← Book details Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 30

Sashe 8

Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga duk mai bukatar karantawa sai ya tura kudinsa ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank idan kuma katin waya mutun zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din zan fad'a masa yanda zai biya kud'in....08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar littafin to sai ku tura dala dari ta wannan numbars.....90899076 _88137740 katin airtal ko orange.....Dala dari itace a madadin dari uku na najeria.*_
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________

Free pege 8

*Asalinsu*
Jauro mai shanu shine mahaifin Alhaji Inuwa da Kawu Tanko sai baba Indo wacce Allah yayi wa rasuwa shekaru goma da suka wuce lokacin Sayyada nada shekaru hudu a duniya yanzu in an hada duk tana da shekaru goma sha hudu a duniya.

Malam Jauro mai shanu yana da mata biyu Baba Ladidi da Baba Marka wanda rana d'aya aka d'aura masa auransu suka tare a rana daya....Shekara nayi Baba Ladidi ta haihu inda ta haifi da namiji aka sanya masa sunu Auwalu sai da Auwalu ya shekara bakwai sannan baba marka ta haihu itama namiji ta haifa Aka sanya masa suna Haruna dake sunan mahaifin Malam Jauro ne sai suke ce masa Tanko.....Bayan shekaru uku Baba Ladidi ta haifi mace Aka sanya mata Aisha suke kiranta da Indo Tsakanin Marka da Ladidi suna zaman lafiya sosai da sosai ta inda yaransu basa gane cewar wacece mahaifiyarsu a ciki zaman lafiya da kwanciyar hankali suke inda har jama'ar garin suke sha'awarsu suke kuma kwatance dasu.

Dai-dai gwargwado Auwalu da Tanko sun samu ilimin addini dana boko sai suka soma har kokin noma da kiwon shanu da sauransu dake Auwalu mutum ne mai kuzari da zafin nama sai ya yanke shawarar fita daga garin nasu neman shekarar da sukayi aikin shinkafa ya cika mota guda ta a kori kura ya nufu kasuwar kano kasuwar (dawanau) ya sauka jama'a suka rufe shi kafin kice kwabo shinkafar da ya sauka da ita ta kare kimanin buhu talatin 'yan sari duk sun siye a take ya had'o kan kudinsa ya nufo gida suka sake aikin wata shinkafar ya sake dauka ya nufi garin kaduna anan ma dai shinkafar ba tayi wani tasiri ba suka siye tas....Kafin kice kwabo likkafa ta cigaba harkoki suka budewa Auwalu ya dinga bin gari gari yana sauke musu shinkafa mai kyau suna siya.......Cikin garin kaduna ya hadu da matarsa wacce ta kasance itace uwar 'yayansa Fatsima sunanta, ko da ya sanar da iyayensa cewar ya samu matar amma ba 'yar dangi ba bace can garin Kaduna take sai suka nuna amincewarsu sukayi masa fatan alkairi ba'aja wani dogon lokaci ba aka daura aure tare da amincewar su.

Allah ya albarkaci auran kawarai da gaske Arziki da wadata suka sake suke 'karuwa shekara na zuwa duk ya biya musu kudi sukaje suka sauke farali Dashi da Mahaifinsa Jauro da kuma baba ladidi da baba marka da Indo sai da dan uwansa Tanko da matarsa, addua ta ko wane fanni Alhaji Auwal ya samu ya gina gida mai kyau da kayatuwa sannan ya dawo garinsa na gado *Dabi* ya gyara musu dai-dai gwargwado ya zube musu abubuwan more rayuwa.....Tanko shike kula da harkokinsu na noma na garin.....Shekara daya da zuwansu aikin hajji Hjy Fatsima ta haihu inda ta haifi d'a Namiji aka sanya masa suna Sulaiman.....Malam Jauro da iyalinsa suka zo suka ga jinjiri suka sanya masa albarka.

****

Auran Kawu Tanko da Baba Indo a rana daya aka daurashi Kawu Tanko auran zumunci yayi inda ya auri 'yar gidan Dantani wanda ya kasance 'kani na jini da Malam Jauro Baba Iya itace matar Kawu Tanko asalin sunanta Hamara'u

Baba Indo kuma ta auri d'an gidan Maigarin garin *Dabi* mai suna Qasimu, ta zauna a cikin gidan mai gari dake gidan mai girma ne sosai bangare guda aka ware mata a cikin gidan.

***

Sulaiman nada shekaru hudu Hjy Fatsima ta sake haihuwa inda ta sake haihuwar Da namiji lokacin ne aka rigima tsakanin turawa da salihin mutumin nan da ya baiwa addinin musulunci guduma wato *Sadam! Hussain* a ranar da aka haifeshi aranar aka kashe Sadam! don haka sati na zagayowa Alhaji Auwal ya sanya masa suna Sadam! Saboda duk wani musulimi a wancan lokacin yaji ciwon abinda kafirai suka aikata kan mutumin nan duk mai kishin musulunci dole sai ya jajanta al'amarin.

*******

Sadam! tunda ya taso yake da wani irin hali mutum ne mai gudun zuciya da tsantseni yana da tsafta sosai kuma miskili ne sam baya son wasa idan kagan shi tare da d'an uwansa sai ka dauka shine babba saboda Allah yayi masa kwarjini da haiba dukanin family dinsu babu ba'ki sai shi dukaninsu farare ne kyawawa daga mazan har matan hanci har baka ga uban gashi shi kadai ne 'baki a cikinsu amma kuma a zahirance yafi su kyau sai wanda ya zauna dashi zai fahimci hakan kyakykyawa ne mutuka yana da manya idanu wanda suka dan risina kadan kewayayyiyar fuskar ta kawatu da wani saje mai kyau da tsari kasan ha'bar sa da saman bakinsa yana yawan yin gyaran fuska saman goshinsa akwai wani abu da yayi duhu tabon sallah kenan Sadam! yana da ibadah da kula da addini tun yana dan shekara goma sha hudu ya sauke al'kur'ani mai girma kwataa-kwata ba tsarinsu d'aya da yayansa Sulaiman ba wanda shi ya kasance mutum mai a'kidun turawa kaf karatunsa akasar waje yayi yanzu haka yana aiki 'karkashin hukumar tsare birni da kewaye na jahar Kaduna Sulaiman yana ta'ba siyasa sa'i da lokaci don har takarar dan majalisa ya tsaya Allah bai bashi ba.

***
Sadam! kam tunda ya kawo 'karfi yaji yana sha"awar aikin soja don haka kawai sai ya sanja shawara ya shiga makarantar horar da sojoji dake Kaduna ba, General Abdul Salamu shine ya tsaya kai da fata kan Al'amarin Sadam! a cewar sa a wannan zamanin idan Najeria ta samu jajurtaccen mutum irin Sadam! zata samu cigaba irin wanda ake bukata.

To tun Alhaji Auwal da Hjy Fatsima basa son abun suka dawo suna so domin General Abdu salam da kansa yazo ya sake wayar musu da kai kan yanda al'amarin suke sai suma daga baya suka gane abinda yake nufi.

A da Sadam! yana karantar aikin likita ne wato bangaran mata to sauyawar ra'ayi yasa ya aje karatun likitanci ya shiga aikin soja gadan! gadan! A yanzu Sadam! nada mu'kamin Captain a brecck din nasu kuma suna masifar ji dashi saboda babu wani abu da zai tun karo su na tashin hankali bai magance musu ba,

****

*Waiwaye adon tafiya*

Wannan magana da Baba Ladidi da Baba Marka suke ta samo asali ne daga gurin marigayiya Baba Indo wato mahaifiyar sayyada kenan Baba Indo in dai baku manta ba 'yace ga Baba Ladidi ta kasance 'kanwar Alhaji Auwal da Kuma Kawu Tanko....To a tun lokacin da aka kaita dakin mijinta ta had'u da lalura wani ciwo ya fito mata a kafarta guda inda ya dinga cin jikinta a lokacin har ta haifi Sayyada tayi wayo kusan shekararta hudu a duniya saboda yanayin jinyar da Indo take ne yasa Baba Ladi ta dauketa ta koma gurinta da zama. To duk a wannan lokacin Ciwon ajali ya kwantar da Malam Jauro inda baiyi wata doguwar jinya ba Allah ya amshi ransa......Wata uku a tsakani Baba Indo ta bishi a ranar da zata rasu a ranar Sadam! yazo garin hutu.....Lokacin Sayyada tayi bud'ud'u da jar 'kasa hancinta dagaje! dagaje! da majina gashi lokacin kunnenta babu yari ga aski baba ladidi tayi mata saboda kuraje da suka dame ta Sayyada dai kwandala ba zaka siye ta ba, aikuwa rankwashinta yayi ta yayi mata tsawa! ya korata gida tana ihu! ta shiga gidan bayan baba ladi ta boya tana nuna shi shi kuma sai hararata yake....Baba Ladidi tace"Daga zuwanka zaka dinga dukanta wannan ai cin zaline da mugunta.

Yana ya mutsa fuska yace."Baba wannan yarinyar sadaka aka bawa mutum ba zai kar'ba ba yarinya kamar ba mutum ba dubi jikinta ka'zama babu kyan gani."

Tace."Ai wasa take kuma yanzu dama nake cewa bari nazo nayi mata wanka."

Yace."Babu wani kawai don nayi magana ne amma da banzo ba haka zata kwana." Mikewa yayi yace."Zanje na duba Baba Indo kafin na dawo kiyi mata wanka." Cikin jin haushi Baba Tace"Ba zanyi ba d'in! kai kaji yaro da iyayi da kaine kake sani nayi mata wankan? sai dai idan ka dawo kayi mata ehee."!

Fita yayi bai ce mata komai ba....Halin da ya iske Baba Indo a lokacin da ya isa gidan ya bashi tsoro

Matan gidan sun kewaye ta suna mata fifita masu kuka nayi da salati baba indo kuwa bata san inda kanta yake ba sai nishi takeyi kamar ance ta bude ido sai ta ganshi a tsaye a kanta ta mika masa hannu matan gidan duk suka cika da mamaki hannunsa ta rike da kyau tana so tayi magana bakinta yayi mata nauyi da kyar tace"A kawo min Sayyada." Matar kanin mijinta ta fita daga dakin da sauri ta sanya yaro ya nufi can gidan ya fada musu halin da ake ciki......Minti ashirin ya kawo su Baba Marka ta fashe da kuka ganin halin da Indo ke ciki Ita kuwa Sayyada kin zuwa gurin mahaifiyar tata tayi ta 'buya a bayan Baba Ladi dake kukan zucci tana addua Allah ya saukakawa indo wannan larurar
Chapter 8 · 0% Book details