← Book details Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 30

Sashe 7

Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ransa ya 'baci wato don taga yana lalla'ba ta shine zata kawo masa raini sai ya murtuke fuska yace."Wallahi zan mareki kika kara wata magana anan gurin wuce ki shiga gida."

'Kin shiga tayi sai ma ta dinga matsawa jikin Talle tana tauna gyalanta sai kace yarinya karama.....A fusace! ya jawo ta zai gaura mata mari Talle yayi caraf! ya ri'ke hannunsa "Kai kar ka kuskura ka dok......... Kafin ya 'karasa yaji wani irin azabar rad'ad'i! a hannunsa Sadam! ya murd'e masa 'yan yatsu har sai da suka bada sautin 'kas!'kas!!!! Ihu!!! yayi a take idanunsa sukayi jawur! saboda azabah! fitsari ne kawai Talle bai saki ba.....Sadam! na sakar masa hannu ya kama hanya ya fice da sauri ko waigowa baiyi ba.

Sayyada na ganin ya juyo kanta...Sai ta shige cikin gidan da sauri tasan halin sa sai ya mareta gashi marinsa zafi ne dashi takan kwana biyu tana jinyar fuskarta.

28/5/2020

*BINTA UMAR ABBALE*

_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga duk mai bukatar karantawa sai ya tura kudinsa ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank idan kuma katin waya mutun zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din zan fad'a masa yanda zai biya kud'in....08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar littafin to sai ku tura dala dari ta wannan numbars.....90899076 _88137740 katin airtal ko orange.....Dala dari itace a madadin dari uku na najeria.*_
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________

Free pege7

Ko lokacin da Sayyada ta shiga ciki Baba Ladidi da Baba Marka duk sunyi bacci a tsakar gida da yake lokacin zafi ne nan suke kwanciya sai asubah suke komawa d'akunansu, kai tsaye daki ta shiga domin dauko bargon da take kwanciya taji masifar dadi da Sadam! ya ga Talle suna zance yasan itama ba samari ta rasa.

Tana fitowa daga dakin suka ci karo dashi ya shigo sai tayi saurin komawa da baya gabanta na faduwa ta dauka ai yayi tafiyarsa.

Cikin uwar dakin ta shiga ya bita sai ta soma ta'be fuska zatayi kuka ya daka mata wata iriyar tsawa! shiru tayi tana kallonsa.

"Wallahi duk sanda na kara ganinki a tsaye da wannan 'kazamin sai ranki ya 'baci ke ki rasa wanda zaki tsaya dashi sai wannan shashashan mai warin d'auda."!

" To ina ruwanka dashi ni shi naga ni kuma shi nake so."!

Mari ya kai mata ta kauce! da sauri ta tsorata da ganin yanayinsa.

Yace."Saboda baki da kunya ina miki magana kina mayar min kin raina ni ko."!?
Da karfi ya fadi maganar.

Shiru tayi yace."To ki kuskura na gani ko naji labarin kin sake tsayawa dashi wallahi sai na dauki mataki mai tsauri a kanki zan sanya matakan tsaro sosai a kanki."

Tana kuka tace"Wai kai ina ruwanka ne? kaine fa kace ba zaka aure ni ba sai kuma ka hanani kula Samarina ai ba zai yiwu b......Ya kaiwa bakinta duka da sauri ta rufe da hannunta ya daki hannun ta sake fashewa da kuka mai karfi wanda yayi sanadiyar tashin Baba Ladi daga bacci....."Ke! Sayyada menene kina ina ne."!? baba ladidi ke wannan maganar tana haska karamar toch inda sayyada ke kwanciya sai taga gurin wayam! tana kokarin mikewa Sayyadar ta fito daga d'akin a guje bayanta ta 'buya tana kuka Ya fito daga dakin yana wani irin huci! na bacin rai!

Baba Ladidi ta haske shi da fitila tace"Wai menene? Bafa nasan neman fitina me tayi maka."?

Yace."Baba kina kwance da kina bacci yarinyar nan ta fita da daddare tana zance da wani d'an iskan yaro kazami! duba time goma na dare har ta wuce."

Baba ta kalli Sayyada dake tsaye tace"Wato da kikaga nayi bacci shine kika fita zance ko wai ke Sayyada me yasa bakya jin magana ne."!?

Tana kuka tace"To Baba ai ba laifi nayi ba shima yana zance da wata kuma ai har yanzu bai tabbatar muku da cewar zai aure ni ba to kawai sai a hanani inyi zance."

Baba Marka dake kwance ta mike zaune tana fad'in" Yanzu ke Sayyada me zaki ci da wannan yaron Talle bai aje ba bai bawa kowa ajiya ba haba kiyiwa kanki fad'a mana, koda Sadam! bai aure ki ba Talle ba sa'an auranki bane saboda duk gari kowa yasan ba yaron arziki bane ko ya aure ki ba zaki samu kyakkyawar kulawar da muke so ba."

"To ni dai shi nake so A kyaleni kawai." Tafada tana goge fuska....Sadam! yace."Shikkenan Baba ku rabu da ita tunda shi take so sai a daura mata aure dashi ni idan Allah ya kaimu gobe kafin in wuce zan samu iyayensa sai a tsayar da magana."

Sayyada gabanta ya yanke ya fad'i!!!! da jin abinda yace cikin zuciyarta tace "Allah yasa ba da gaske yake ba lokaci kankani jikinta yayi sanyi.

Baba Ladidi tace" Shikkenan ni na cire bakina daga wannan sabgar tunda dai kin nuna mana cewar kin fi son ki auri Tallen shikkenan, kai Sadam! idan Allah ya kaimu gobe da wurwuri sai kuje da Kawunka ku fara maganar auran Allah ya za'ba abinda yafi alkairi."

Ya kama hanya futa Baba Marka tace"Yau ba anan zaka kwana bane."!? Yace."Eh can sashen Kawu Tanko zan kwana." Tace"To Allah ya tashemu lafiya." Ba tare da ya amsa ba ya fita.

Sayyada tayi tsuru a zaune Baba Ladidi da Baba Marka suka gyara kwanciyarsu ko wacce ta cigaba da baccin ta suka bar Sayyada da tunanin ya zatayi ta fitar da kanta.

Juyi kawai takeyi ta kasa bacci ga gari yayi duhu sosai kowa yayi bacci da alama ma sha biyu ta wuce sai dai karfe daya kuma, mi'kewa tayi a hankali ta lalla'ba ta fice kai tsaye 'kofar Kawu Tanko ta nufa......Shiru kowa yayi bacci ta lalla'ba ta nufi dakin da take tunanin yana ciki aikuwa takalmanshi ta gani kofar a bud'e amma ya sayo ta ta tura ta shiga babu fargabar komai a tattare da ita.

Yana kwance kan katifa da wayar a hannunsa yana dubawa da alama wani abu mai muhimmanci yake dubawa yana sanye da vest fara sai gajeran wando kirjinsa da abinda yayi cinyoyinsa zuwa 'kasa wani irin gashi ne akwance da alama mutum ne shi mai gargasa a jiki ko ga yanayin sumar dake kansa zaka gane.

Da sauri ya mi'ke zaune ganinta a tsaye a kansa ya kunna hasken wayarsa yana haske fuskarta.

"Ke! Lafiya."!? yafada cikin mamaki.!

Wasa ta farayi da hannunta ta jawo jelar dankwalinta tana taunawa, haushi ya isheshi saboda yanayi na dare yasa ya taushi zuciyarsa yace." Wai ba dake nake magana ba me ya kawo ki nan."!?

Zubewa tayu gwiwa bibbiyu ta fashe da kuka!

A razane! ya mike isa inda take, tura kofar dakin yayi sannan ya dawo inda take ya mikar da ita tsaye tare da toshe mata baki da hannunsa guda, hannunta yaja suka isa bakin katifar ya zaunar da ita kusa dashi har yanzu hannunsa na rufe da bakinta ya kura mata ido yana kallo itama shi take kallo da ido yake mata magana ta gane abinda yake nufi sai tayi kokarin had'iye kukanta sai da ya tabbatar tayi shiru sannan ya bude mata baki.

A miskilance yace."Menene."!? Shiru tayi tana turo baki yace."Ke yanzu kawai sai ki shigo min daki kina kuka kawai saboda ki jawo min magana ko sharri kike so kiyi min."!?

Girgiza kai tayi, Yace."To kan wane dalilin kike kuka kuma me kike so nayi miki cikin dare kika shigo min daki."

Cikin kuka tace"Nifa ba cewa nayi kaje gidansu Talle ba na fasa auransa."

Shaf ya manta da maganar mana Yace."Wannan dalilin ne yasa kike kuka."? daga kanta tayi yace."Me yasa to ba kyajin maganar magabatanki."? Shiru tayu tare da sunkuyar da kanta

Yace."Tunda dai aure kike so to za'ayi miki insha Allahu."! Ta kalleshi da sauri! Sai ya d'aga mata girarsa guda ta mai da kanta kasa yace."Ko ina da wata magana."!?

A hankali tace."To kai ba zaka aure ni ba."! Yace."Dama ai bance zan aure ki ba su Baba ne suke maganarsu bana sha'awar auran zumunci."

Sai hawaye ya fara zubo mata ta mike tsaye shima ya mike fuskarsa a daure yace."Idan zaki daina kuka da damuwa ki daina Aure kamar anyi miki da Saurayinki anyi an gama."

Tace."To sai me? ai shima mutum ne."! kofar dakin ta bude ta fita tana kuka ranta in yayi dubu ya 'baci.!

Murmurshi yayi ya koma ya kwanta ya cigaba da abinda yake.

Washe gari ya tashi da wuri ya tashi ya shirya tsaf ya nufi sashen su Baba domin su gaisa.....Lokacin da ya isa sashen suna karya kummalo Baba Marka ta shimfida masa tabarma ta kawo masa kayan karin kummalo ya karya Baba Ladidi ta fito da mafici a hannunta ta zauna kan kujera 'yar tsuguno tana fad'in"Ashe ka shigo." Yace."Eh Baba." Gaisawa sukayi yace."Kina fiffita da safe sai kace wata mara lafiya." Tace"Aini jin zafi ne dani bana rabo da mafici Tace."Ina fatan dai kunje gidan Su Talle kunyi maganar." Yace."Sai na k'ara dawowa za muje." Tace."Ai shikkenan to Allah ya kara dawo da kai lafiya." Yace." ameen. Suna nan zaune ta fito daga dakin cikin hijan na makaranta isilamiyya ta jakar buhu a rataye a kafadarta ko kallonsa ba tayi ba tace"Baba ni na tafi."

Baba Marka tace"Kina kallon Sadam! kin wuce ba tare da gin gaishe shi ba." Banza tayi mata tayi tafiyarta."

Baba Ladi tace"Ki kyaleta kawai kina ganin ko karyawa ba tayi ba zata fita jiya ma ba tayi wani baccin arziki ba saboda an hanata soyayya da Talle."

Baba Marka tace"Ni dai banga abinda Sayyada zata ci da Wannan yaron ba."

"To ai tunda shi ta za'ba zata aura shikkenan Allah ya sanya alkairi." Sadam! na jinsu suna zancen su uffan bai ce musu ba har ya gama karyawa kana yayi musu sallama ya kama hanyar Kaduna.

29/5/2020

*BINTA UMAR ABBALE*
Chapter 7 · 0% Book details