Sashe 11
Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rife fuskar ta tayi tana murmushi tace"Wayyo Yayana wai na sauya maka ne naga sai kallona kake tun da kazo." Ya saki murmushi mai kyatarwa yace."Sosai kika sauya min Sayyada kin girma kin zama cikakkiyar mace alhamdullahi ina rokon Ubangiji ya baki miji nagari wanda zai kula dake."
Murmushi kawai tayi tace "Yayana ina auntyna." Yace."Tana nan lafiya lau da da tare zamu zo to saboda yanayin jikinta ne ya sanya nace ta bari sai ta haihu sai na kawo ta ta kwana biyu tare daku."
"Wayyo Allah ashe auny Luba ta kusa haihuwa kai gaskiya naji dad'i wallahi Allah ya sauke ta lafiya." Yace."Ameeen ya rabbi Sayyada ya karatu ina fatan kina mai da hankali ko." ? Tace"Eh Munayi yayana A dai taya mu da addua."Yace."Idan kina so in tafi dake can kaduna mana sai ki cigaba da karatun ki a can ni sai nake gani kamar bakya mai da hankali anan." Jiki a sanyaye tace"Wallahi ina karatu Sosai Sai dai kasan makarantun cikin birni da irin namu ba d'aya bane amma nima ina ganewa sosai." Yace."Okey zanzu kuna jiran jarrabawa ta fito kenan." Tace"Eh kuma isilamiyya ma mun had'a izifi ar'bain." Yace."Alhamdullahi to kafin in koma za muyi karatu ni dake sai in gani shin da gaske kike kina fahinta ko kuwa." dariya tasa tace"Tom ai kuwa zan baka mamaki."! Mikewa tayi tace"To bari dai in dora maka abinci ko." murmushi yayi ya bita da kallo yana ayyana abubuwa da dama a kanta.
Baba Ladidi ta shigo da daurin buhu a hannunta wani a kanta tana ganinsa a ki shingide ta saki fuska da fara'a ta karaso tana fad'in"Ashe bature ne a gidan namu sannu da zuwa ai jikina yayi ta bani dama zanyi babban bako." mikewa yayi zaune yana mata sannu da zuwa tare da bin buhuhunan da take ajiyewa da kallo.
Mayafin dake saman kanta ta cire ta rataye a giya tace"Sayyada kawo min ruwa nasha kafin mu gaisa da mai gidan nawa." Sayyada ta mika mata ruwa cikin kofi da ta d'ebo a randa Baba Ladidi ta shanye ruwan tas ta aje kofin kafin kice kwabo gumi ya yanke mata sai ta fara neman mafici Sayyada ce ta mika mata ta hau fiffita tana fad'in"Kai nasha rana wallahi ai da yake yau juma'a shine kowa ya fito ya ci kasuwarsa amma ai bukata ta biya tunda na samo abinda nake so."! Yace."Wai Baba daga ina kike haka kin dauko rana gaki dauke da buhuna sai kace wacce zata bar gari."
Baba Ladi ta gyara zama tare da jawo buhun da ta shigo dashi tana fad'in"Naje na d'an yo sare-saren kayan siye da sayarwa kasan zama babu sana'a babu dad'i ko yaya kana d'an motsawa sai kaga asirin ka ya rufu."
Yace."Idan na fahinta kina so kice asirin ki a tone yake yanzu."!? Tace."Oo!! ni ban fad'a ba ni nace asiri na a tone yake ai idan nayi haka nayi wa Allah butulci.'' Yace"To meye kuma zaki dinga d'aukar rana kina shiga kasuwa salon ki jawo mana zagi menene ba a siya muku na abinda kuka bukata."? Tace"Sulaiman rabu dani don Allah nifa ba zan zauna haka kawai na rungume hannuna ba bana sana'a kawai sai in dogara da wani kuje ku ri'ke abunku ni ku barni na nemi kud'i na." Girgiza kai yayi yace."Ai kaji irinta ita baba Marka me yasa bata sana'ar sai ke ? ke dai kawai kice kina da son kudin tsiya kuma haka zaki tara mana ki tafi ki bari."
Tace"Eh ai haka yafi akan in mutu mutanan gari na fad'in ban bar muku komai ba. Sai dai duk abinda zakuyi kuyi sana'a kam yanzu na fara wancan miskilin ma da ya fika 'bakar zuciya yayi ya gama kuma ya hakura ya kyaleni bare kuma kai."! Dariya ya sanya yace."To ai shikkenan Baba kiyi sana'a Allah ya bada sa'a." Tace"Ameen."
Baba Marka ce ta fito daga daki dauke da kwanon sha ta damo fura tayi luwai taji nono mai kyau ta aje gabansa yace."Ina godiya Baba gyara zamansa yayi ya sanya ludayi ya fara shan furar cikin nutsuwa.
Baba marka tace"Ashe kin dawo to ya kasuwar yau dai da alama babu cikowar jama'a naga kin dawo da wuri." Baba Ladi tace"Aikam akwai cinkoso Allah ne kawai yasa zan dawo da wuri na samo mangwaro masu kyau da za'ki irin wanda yara suke so."
Baba Marka tace"Aikuwa yanzu xaki ga ya 'kare yara da son mangwaro." Baba Ladi ta zazzage buhun mangwaron tace"Kinga irinsu so."!? Da sauri Sayyada tazo gurin tana fad'in"Gaskiya baba mangwaron nan zaiyi za'ki."! Baba Ladi tace"Maza jeki dauki wannan katon farantin ki kasa mangwaron a ciki kije can bakin darbejiya ki zauna wannan mangwaron ba yara kad'ai ba har da manya sai sun siya saboda yana da 'kwari."
Baba Marka tace"Aikuwa dai gaskiya yau kinyi sa'ar zuwa." Sayyada ta dauko katon faranti ta shiga jera mangwaro akai Baba Ladidi tace"Guda daya naira goma shida hamsin." Sayyada tace"To fara bani nawa in sha tukkuna."Tace"Kije ki dawo gashi na ajiye miki masu za'ki." hijab din ta ta zara ta zura ta dauki katon farantin dake ciki da mangwaro zata fita Sulaiman yace"Ke Sayyada dawo da kayan tallan nan." Sai taja ta tsaya ganin fuskarsa a hade yasa jikinta yayi sanyi sam bata son taga yana fushi da ita sai ta dawo ta zauna....Ita kuma Baba Ladidi ta hau zazzaga masifa kan bai isa daga zuwansa ya hanata abinda takeyi ba har da cewa Ubansa ma yayi kadan bashi ba, shi dai sulaiman baice mata komai saboda yasan halin jarabar ta bayan ya ci abinci ne sai da ya tabbatar Sayyadar ta tafi isilamiyya sannan ya fita daga gidan kai tsaye gona ya nufa inda Kawu Tanko yake....! Sosai ya nuna masa 'bacin ransa kan ya akayi suka sake har Baba ke fita cikin kasuwa tana sare sare sai kace wacce ta rasa ci da sha sannan babban abin damuwar yanda take dorawa Sayyada tallah wannan ai zubar da mutumnci ne, Kawu Tanko yace"Shima ba a son ransa hakan take faruwa ba Baba dai mahaifiyar sa ce dole yayi mata biyayya amma yana ganin wannan karon dole yayi ta maza tunda dai abin nata na kokarin wuce gona da iri sannan maganar tallan da take d'orawa Sayyada kuwa zai sanar da ita cewar zai je ya shaidawa iyayenta tunda dai su basu suke da iko da ita ba yasan can gidan maigarin basu san abinda ke faruwa da tuni sun dauki mataki kan al'amarin domin kankaro da martabarsu tabbas ya fada mata haka yasan zata daina dora mata tallah tinda itama bata so mutuncin ta ya zube a gurin mutane.
Sulaiman yace"Wannan hukuncin da ka yanke shine ya dace tuntuni a dauka a kanta.....Sai daf da magariba suka nufo gida a tare abin mamaki suna dosowa layin suka hango Sayyada gindin darbejiya tana sai da mangwaro Talle na zaune a gefanta sai hira suke...Kawu Tanko yace."Ka gani ko Sulaiman duba ka gani." Sulaiman ya kalli inda yake nuna masa hankalinsa ya tashi ainun kai tsaye gurin ya nufa ransa a 'bace!
Talle na ganin ingarmar namiji ya doso gurin sai yayi sauri ya mike duk a tunaninsa ko Sadam! ne domin bai manta da marin da yayi masa a watannin baya sai da Sulaiman ya karaso gurin sannan ya gane bashi bane domin shi wancan yafi wannan fad'i da murd'ewar jiki sannan bai kai hasken wannan ba amma dai duk da haka dole ya kiyaye domin ya lura shima wannan d'in babu sauk'i a fuskarsa.Gurin yayi saurin bari Sayyada na kwala masa kira yazo ya 'karbi sanjinsa yace."Ki rike na bar miki." Tace"To nagode." Sulaiman yace"Sayyada ashe kema baki da kamun kai ashe baki san ciwon kanki ba Sayyada! bayan fitata ashe dai sai da kika d'auko tallan mangwaro kika fito bakin bishiya shin wai me kuke nema ne ke da Baba Ladidi? babu rashin ci babu rashin sha babu rashin suttura kuke nema ku zubar mana da mutunci a gari dai dai gwargwado muna sauke hakkinku banji dadin abinda kikeyi ba shin wannan saurayin da yake zaune a kusa dake meye matsayinsa a gurinki.'!? Tana kuka tace"Saurayina ne Talle." Sai yaji gabansa ya fad'i! Yace."Saurayin ki ne Talle ."!? Daga kai tayi girgixa kansa yayi yace."Dauko kayan muje gida." Ta sunkuya ta dauki farantin mangwaron suka nufi gida Sulaiman takaici na cin zuciyarsa dole tilas kafin ya bar garinan ayi wacce za'ayi Dole ne Sadam! yayi wani abu akan lamarin nan sam! shirun da yayi bashi da wani amfani kawai ya fad'i abinda yake ransa shin yana son yarinyar nan ko baya so idan baya so to babu shakka shi kam kafin ya koma bakin aiki sai ya tabbatar da cewar an d'aura masa aure da ita ya tafi da matarsa inda yake da wannan tunanin suka isa gidan
Kawu Tanko na tsugune gabanta yana magana 'kasa-'kasa da son ya fahintar da ita cewar abinda takeyi ba dai-dai bane ita kuma sai furjewa takeyi tana kawo 'kauli da ba'adi! Sulaiman najin tababar da suke yace."To shikkenan tinda kin'ki fahinta mu zamu shigar da 'korafin mu gaban maigari in yaso sai ki fad'a musu dalilin da ya sanya kike d'orawa 'yarsu tallah."! Ai sai ta fashe da kuka tana fad'in Sulaiman bashi da kunya yana kokarin zaginta ya fad'a mata magana in dai kan Sayyada suke wannan maganar to ta zare hannunta daga kanta.
Sulaiman yace."Shikkenan kin gama magana tace"Ban gama magana ba ai tunda kunce Sayyada ba zata yi min tallah ba to sai ku sanar da wancan miskilin mai kafirar kafiyar tsiya ya fito a daura auran in daina ganinta a gabana idan kuma ya'ki to wallahi nima ba zan daina d'ora mata tallah ba."