← Book details Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 30

Sashe 21

Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kici-kici yayi da fuska yayi shiru! tace"Naga ka 'bata rai kai bakace komai ba sai hidima ake maka kana kwance."! Yace."To Mamah me zance." Tace"kace ka gode sannan don Allah ka rage zafin rai ka zauna da kowa lafiya d'an uwanka na son ku zauna lafiya amma kai kullum cikin fushi da d'acin rai wannan ba sara bace." Yace."To Mamah! na daina isha Allah." Yasan in ba haka yayi ba to zata dinga nanata maganar ne. Tace"To ka bude kayan ka kalla yace."to duk dan ya faranta mata rai ya bude akwatinan yana dubawa kayane na gani na fada masu masifar tsada sarkoki abubuwan hannu dogwayen riguna dasu pakistan turarrika masu kamshi da tsada.....Sai Uban 'kananun kayan bacci masu kyau.....Sam hankalinsa bai kwanta da kayan ba don ba yarda zaiyi ne ya rufe akwatinan yace."Kaya sunyi Mamah." Tace"To ko kaifa gobe zamu tafi can *Dabin* zamu tafi da akwatinan lefan su gani in yaso sai a dawo dasu. yace."Hakan yayi kyau." To hira ce ta 'barke a tsakaninsu, Sadam! na fad'a musu banan babu wata uku zasuyi tafiya zuwa wani 'kauyen 'kayau dake can cikin Maiduguri domin kwantar da tarzomar da take tashi a yanki wanda masana bunkice sukayi itifakin cewa 'yan boko haram din da suke cikin wannan yanki suna da yawa kuma mafiya akasari sune suke sajewa da mutane su fito cikin gari da cikin kasuwanci suyi aika-aika su gudu kuma neman duniya ba'a ganinsu duk kuwa sojan da yayi gangancin shiga wannan kyauye to sunansa matacce, sai mai tsananin rabo ne yake dawowa da ransa amma fa sai yayi jinya me tsayi domin sai sun rautana shi.
Daga jin yanda yake basu labarin had'arin dake cikin 'kauyan sai duk jikinsu yayi sanyi Hajiya Fatsima tace"Sadam! daka hakura da zuwa wannan gari jikina har yayi sanyi da jin wannan magana." murmushi yayi yace."Mamah mutukar kikaga banje wannan jihadin ba to bana numfashi a doran duniya ke dai addua kawai zaki cigaba da yi min." Tace."To Ubangiji Allah ya baku nasara ya kuma dawo mana daku lafiya."Alhaji Auwal dashi Sadam! din suka amsa da "Ameeen Ya rabbi."!

***
Amarya Sayyada fa sai gyara take sha ta ko wanne fanni domin can 'bangaran mahaifinta ma kullum sai sun kirata sun turara mata jiki da had'in turare sannan sunyi mata dame-dame na maganin gyara tasha sun shafe ta da lalle tare da bata rubutu na tsari a cewarsu wannan lokacin ne ya kamata su nuna mata kaunar da suke mata, Mahaifinta yayi mata siye-siye sannan ya bata shanu biyu saniya da sa yace amma za'a ajiye mata a garin duk zuriar da ta samu nata ne Sayyada taji dadin kyautar da mahaifinta yayi mata Kakanta maigari ma yayi mata kyauta ta ban mamaki! kowa ya kula da Sayyada a cikin gidan Maigari banda matar babanta Allah ya sanya alkairi ma ta kasa cewa saboda tsabar bakin cikin dake damunta

*Wannan kenan*

Cikin 'yan kwanakin da Sayyada tayi tana shan magani gami da kar'bar gyaran jiki sai ta ciko sosai tayi kwarjini kyawunta ya sake fitowa fatar jikinta ta goge sosai ta zama abin sha'awa in ka ganta sai ka rantse da cewar cikin birni akayi mata gyaran amare saboda yanda ta koma, Kullum tana gidan Mariya tare da Ummi da sauran kawayen su suna shirya yanda al'amarin biki zai kasance.....Amina ta 'karfi da yaji ta shiga cikinsu ta saki jikinta ana hidima da ita tun suna zaginta suna mata dariya har suka kyaleta domin ta kiyin zuciya.....Ummi ce ta yankawa Sayyada salatif mai tsari da burgewa suka hada lalle yanda zaiyi kyau yayi kamu! aikuwa Sayyada ta fito ras da ita jan lallan yayi masifar kyau abinka da farar fata.
Kitsone Sayyada tace bata so saboda tsan ko anyi ba zaiyi wani tasiri ba, sai Mariya ta dinga tsokanarta tana fadin ai gwara ki kitse kanki wallahi don kin san kullum sai ya jike da ruwan wanka." Dariya suka sheke da ita suka tafa Sayyada tace"Ke nifa yanzu na fara jin tsoro wallahi."Mariya tace."Duk tsoranki baki kaini ba gashi ni na hakura na zama 'yar gari." Haka suka 'bata lokaci suna hira kafin suyi sallama da Mariya su nufo gida.

****

Yau Juma'a uku ga watan bakwai shekara ta dubu biyu da bakwai aka daura auran Sadam! da Sayyada, Kan sadaki dubu hamsin wanda Sulaiman ya bada da aljihunsa wannan al'amari yayi masifar 'batawa Sadam! rai da kansa ya bada sadakin auran sa naira dubu talatin amma saboda tsabar son a sani yayi gaggawar mi'ka nasa sam bai wani burgeshi ba ya fi son komai yayi da kansa tunda har ya fara goranta masa kan aikinsa to baya so ya gaza ta ko wanne fanni.

Labarin daurin auran na isa cikin gidan Sayyada jikinta yai 'kwata'kes! salo-salo taje ta kwanta kan gado gabanta na fad'uwa! gayyar 'kawayenta ne da suka zo suka sanya ta saki jikinta duk sunci kwalliya dai-dai gwargwado amma kuma kana ganinsu zaka gane akwai banbaci da 'yan cikin gari......Itama amaryar tana sanye da Swiss les purple anyi mata dinki stone work dake duk Hjy Fatsima ta bayar an dinka mata rabin kayan lefan dinki irin na 'yan birni Sayyada tayi kyau sosai ta gyara gashinta ya sauka gadon bayanta ta yafa dankwalin les din kana sanya takalmi plete da pose irin ta amare tayi kyau sosai sai dai kana kallonta zaka gane bambamci da ita da amaryar cikin gari sannan kuma akwai yarinta a tare da ita tunda yanzu ba tafi shekaru goma sha hudu zuwa sha biyar ba........Jama'ar da suka cika gidan suka dinga janta da wasa tana dai daurewa tana gaishesu da abun yayi yawa kawai sai ta fashe da kuka ta rungume Baba Ladidi to itama Baban ashe 'boye kukan take ganin Sayyada nayi sai itama ta fara nata aka rasa me basu hakuri su hakura....Cikin wannan hali suka shigo gidan....Sadam! da Sulaiman kaya iri daya ne a jikinsu shadda ce galila dinkin babbar riga, Sulaiman fuskarsa a sake ya dinga gaisawa da jama'a shi kuwa gogan bai wani tsaya sosai ba a gurin tunda yaga abinda yake faruwa takaici yasa ya bude dakin da suke sauka ya shige har da turo kofa....Sulaiman kam wayarsa ya fito da ita ya dinga musu hoto yana dariya sai da yaga abun nasu yana nema yayi yawa sannan ya soma rarrashinsu da kyar suka daina kukan Jama'a kuwa sai dariya ake musu.

Yana daga kwance cikin dakin yana jiyo abinda yake faruwa juyi kawai yake yana mamakin zubar da girma irin na Sulaiman yana jiyo muryarsa yana tsokanar Sayyada ji yake kamar ya tashi yaje ya kwad'e shi don takaici......."Yaya Sulaiman bamu wayarka muyi selfie." muryarta ya jiyo cikin taratsi tana wannan maganar.....Kafin ya ankara yaji sulaiman din na cewa"Muje inyi muku keda 'kawayen naki." Firgigt! ya mi'ke zaune rigarsa da ya cire ya dauka ya sanya ko botiran bai mayar ba ya fito fit!!! ai tuni sun fice daga gidan.....Kai tsaye hanyar fita ya nufa, yana jin yan biki na fad'in"Ango kasha kamshi Allah ya sanya alkairi." bai ce komai ba yayi gaba........Can baban soro ya riskesu suna ta hauka shi kuma Sulaiman din sai biye musu yake yana dariya harda Mariya da take matar aure ta cire mayafi tana gantsare-gantsare wai ita dole hoto takeyi tana so tayi kyau........."Wannan wane irin hauka ne."!!!! muryarsa ta sanya suka juyo da sauri....yana tsaye da fuska a daure ya hard'e hannunwa a kirji yana watsa musu dan iskan kallo....Ya kalli Sulaiman cikin takaici yace."Wannan dai ba girman ka bane wallahi karfa ka manta da cewar wa d'an nan yaran ba irin 'yan matan cikin gari bane babu abinda suka sani bayan haka kuma akwai matata a cikinsu dai-dai kenan kazo kana daukarsu a hoto kana dariya."
Chapter 21 · 0% Book details