Duk cikin family d'insu shi kad'ai ne ba'ki shima ya d'auko fatar mahaifiyarsa ne kasancewar ta 'yar asalin garin Maiduguri kasuwanci ya kawo mahaifinta Kaduna amma yawanci danginta na can barno da zama Hajiya Fatsima tana da kyau sosai sai dai 'bakace Sadam! sai ya dauko yanayin fatar ta amma kuma ya fita haske saboda shi tasa fatar sai ta kasance tamkar ta ba'ka'ken turawa black America yana da dogon hanci da manya idanu wanda kusan kullum suke a lumshe sai yana filin daga sannan za kaga ainihin hallitar idanunsa amma haka kawai gari banxa baka isa kaga ya ware maka dukanin idanunsa ba ko kallon mutum zaiyi ta 'kasan ido yake kallonka saboda tsabar munafurci haka duk yake 'karewa matan mutane kallo dake yana da yalwar gashin ido idan yana kallonka baza ka ta'ba ganewa ba.....Dogo ne shi amma ba sosai ba yana da fad'in kirji da murd'ad'an jiki wanda yasha training sannan jikinsa du gargasa ce mussaman kirjinsa da kafafunsa kusan kullum cikin gyaran fuska yake saboda yanayin hallitarsa domin ita kanta sumar kansa abin kallo ce yana bala'in ji da ita da kashe mata kudi wanda baza su ta'ba lisaafuwa ba.

Sayyada Fara ce tas saboda tsabar haskenta har yalo takeyi mussaman idan taji rana to ita abun ne ya had'e mata biyu can bangaran mahaifinta fulani ne suma sannan bangaran babarta ma haka shiyasa abin yayi mata yawa tana da gashi sosai gashi ba'ki mai santsin tsiya wanda ko kitso ma ba ya zama a jikinda sai dai kawai ta gyara tayi gammo dashi......Siririya ce tamkar ka bushe ta ta fad'i amma kuma idan ka kalli yanayin jikinta mussaman tsintsiyar hannunta da zara zaran yatsunta zaka fahimci cewa gaba kad'an idan ta samu kulawa da abinda take so zata cika ta batse.....Tana da wani irin sharp mai fizgar hankali cikinta a shafe tamkar bata cin abinci sai dai kas! babu nonowan arziki a kirjinta kananu ne wanda itama duk kankantar hannunta baza su cika su ba, Ko da yake ai akwai sauran shekaru a gaba zasu fito sosai.

Sayyada mai kyauce wanda kallo daya kayi mata zaka so ka sake kallonta tana da kyawu bayyanan ne kewayayyiar fuskarta na dauke da dogon hancinsa sa siraran le'bunanta masu d'an tudu kad'an bata da manya ido sosai sai da Allah ya wadata ta gashin gira dana ido gazar gazar dasu abin sha'awa idonta kamar tasa sanya kwalli shiyasa sam bata damun kanta da lallai in tayi wanka tasa kwalli ba saboda ita Allah ya zana mata a idonta.

Sayyada nada rawar kai sosai bata cuta amma ba yarda a cuceta ba Allah ya sanya mata kauna da son Sadam! tun bata kai shekarun haka ba take sonsa idan yazo garin takan shiga cikin wani yanayi mai dadi haka kurrum yanayinsa da yanda yake tafiyar da rayuwarsa yake burgeta tsaftarsa da kamun kansa na burgeta da bata sha'awa tun lokacin data girma taji labarin auransu tayi ta murna da farin ciki tana fadin mutukar ta auri Sadam ta gama dace da mijin aure.

****
Sulaiman fari ne tas dogo dan ya d'ara Sadam a tsayi sai dai Sadam din ya fishi cika ido Sulaiman kyakkyawa ne ajin farko kuma dan boko ne duk a 'kidunsa na nasara ne domin ma bai cika tu'ammali da manya kaya ba sai da kananu Yayi aure shekaru biyar da suka wuce matarsa ko 'batan wata bata ta'ba yi ba sai wannan karon ta samu ciki yanzu dai cikin nata nada watanni takwas.

Amina tana da hankali da nutsuwa ta girmi Sayyada da shekeru uku shiyasa tafita hankali Amina gajera ce bata kai tsayin Sayyada ba amma tana da kirar jiki mai kyau fatarta luwai luwai sannan Allah ya wadata ta da nono masu daukar hankali tana da sauki hali mutuka don magana ma bata dame ta ba, ba kamar Sayyada ba da in tana guri sai ta gundiri jama'a.
A tsakaninsu akwai sha'kuwa sosai da fahintar juna Amma tun sanda Sayyada ta lura da yanda Aminar ke shishshigewa Sadam yasa taji ta soma tsanarta Sai ta rage shiga kofarsu sai dai Aminar ta shigo to idan ma ta shigo kofar tasu Sayyada watarana basa wanyewa lafiya da fada suke rabuwa.

Duk Wasu abubuwa na bukatar rayuwa Alhaji Auwal da 'yayansa na kokarin ganin sun kawo musu don haka basu da matsalar abinci da abun bukatar rayuwa Baba Ladidi ce kawai 'yar rigima ita lallai sai ta dorawa Sayyada tallah,ita kuwa Baba Marka tana kad'a lagwanin risho ne 'yan yaran matan dake unguwar wanda basa aiki da itace suke siya wannan shine sana'ar da takeyi daga zaune. itama Baba Ladidin ganin Sayyadar ne yasa take d'ora mata tallah amma da babu ita dole ne ta hakura tayi sana'a irinta Baba Ladidi.

Wannan kenan.

****

Yana zaune a ofis Captain Habu ya shigo hannu ya bashi suka gaisa kana ya zauna kujerar dake fuskantarshi hankici ya ciro daga aljihunsa ya goge gomin fuskarshi ya kai kallonsa kan Sadam! da yake faman duba wasu takardu yace."Wai ya zamuyi ne da tafiyar da take tun karo mu kasan Allah ni jin tsoron tunkarar wannan 'kauyen da babu wani dan adam din da yake rayuwa a cikinsa Ina jin tsoron mutanan sosai domin sharrinsu yafi na tsohowar mota."

Ya d'ago kansa yana kallonsa fuskar nan a murtuke yace."Wai ke me yasa kake hakane? tamkar ba namiji ba kar fa ka manta da cewar wannan aikin da kakeyi ka dauke shi ne da al'kawari ko kashe ko a kashe ka gabakidaya rayuwarka kar ka sanyata a ranka komai zakayi to kayi da zuciya d'aya tare da taimakon neman taimakon Allah, ladanka yana gurin Ubangiji Sannan kuma ka daina jin tsoron wani hallita in ba Allah ba Allah da manzonsa su kadai ne suka cancanta da muji tsoro ba wata hallita ba, ni ka ganni ko Wallahi Wallahi! Wallahi! kaji nayi maka rantsuwa sau uku ko!? mutukar kaga ba'ayi wannan tafiya dani ba to bana nuffashi a doron duniya, a yanzu babu abinda yake gabana sai tunanin yaya za'ayi mu ci galaba kan wad'annan azzaliman mutanan."

Captain Habu ya girgiza kai yana kallon Abokin nasa yace." A gaskiya ni ina jin in shigar da uzirina gurin Yalla'bai domin jikina na bani gagarimun al'amari zai faru kaga ni ina da iyali da yara gwara kai baka aje kowa ba kuma a zahirance kai ka fimu taurin zuciya da jajurcewa da hikimar ya'ki ina ganin zaka iya tseratar da ranka in wata matsala ta afku"

Murmushin takaici yayi ya aje biron dake hannunsa yace."Wai Habu don Allah waye meyi ne."? Habu yace."Allah ne." Sadam! yace."To amma ka kasan da haka ka kasa yin tawakalli ka bar masa lamarinsa, idan fa mutuwa kake tsoro to ko kaje ya'ki ko ba kaje ya'ki ba idan lokacin ka yayi sai ka mutu gwara ma a kashe ka gurun ya'ki kasan kayi jihadi makomarka Aljanna kuma kana maganar Iyali ni waye ya fad'a maka bani da iyali ina mai tabbatar maka da cewar yau saura sati biyu kacal daurin aure na." Captain Habu yayi saurin d'ago kai yana kallonsa da mamaki a tare dashi....Sadam! ya d'aga masa kai yana so ya tabbatar masa da gaskiyar magana yace."Iyayana sun had'ani aure da 'kanwata dake can garinmu *Dabi* So kaga magana Iyali ba kai kad'ai zakayi ba har dani."
Chapter 14 · 0% Book details