← Book details Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 30

Sashe 26

Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Saboda me."?tafad'a tana kallonsa....." Ke! ni nake magana kina tambayata." ! ya fada yana kwalalo mata manyan idanunsa....Ba taji tsoro ba sai ma zumbura baki da tayi...."Ko ba kyaji ne."!? banza tayi masa. Duk tausayin kanta ya cikata Yaya Sadam! baya sonta sai wulakantata yake sai idanunta suka soma kawo ruwa, Idanunsa a tsaye a kanta ya gani da sauri yace."Karki kuskura hawayen nan ya zubo." Ai ya 'bata bakinsa don tuntuni hawayen ya tsinke sai kawai ya saki baki yana kallonta Dr ne ya shigo tayi sauri ta 'boye fuskarta cikin hijab, Ganinsa kan dadduma yasa dr fad'in"Alhamdullahi Yalla'bai da alama ba zaka dade a kwance madam ta iya jinya." Hannu ya bashi suka gaisa dr ya duba jikin nasa kana ya bashi magani yana fad'in''Ni zan dinga baka magani da safe Madam kuma ta kula da kai da rana da dare ." Yace."Kai ma na huttashe ka ai ba yaro bane ni zan sha magani da kaina." Dr na dariya yace."A'a Madam ya fi kamata ta baka zakafi samun sauki da wuri." Murmushi kawai yayi dr yayi masa sallama ya fita.
Mi'kewa yayi ya isa gadon ya zauna yana kallon bayanta shiru babu wanda yayi magana ya sanya hannu yaja hijab din ta baya ta rike wuyanta da sauri ta juyo tana kallonsa, Sai ya saki hijab din ya kwanta rigingine ba tare da yace mata komai ba ita kuma hakan da yayi sai ya sake tunzura ta ta mike zata fita daga d'akin!....."Sayyada."!!! Ta jiyo muryarsa na kiranta ko kallonsa ba tayi ba ta bude kofa ta fita, sai suka ci karo da Captain Habu da Saleh zasu shigo dake kofar a bude take duk yana hangosu yana kallon tana gaishesu har shi Captain Saleh din da yake mata wani irin kallo.....Ransa ya 'baci! yarinyar nan ta raina shi wato yace kar ta fita sai da fita! ga matsiyacin nan yana kallonta Captain Saleh anyi d'an akuya......Habu yace."Sayyada ina zakije." ? inda inda ta hau yi yace."Muje ciki." gaba tayi suka rufa mata baya........Xaune suka same shi fuskar nan a murd'e fatar goshinta duk ta tattare kana kallonsa zaka fahimci ransa a 'bace yake.

12/6/2020

*BINTA UMAR ABBALE*

_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga masu bukata zasu tura kudin ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars zan fada mata yanda zata biya kudin....08089965176 _07084653262.......Mutanan Nijar idan kuna bukata to zaku tura dala dari ta wannan numbar....9089976 _88137740 katin airtal ko orange Dala dari uku kudin Najeria.*_
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________

_*Na kusa gama Free Peges ga duk me bukata sai ya garzayo ya biya kudin karatu*_
*Free Pege19*
Jiki a sanyaye taje bayansa ta zauna tare da rufe jikinta da hijab idanun saleh na kanta sai ya soma zargin wani domin shi duk abinda akeyi bai sani ba bai san cewar Sadam din yayi aure ba tunda ba shiri suke da juna ba, ammafa ganin farko da yayiwa yarinyar ya kwadaitu da ita tabbas idan ta kasance matar Sadam! ce ita to kuwa duk yanda zaiyi sai yayi ya biya bukatarsa ko dan ya kashe sadam din da bakin ciki Sakin fuska yayi tamkar ba mugu ba ya duba sadam din yana tambayarsa jiki duk gurin sai da sukayi mamakin sauyawarsa lokaci guda Sadam kam baiyi wani mamaki savoda yasan Saleh ba karamin makirin mutum bane.
Duk da yayi kokarin danne 'bacin ran dake damunsa amma duk da haka Habu ya fahimci yana da damuwa,Sama-sama suka gaisa da abokanan aikinsa inda ya na hankalce da inda Captain Saleh yafi mai da hankali gurin kallo sai yaji tamkar ya tashi ya Nausheshi saboda takaici, Captain Saleh mayen mata ne shi yasa kwata-kwata baya son zamanta a bracck din saboda irin su Saleh a kwai hadarin gaske......Hira sukeyi sama-sama, ba tare da ya sanya musu baki ba, Sai da ya gaji da abinda Saleh keyi masa yace."Ya kamata fa ku shiga ofis naga lokaci ya wuce." Dukaninsu suka mike sukayi masa sallama, Saleh har da waiwayen Sayyada saboda tsabar jaraba.

Suna fita ya mi'ke zaune yace."Ke! juyo nan ki kalleni." Juyowa tayi tana kallonsa kana kallonta kasan a tsorace take domin miryar da yayi mata magana kamar ba ta mutum ba.

"Baki isa kizo ki zubar min da mutunci ba." Ya fad'a yana zare mata ido! ya cigaba da cewa meye amfanin xamanki anan da zakice dole sai kin zauna tare dani me kike tsinana min ? daga anyi magana sai ki hau kuka bakyajin maganata nace dake Karki fita sai da kika fita ni da bakina nace kar in kara jin wani namiji ya shigo kin gaisa dashi saboda ban isa ba naji da kunnena kina gaisawa da Saleh! To yau d'in nan zaki bar brecck din nan ko 'kinki ko kinso idan kukan jini zakiyi sai dai kiyi na gama magana."""" Shiru tayi masa idanunta ya kad'a yayi jawur! Sadam baya sonta yanzu meye laifin wanda ya kula da kai da rayuwarka kan kawai tace zata zauna tare dashi yake wulakanta, Hawayen da take ta kokarin dannewa suka fara zuba.....Yana jinta tana shashshekar kuka yaki kallonta lumshe idonsa ma yayi bacci na daukarsa,Motsin bude kofa yaji ya bude ido ita kuma tayi saurin sanya gefan hijab dinta ta kare fuskarsa.

Sulaiman ne ya shigo cikin Shadda galila 'yar gasken anyi masa d'in 'yan birni yayi kyau sosai kamshi ne kawai yake tashi a jikinsa.

Babu yabo babu fallasa ya amsa sallamarsa Sayyada najin muryar Sulaiman ta bude fuskarta, Sulaiman ya karaso bakin gadon ya tsaya yana kallon Sadam! din A hankali yace."Ya jiki."? "Alhamdullihi." Yafada ba tare da ya kalleshi ba. "Yaya Sulaiman ina kwana ya kwanan Aunty Luba."!? Ya Juyo yana mata wani sihirtaccen kallo fuska a sake yace." Lafiya lau baby Sayyada dake haka yake kiranta tun tana yarinya ya cigaba da cewa "Ya mai jiki? ina fatan komai lafiya."
Da gefan ido ta kalleshi taga ya wani ci kunu! gabanta na faduwa tace"Jiki da sauki wallahi." Shiru dakin yayi Sadam! na mamaki wato duk hargagi da masifar da zaiyiwa yarinyar ba zata ji maganarsa ba dole ya koya mata zama.

Sulaiman ya kalleshi a nutse yace."Babu abunda kake bukata ko? Ko da yake ma naga jikin da sauki Allah ya takaita wahala." Wannan magana da Sulaiman din yayi ta tun zura masa zuciya domin shi a yanda ya fassara maganar kamar ta rainin hankali ne *Allah ya takaita wahala* Idan bai manta ba akwanakin baya Sulaiman ya sha cewa dashi ya rabu da aikin soja saboda a cikinsa akwai babban kalubale sannan mutum yazo ya mutu a banza a wofi bai cimma shekarunsa....Wannan magana da ya fad'a ta nuni da irin maganganunsa na baya....Kamar ya bashi amsa dai-dai dashi sai kawai ya kyaleshi domin baya so su raba hali a cikin mutune amma hakika abinda Sulaiman din keyi masa ya soma wuce makadi da rawa.

Hira sukeyi yana jinsu dama can yasan akwai shakuwa a tsakaninsu bai wani damuba tunda bai ga an wuce gona da iri ba, shine dalilin da ya sanya ya rabu dasu suke maganganunsu na can Garinsu *Dabi* Bai tanka musu ba ya dai kasa kunne yana jinsu........"Sadam! ni zan wuce kasuwa Allah ya sawake, ya ta'kaita wahala."! Sai ya bud'e idonsa da saurin gaske ya mike zaune " Dakata malam kar ka fita tukkuna sai ka tsaya ka fad'amin ma'anar wannan kalmar da kake ta nanatawa tund'azu."!! Cikin 'karfin murya yake maganar yana wani irin haci!!! Sayyada cikinta duk ya d'ori ruwa mutum ma na kwance bai da lafiya amma ba zai bar masifa ba.

Murmushi yayi yace."Saboda nayi maka addua kake tuhuma Sadam! *Allah Ya takaita wahala* yanzu ma na 'kara fad'a." Ya fad'i maganar yana d'aga kafad'a alamun bai damu ba.

Yace."Kai! baka isa kayi min addua ta kar'bu ba ka sani Allah na kar'bar adduar mai kyakkyawar niyya ne me kyawun zuciya kai kuwa fa kullum zuciyarka ba'kikkirin take baka nufin mutun da alkairi sai sharri Ni! nafi karfinka wallahi baka isa kayi min abinda Allah baiyi min ba, bana nadamar na rasa raina a aikin soja! saboda nasan nayi aiki domin Allah da mazonsa zan samu kyakkyawan sakamako gurin Allah."

"Ni kake fad'awa wannan maganar."! ? Sulaiman ya fad'a ransa a mugun bace."!
Chapter 26 · 0% Book details