Sashe 24
Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kuka takeyi sosai! har sai da ta bashi tausayi yaja hannunta suka fita motarsa ya nufa da ita ya bude suka shiga"Goge hawayen ki."Ya fada tare da mika mata hankici mai kamshi
Bayan ta goge sai ya mika hannu ta bashi makale kafad'ata tayi yace."Saboda me."? "Saboda ina son 'kamshinka Don Allah Yaya Sadam! kar kaje gurin nan kaji ina sonka bana so wani abu ya sameka."!
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace." Kin gane ko Sayyada shi wannan aikin namu daban yake da sauran, muna taimako da tsare rayuka da dukiyoyin talakawa ne kuma kafin mu kar'bi aikin sai da mukayi rantsuwa da al'kawari kan cewar komai wuya rana zafi ruwa sanyi zamu fito a duk lokacin da wata tarzoma ta tashi zamu taimaka koda zamu rasa ranmu saboda haka ki kwantar da hankalinki babu abunda zai sameni sai alkairi."
Hawaye take tace"To Ina rokon Allah ya tsareka kuma ya baka nasara mijina." Murmushi yayi irin wanda bai ta'ba yi mata irinsa ba ya "karbi hankicin ya goge mata hawaye kana ya mika mata ta kar'ba tana murmushi.....Shina murmushin yake yana kallon fuskarta.
Hannu yasa ya d'ago fuskarta a hankali yace." Bani nasha."! ta lumshe idonta tare da budewa sai taga fuskarsa daf da tata, rintse ido tayi gabanta na fad'uwa.....Murmushi ya saki ya sakar mata fuskar ba tare da yayi mata komai ba yace."Kije gida kiyi min addua amaryata."
Ta bude kasalallun idanunta tana kallonsa hannu ya zura ya bude mata kofar motar ta fito ya daga mata hannu kana yaja motar mai gadi ya bude gate ta figi motar a guje ya fice!!! ta jima a tsaye a gurin tana kallon hanyar da ya wuce jiki a mace ta koma bangaransu ta kwanta inda ya kwanta jiya ta dauki jallabiyarsa da ya cire ta rungume a kirjinta tana hawaye. haka bacci ya dauketa.
Sulaiman kuwa ganin Sayyada bata dawo ba sai yaji duk xaman gurin ya isheshi tashi yayi zai fita aunty Luba tace"Darling yaushe xamu koma gida ne.? ba tare da ya juyo ba yace."Duk sanda kika shirya komawa." Ta mike da kyar tana fadin "Yanzu ma a shirye nake." Tsaki yaja ya fita sai ta bishi da kallo cike da mamaki! auran soyayya sukayi da juna amma tunda ta samu ciki ta rasa gane kansa da gidinsa wulakancin yau daban na gobe daban, kwata-kwata bashi da lokacinta sai aukin hira da 'yan mata a waya.
Ta wagar sojojin na shiga cikin kasuwar jama'a suka soma watse masu sana'a da suka karkasa kayansu suka soma kwashewa Sadam! ya kar'bi abin 'kara karfin murya yace."Kowa ya zauna ya nutse kuma ku daina kwashe kayan sana'ar ku bunkice muka shigo zamu tafi idan mun gama mu barku ku cigaba da sana'oinku.'' To sai da sukaji wannan magana sannan hankalinsu ya kwanta....Su kuma sojojin sai suka watsu dana already wasu sun rufe gate din gaba da baya kuma tsun tsare hanya......Sadam! ya dinga kutsawa cikin rumfunan jama'a ya duddubawa su kuma sauran suna zazzage buhunhuna! na kayayyakin sana'a duk wasu daurarrun kayan sai da suka kwance suna dubawa babu wata alamar ganin mutum......duk fad'in kasuwar sai da suka bunkita basu ganshi ba....Sadam! ya ri'ke 'kugu yana kallon tarin jama'ar da sukayi tsuru-tsuru suna jimami d'an boko haram! ya shigo cikinsu basu sani ba wasu daga cikin ma har sunyi alkawarin cewa daga yau ba zasu sake fitowa kasuwa ba har sau gwamnati ta shiga al'amarin......Dai-dai inda yake tsaye karkashin wata katuwar kwata ce da aka rufe ta da silaf kwatar tun daga farkon kasuwar take har karshenta kuma duk rufe take da Silaf.....Babu zato! Sadam!! yayi 'yar hantsle!!! Ya ganganra can! gefe kafin kice kwabo guri ya hautsine da hayaniya kowa naso ya tsira da ransa......Cikin zafin nama ya mi'ke.....da gudu! ya nufi gurin kafin ya 'karasa an jefo wani abu!!! jama'a na dubawa suka ga bomb!!!!! Sai ihu! gudu karce! marasa karfi sai faduwa sukeyi ana tattake su kowa dai na neman ya ceci ransa.......Ba tare da wani tunani ba ya afka cikin kwatar, Can ya hango shi yana gudu!!! cikin kwatar bakajin komai sai motsin ruwa!!!! Sa'ilin da gurin ya hargitse ne aka samu wani wanda yayi saurin mayar da silaf d'in da wannan d'an boko haram d'in ya cire ya rufe gurin alhalin yasan Sadam! na ciki......Jama'a sunyu dafifi bakin gate suna ihu! ga gate a kulle marasa hakuri kuwa ai har sun soma haura katanga suna dura 'kasa, Captain Habu ne yazo cijn zafin nama ya bude gate din aikuwa jama'a suka dinga turareniyar fita......Captain Aminu shine yayi jihadi ya d'auki bomb din a guje ya fita dashi can cikin bishiyo ya jefa shi ya bar gurin da saurin gaske.........!
Sadam! harbi kawai yake saki! ta ko ina! cikin ikon Allah yayi nasarar samunsa a kafarsa...aikuwa a take ya zube a gurin.....! yana rike kafa Sadam! ya 'karasa inda yake cicci'barsa yayi ya sa'ba a kafad'a ya dawo baya sai da yazo yaga babu hanya ko ina a rufe......Ya cika da mamaki a jiye mutumin yayi ya fara kokarin ture silaf d'in domin ya samu hanyar fita inda anan mutumin ya samu nasarar zare bindigar dake jikin wandonsa ya saita kafad'arsa ya sakar masa bulet!!!!!! Ya juyo a fusace! ya dauke shi da mari! faduwa yayi cikin kwatar ya sanya takalminsa ya take masa wuya yana cije baki!! hannu daya ya ture silaf din kana ya sunkuya ya d'auko shi jikinsa jage-jage! da jini ya fito.......Gurin tsit!!! Can Captain Habu ya hangoshi ya fad'i ga jini a jikinsa a guje ya 'karaso gurin yana kiransa idanunsa yaga suna lumshewa jiri ne kawai yake d'ibanshi hannunsa ya rike yana goge masa zufa.....Da bayan bayan daya sojojin suka dawo nan sukaga halin da Sadam din ke ciki gashi dai an samu nasarar kama mutumin amma kuma wanda suke alfahari dashi yana cikin matsanancin hali.
11/6/2020
*BINTA UMAR ABBALE*
_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga duk mai bukatar karantawa sai ya tura kudinsa ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank idan kuma katin waya mutun zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din zan fad'a masa yanda zai biya kud'in....08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar littafin to sai ku tura dala dari ta wannan numbars.....90899076 _88137740 katin airtal ko orange.....Dala dari itace a madadin dari uku na najeria.*_
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*
_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________
_*Na kusa gama free pegea duk me bukata sai ya turo kudin karatu*_
*Free Pege18*
Da sauri Captain Habu ya bar gurin, Captain Saleh yazo yazo ya tsaya kawai a kansa yana masa wani irin kallo yaso ace ha'kansa ya cimma ruwa yaso ace bukatarsa ta biya a kansa amma babu komai watarana ya tabbatar da cewar bukatarsa sai ta biya a kansa ya dauki alwashin sai ya salwantar da ransa mutukar suna aiki a guri guda.
Mota Captain Habu ya shigo da ita da sauri Captain Saleh ya sunkuya domin taimaka masa sai ya d'aga masa hannu goshinsa duk ya tsatstsafo da gumi hannunsa a kafadarsa ya rike gurin harbin jini kam duk ya jika masa jiki.....Captain Saleh ya matsa gefe guda yana kallo Captain Habu ya rirrikeshi ya kaishi mota, sannan suka tasa 'keyar d'an boko haram! din wanda suka rufe masa fuska da wani ba'kin abu suka daure duk hannayensa da ankwa....Gurin cika yayi da mutane 'yan jarida har sun hallara a gurin mutane sai dauka suke a wayoyinsu da kyar motar ta fita daga gurin.....Cikin brecck din akwai asibiti dake kula da sojoji da iyalinsu kai tsaye can aka nufa da Sadam! wanda tsabar dauriya tasa idanunsa ya kada yayi jawur jijiyar kansa duk ta tashi kana kallonsa a lokacin zaka fahimci yana jin jiki sosai....Lokaci guda likitoci suka rufu a kansa har sai da suka samu nasarar cire bulet! din sukayi aikin gurin yanda ya kamata kana sukayi masa allurar bacci domin ya samu hutu.