← Book details Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 30

Sashe 1

Ni Da Yaya Sadam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu Nazari da aikin da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta_
____________________________________

_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kud'i ne ga mai bukatar karanta littafin zai tura #400 kacal ta wannan accont d'in.......0542382124......Binta Umar Gtbank.....Idan kuma katin waya zaka tura to sai ka tuntu'beni ta wannan numbars din nawa zan fad'i yanda zaka/ki biya kudin......08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar karanta wannan littafi to zaku tura katin airtal ko orange na dala dari a wannan numbars......90899076 _88137740.....Dala d'ari itace a madadin d'ari uku kud'in Najeria*_

Dukan Yabo da godiya sun tabbata ga Allah mad'aukakin Sarki Allah kayi dad'in tsira ga Annabi Muhammad SAW Ina rokan Ubangiji akan yayi min jagora ga dukanin abunda na sanya a gabana. Allah yanda ka bani ikon fara rubuta wannan littafi lafiya Ina roko ka sanya na gama lafiya. Allah ka sanya in rubuta abunda zai amfani al'umma Allah ina rokan ka hane ni rubuta abunda zai cutar da Al'umma.
************************

_Kuna raina masoya a ko ina kuke a fad'in duniyar nan ina mi'ko gaisuwa a gareku masoya na na nesa dana kusa wanda na sani da wanda ban sani ba ni Binta ina matukar alfahari daku_

💘💘💘💘💘💘💘

*A rashin sani!*

Wannan littafin mallakina ne kuma 'Kirkirarran labari ne banyi don wani ko wata ba duk wanda yaga yayi dai-dai da yanayi na labarinsa to a rashin sani ne.

*Gargadi da jan kunne!*

Ban yarda a juya min yanayin labari na ba ta ko wacce siga ban yarda wani ko wata ya siyar min da littafi ba duk wanda ya aikata d'aya daga cikin abunda na fad'a To Allah ya isa! zan had'ashi da Allah ya bi min hakkina!

*A lura*

Mu lura da lokacin ibada 'yan uwa don girman Allah idan lokacin sallah yayi 'yar uwa komai dad'in da littafi yake miki ki aje kije ki gaishe da Ubangiji sai ki cigaba, Allah kasa mu dace.

*Gaskiya d'aya ce daga 'kinta sai 'bata*

Idan kin san zaki biya kudin karanta wannan littafi ki futar min dashi waje to kiyi hakuri don Allah bana bukatar ki, Ni ina bukatar mutane masu amana ne Littafi mallakina ne kun biya kudin karatu ne banyar da a futar min da book ba ban yarda a turawa wani ko wata ba idan kikayi min haka to Na barki da Allah!!!!

*Gare ku masu siyar min da book*

Ba zan gaji da cewa Allah ya bi min hakkina ba a kanku kuma bazan daina rubutu ba a kanku idan abunda kukeyi shine dai-dai a gurunku to sai ku bada himma akwai dai ranar 'kin dillanci!!!!!!!

Free Pege 1

*JIGAWA STATE*

Jahar jigawa Akwai wani 'karamin gari mai zaman kasan a cikin jahar, sunan Garin *Dabi* 'karamar hukuma ce guda wacce ta tara fulani usul a cikinta, Garin bashi da yawan mutane sosai Amma Allah ya albarkace su da gona ki da abubuwan more rayuwa don duk wanda ya shiga garin sai yayi sha'awar shi saboda dad'in sa suna da wuta da ruwa sannan suna da makarantu na boko da isilamiyya da allo Gaskiya Mai wakilatar garin yana kula dasu sosai, Jama'ar dake cikin garin *Dabi* suna da wayewar kai babu laifi sai dai idan suka fito cikin gari ne suke komawa 'yan kyauye mussaman idan suka shigo garin *Kano* sai suji tamkar a saudia suke saboda tsabar murna. Yawancin jama'ar garin 'yan uwan juna ne shiyasa suke zumunci sosai da sosai sam baka ta'ba jin wata 'baraka ta fito daga cikin 'karamar hukumar saboda suna da had'in kai kuma suna aiki da Iliminsu dai-dai gwargwado.

Wata 'katuwar 'kofa na kutsa kaina ciki na fara rarraba idona.

Kofafin na gani sun kai ashirin da wani abu kuma ko wace 'kofa akwai mutane a cikinta can na hango wata Matashiyar budurwa ta futo daga wata 'kofa a guje! tana nema ta bugeni nayi saurin kaucewa ina binta da kallo naga ta nufi babbar kofar da zata sada ka da ainihin 'kofar gidan gabad'aya.....Kafin in dawo daga tunanin da nakeyi na hangoshi yana talle mata 'keya tare da haurinta da takalminsa irin na sojoji ita kuma sai murza ido take tana zum'bura baki.

Nayi saurin 'buya bayan gatanga har suka wuce inda nake la'be sai na fito a hankali na bi bayansu.

'Kofar da yarinyar ta fito nan naga sun nufa sai na rufa musu baya domin inga 'kwal Uwar daka.

Tana zaune tana gyara fitilar 'kwai irin mai kamar a ci balal d'in nan sai mita takeyi tana fad'in "Marka kinga ja'irar yarinyar nan ko sai dai ta fasa min 'kwan fitila sannan taji dad'i."

Marka dake zaune a kofar d'akinta tana kad'in lagwani tace"Aifa! Ladidi kin manta halin Sayyada kenan nazo fitowa daga 'bandaki naga ta farara da gudu tana dariya sai kace wacce tayi abin arziki."

"Ki rabu da ita Marka ai yau sai na zane mata jikinta wallahi ki duba ki gani 'kwan fitila ta ya kai shekara guda a jiki amma sai da tayi sanadin sa har sauran kalanzir d'ina sai da ta zubar."

Marka tana kad'i tace"Kamar gaske ai ba zaki iya dukanta ba humm! sau nawa Sayyada nayi miki laifi kice zaki hukunta ki kasa Allah dai ya kyauta mutum d'aya ne yake maganin Sayyada."

Tace."To ki zuba ido kisha kallo yau sai na hukunta ta kan 'barnar da tayi mi........Kafin ta 'kara maganar ta sai suka jiyo gunjin kukanta daga soro!

"Wayyo na shiga ukana!! Wayyo baba Ladidi Wayyo Baba hiiiiiiii!hiiii! Wayyo Allahna baba Ladidina."!!!!!!!

Ai da sauri Baba Ladidi ta mi'ke don har zaninta ma ya kusa fad'uwa tayi sauri ta gyara tace" Marka kin gani ko ta futa an zalince ta kai! jama'a mutane basu da tsoron Allah yanzu daga futar ta ko minti biyu bata yi ba har an doko t.......Maganar ta ta katse lokacin da ta hango shigowarsu yana talle mata 'keya tare da rankwashinta aka.

Komawa tayi ta zauna tasha kunu! tana hararasa.

Baba Marka ta washe baki tana fad'in"Maraba lale sannu da zuwa soja marmari daga nesa sannu da zuwa sannunmu zauna ga gurin xama na gyarama ka." Tafada tana shimfida masa tabarmar dake kusa da ita a jinge ne.

A nutse ya cire takalmin sa ya zauna cikin nutsuwa yana gaisheta.....Baba Marka ta amsa cike da walwala da farin ciki tace"Ashe ka shigo gari shiyasa naji waccan kafirar tana kuka dama ai yanzu yanzu nake fad'in kai kad'ai ne maganinta."

Ya kalli gefan da suke zaune Baba Ladidi ta tsuke fuska sam! ta'ki dariya ballanta ta sakar masa fuska saboda ya doki 'yar gidanta.

Fuskar nan a had'e yace."Baba na same ku lafiya."?

Tace"Yo da baka sameni lafiya ba ai ba zaka ganni a zaune da'kau! ba haka kawai daga saukar ka sai ka fara cin zali ni bana son haka wallahi."

Shiru yayi yana kallonta tsawon minti sai ya girgixa kansa kawai ya mai da hankalinsa kan Baba Marka suka cigaba da hirarsu.

Sayyada ta zauna kan 'kafafun Baba Ladidi tana shar'bar majina tare da kuka wiwi "Allah ya saka min Baba wai me nayiwa wannan ne ya tsaneni! kullum sai ya dakeni Allah ya isa ban yafe ba."!!! Tana kuka take wannan maganar fuskarta duk tayi jage-jage da hawaye.

Ya juyo yana kallonta Tayi sa'ke_sa'ke! kan lanjararrun 'kafafun Baba ladidi wanda da 'kyar take tafiya dasu amma saboda tsabar so da sangarta ta bari Sayyada na tumurmusar su........Sarkin Zuciya da miskilanci kawai sai ya mi'ke! a fusace ya zare blet din 'kungunsa ya shiga tabka mata a jiki.

Daga Sayyadar har Baba Ladidin gigicewa sukayi Baba sai kare Sayyadar take wai kar ya daketa shi kuma yana sane ya dinga labta mata blet din ta ko ina!!

A guje! ta mi'ke ta nemi hanyar tsira bayan Baba Marka ta 'buya tana makyarkyata!

Baba Ladidi ta saka kuka tana fad'in" Wannan rashin imani da yawa yake Wallahi tallahi Sadam! zanyi maka Allah ya isa kan kana dukan 'yar nan zan iya bar muku garin gabad'aya mu koma wani gari ina dalili umm! me yarinya tayi maka kawai zaka tsane ta babu dama ka shigo gari shikkenan hankalinmu ya tashi yau har dani ka had'a ka doka tom zamu bar muku garin *Dabi!!."* Tana gama maganarta sai ta dingisa kafafu ta shige d'akinta tana share hawaye.

Sayyada ta mi'ke zata bi bayanta ya buga mata wata razananniyar tsawa"Koma ki zauna munafuka 'kazamiya kawai."!

Ta koma ta zaune tare da sunkuyar da kanta 'kasa! duk rawar kanta tsoron sa takeyi mutum sai kace mala'ika mugunta a cikinsa har da ta siyarwa gashi tunda take dashi bata ta'ba ganin dariyarsa ba.

Mi'kewa yayi fuskar nan a murtuke ya nufi d'akin Baba Ladidi.....Ya shiga ya tarar da ita tana had'a kaya cikin wata tsohowar akwati.

24/5/2020

*BINTA UMAR ABBALE*
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu masu nazari da aiki da Iliminsu, burin 'kungiyar a ko da yaushe ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyan ta_
_____________________________________________

*_Littafin Ni da Yaya Sadam! na kud'i ne 1 _ 2 ga mai bukatar karanta littafin zai tura #400 kacal ta wannan accont d'in.......0542382124......Binta Umar Gtbank.....Idan kuma katin waya zaka tura to sai ka tuntu'beni ta wannan numbars din nawa zan fad'i yanda zaka/ki biya kudin......08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar karanta wannan littafi to zaku tura katin airtal ko orange na dala dari a wannan numbars......90899076 _88137740.....Dala d'ari itace a madadin d'ari uku kud'in Najeria_*

Free pege 2

Ganin inuwar mutum a tsaye a kanta yasa ta d'ago kanta suka had'a ido sai tayi saurin mayar da kanta 'kasa ta cigaba da harhad'a kayanta.

Ya lalla'ba a hankali ya shiga d'akin ya samu gefan gadon karfenta ya zauna yana me sassauta fuskarsa, yace."Baba Ladi."

Banza tayi masa ta cigaba da harhad'a kayanta.

Sai ya sakko daga gadon 'karfen ya gurfana gabanta tare da ri'ke hannunta yana kallonta a marairace yace."Wai me yasa yanzu kika daina sona ne."!?

Da hanzari tace"Saboda kana zalintar marainiyar yarinya."
Chapter 1 · 0% Book details