← Book details Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 30

Sashe 29

Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonsa tayi taga yaci kunu tasan halin rashin mutumcinsa idan abun ya motsa masa duk da bashi da lafiya zai iya dukanta.....Tace"Idan ni 'yar halak ce daga yau na rabu da kai." tasa kai ta fice daga d'akin....Kafad'a ya d'aga alamun abun bai dameshi ba ya isa bakin kofar ya tsaya yana kallon dambarwar dake faruwa tsakanin Sayyada dasu Mu'azu.......Ana budewa Halima gate Sayyada tayi waje da gudu Halima ta fice da motarta. Yaga lokacin da ta fita daga bracck din sai ya koma dakin a gaggauce ya kira lamar Habu. Yana dagawa yace."Habu duk abinda kake ka aje yanzu yanzu yarinyar nan ta fita ban san ina ta nufa ba." Captain Habu yace."Wace yarinyar wai."! Cikin kufula yace."Sayyada fa nake nufi."!! Habu ya kashe waya hankali tashi ya fito daga ofis gate aka bude masa ya fita can ya hangota tana tafiya gefab titi ya bi bayanta da sauri Sayyada najin sahun mutum a bayanta ta waiwaya sai taga Habu ne ranta ya 'baci itafa ba xata koma ba ta riga tayi alkawari....To da yake tafiyar ba daya bace Captain Habu ya iske gabanta ya tare yace"Sayyada ina zakije yanzu wa kika sani ? kika fito kan titi kina tafiya."! Ta share hawayen dake zubo mata tace"Zan koma *Dabi* ne." Akan wane dalili Sayyada me yayi xafi."!? Sai ta fashe da kuka ta tsuguna a gurin.....Tausayi ta bashi ya dinga rarrashinta sai da yaga tayi shiru sannan yace."Sadam! ne yayi miki laifi ko."? Daga kai tayi yace."Kiyi hakuri da abokina yana da zafi ne amma kuma mutum ya iya zama dashi mutum ne mai saukin hali ki taso mu koma yanzu haka shine ya turo in daukeki."

Tace"YaYa Habu ni bazan koma ba tun jiya yake min masifa motsi kadan fad'a da kyara da hantara me nayi masa kawai don yaga ina sonsa shine fa ya koroni daga dakin saboda budurwarsa.

Cike da mamaki! yace.''Budurwarsa kamar yaya." ? tace"Wata Halima ce tazo shine ta zageni shima yace na fita." Captain Habu ya girgiza kai yasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya Halima tazo kenan to Allah ya rufa asiri....."Kiyi hakuri Sayyada zan nuna masa kuskuransa har yaushe ne xaka fifita budurwa kan matarka ta sinna kiyi hakuri kinji ko ki zama jarumar mace mai juriya kan komai."

Captain Habu yana da mutuncinta a idonta shine dalilin da yasa kawai ta hakura ta bishi suka koma cikin barikin sojojin.

Yana hango zuwansu ya koma cikin dakin hankalinsa ya kwanta shi kanshi ya rasa gane meke damunsa kan yarinyar yana kishinta mutuka haushin abinda tayi masa kan Sulaiman ne yasa ya koreta......Sai da suka hau sama suka fad'o da Habu sannan suka rabu Captain Habu ya nuna masa abinda yake bai dace ba ko babu aure a tsakaninsa da Sayyada kanwarsa ce bai kamata ya fifita wata akan ta ba, da yaga Habun ya dauki zafi sai ya shareshi ya nemi guri ya kwanta har da lumshe ido....Captain Habu ya kalli Sayyada yace"Idan yayi miki wani abu da bai gamsheki ba to ki sanar dani ai shima yana da na gaba dashi kuma a dokar aikinmu bamu yarda da cuzgunawa matanmu ba." Jin abinda Habu din yake fada mata yasa ya bude ido yana harararsa yace."Zaka zugata ne tayi min rashin kunya dama ba ganin mutuncina takeyi ba."! Habu yace."Ni ba zugata nake ba ina koya mata daburu ne da yanda zata kwaci kanta a hannunka saboda na lura kai din ka fiye son kanka da yawa." Miskilin murmushi yayi ya mayar da ido ya rufe....Captain Habu yace."Me kike so na siyo miki in anjima." Tace."Babu komai."! yace."ki bari zan siyo miki shawarma! kici abinki karki bashi." murmushi tayi tana mamakin karamci da kyautayi irin na Habu.

Bayan Captain Habu ya fita sai dakin yayi shuru Sayyada tayi kici kici da fuska taki kallon inda yake kwance tayi alkawarin ai ta daina rawar jiki a kansa ballanta har ya samu damar wulakantata.

Bude munafukan idanunsa yayi yana kallonta amma sai ka rantse da Allah cewar ba ita yake kallo ba......Yanzu tausayi take bashi sosai gyaran murya yayi wai ko zata juyo ta kalleshi yaga ko da wasa bata juyo ba ya cika da mamaki kwarai! sai ya fara d'an tari! a hankali a hankali to wannan karon ta d'an juyo amma babu walwala a fuskarta da dane da tuni taje inda yake tana rawar jiki sai yaga motsi ba tayi ba a inda take........dauke ma kanta tayi ta dora kafafunta duka kan kujera ta juya masa baya.

"Ke!!!." Ya ambata tasan da ita yake sai ta shareshi "Ko bakya ji ne."!? Sayyada ta ci kunu ta'ki amsawa ballanta ta kalleshi idan ya gaji ya kira sunanta.

" Sayyada." Ya ambaci sunanta cikin kasalalliyar murya...Kallonsa tayi tana zum'bura baki! "Kina ji ina magana kinyi banza ko."? " To ai ba sunana "Ke! ba." "Okey naji ina maganina."? " Nima ban san inda yake ba." Tafada tare da dauke kanta........! shiru yayi mata ya koma ya kwanta dama dan dai yayi mata magana ne yasan ba lokacin shan magani bane.

Dake dakin da tv sai ta kuna kallo ta rage vollom Wani indian film take kallo hankalinta ya dauke kan film din ana soyayya Sharukan da Saif Ali khan sai preetyzeenta filim din na soyayya ne sosai ya burgeta ita dai a cikin ranta tafi son yarinyar ta auri Sharukan a ganinta sunfi dacewa.....Sadam! na ganin yanda ta mai da hankalinta kan film din cikin zuciyarsa yace."Yarinyar "yar soyayya ce.....Ganin magariba ta gabato yasa yace." Ki kashe tv haka kije kiyi sallah malama kin kurawa tv ido 'yar kauyen *Dabi."* bata ce masa komai ba ta kashe tv ta nufi bandakin dake dakin alwala tayi ta fito ta tada sallah....Cikin dubara ya mike ya nufi bandakin domin daura alwala.

Sai bayan Sallah isha'i sannan Hajiya Fatsima ta iso ita da Baban gida suka gaisa sosai Tana tambayar jikinsa Sayyada tace"Alhamdullahi Tace"Ga kaya na d'ebo miki tunda zaman asibiti ya kamaki Abbanku yace."Ki zauna kiyi jinyar mijinki." Rufe fuska tayi tana dariya....Yace."Mammah wannan yarinyar babu abinda ta iya komai ni nakeyi da kaina ni da cewa nayi ma idan kinzo sai ku koma gida tare."

Hjy Fatsima tace"Da idona fa naga yanda yarinyar nan take taraiyayarka haba Sadam! Sayyada na iya kokarinta a kanka." Yace." Mammah ba zaki gane abinda nake nufi amma babu komai ta zauna d'in......"Mamah zan biki mu koma gida." Tafada kanta a 'kasa Cikin mamaki tace"Saboda me zaki bar mijinki ki koma gida Sayyada." Tace"shine baya son zamana a gurin." Hajiya Fatsima tace"To in banda abinki Sayyada ba gashi kinji da kunnanki muna magana dashi ba ya amince ki zauna." Sayyada tayi shiru tabbas da zata iya fitowa mata a mutum da ta fayyace mata irin cin kashin da Sadam! yayi mata tsakanin jiya da yau amma babu komai zata zauna kamar yanda ta bukata.

Sulaaim da Alhaji Auwal ne suka shigo tare duk bakin gadon da yake kwance suka nufa suna dubashi Sulaiman ya saki fuska sosai kamar ba dazu suka gama fad'a ba shi kuwa gogan naku da yake bai iya 'boye fushinsa ba ai ko kallo Sulaiman bai ishe shi ba.

Sai kusan karfe tara na dare suka tafi bayan tafiyarsu da minti biyar dr ya shigo domin dubashi Yace."Yallabai yana da kyau kaci abinci kasha magani ka kwanta ka huta gurin mikin nan har yanzu baiyi mana yanda muke so ba kana yawan motsa gurin." Yace."Kar kadamu Dr zan kwanta yanzu."

Dr Ya kalli Sayyada yace."Madam a bashi abinci yaci yasha magani ya kwanta." Tace."Insha Allahu." Dr na fita tayi kwanciyar ta kan doguwar kujera, Sai ta rama abinda yayi mata kuma zai gane tana da rana ko bata da rana a gurinsa.

"Ke." ya ambata a hankali Sayyada na jinsa tayi banza dashi...."Ke! ya sake fad'a shiru tayi yace."Ko bakya jin abinda dr yace ne? ki bani abinci da magani na kwanta." Zumbura baki tayi ba tare da ta juyo ba tace"Ai kai d'in ba yaro bane kana iya had'a abincin da kanka kasha maganinka tunda dai ciwon bai hanaka kokawa ba ai ba zai hanaka ka zuba abinci ba."

Rai a 'bace! yace."Ni kike fad'awa wannan maganar."!? Shiru tayi masa....Ya jima yana mamakinta tabbas yayi sake da yarinyar ta raina shi Kwanciya yayi bai ci abincin ba kuma bai sha maganin ba Sayyada ta kunna shi babu abunda yake so sai ha'kin taba.

Wayarsa tayi ringing sau kusan bakwai bai duba ba ballanta ma yaga me kiran, kamar Sayyada ta dinga fada masa maganar da duk tazo bakinta.

Ita kuma jikinta ne yayi sanyi ganin ya kwanta bai sha maganin ba sai ta mike tana mutsika ido addau take Allah yasa Captain Habu ya shigi aikuwa Allah ya amsa adduarta shine ya shigo hannunsa rike da ledoji

Captain Habu ya shigo dakin tare da fad'in"Ashe bakiyi bacci ba."Tace"Ina jira ka kawo min shawarma ta." Dariya yasa yace."Sayyada bakinki na son cin dadi ne ko." Tana murmushi tace"To waye baya son dadi." yace."To gashi a ciki lafiya." ledojin ya mika mata ta kar'ba tana godiya shi kuma isa bakin gadon Sadam! "Aboki ya jikin ."!? Alhamdullahi ya fad'a a cunkushe Habu ya samu kujera ya zauna yana masa hirarar abunda ke faruwa Kano suma 'yan boko haram! d'in sun addabesu labari ya samesu cewar an kama wani a cikin Unguwar Ja'in ya shiga a dai-dai ta sahu da bomb a jikinsa.

Sayyada tace" Wallahi Yaya Habu ina tsoron mutanan nan Allah yasa kar su shiga Garinmu." Habu yace."Insha Allahu Allah xai kawo mana karshen matsalar nan, za muyi maganinsu da yardar Allah."

Hira suka cigaba da yi tsakanin Sadam da Habu akwai shakuwa da yarda da juna shiyasa duk wani abu da ya danganci Sadam! din Habu yake shiga ciki yayi kane kane Yace."Dazu kafin in shigo Halima ta kirani ta sanar dani abunda ya faru da kai da ita kaga irin abinda nake guje maka ko.......Sadam! yace." Don Allah ka rabu dani da zancan wata Halima itake wahalar da kanta saboda tsabar bata da hankali wai magana takeyi min yaushe zan aureta."

Habu yace."Shiyasa naso ka fad'a mata tun tafiya ba tayi nisa ba yanzu sai da ka bari ta sakankance zaka aureta sai kace wani abu hakan bai dace ba"
Chapter 29 · 0% Book details