← Book details Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 30

Sashe 9

Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A hankali na saka hannu ina knocking d’in k’ofar. Daga ciki principal ya amsa da “Yes come In.” na saka kai na direct cikin office d’in. Daidai lokacin da idanuwana suka sauka cikin na ustaz hancina ya shak’i k’amshinsa. Ji na yi k’afafuna kamar ba a jikina suke. A raina na ce “Nan ma ka biyo ni ne?” “Da principal zai lura lokacin zai ga yarda k’irjina yake bugun gaske idanuna suka tara k’walla. Na shiga office d’in a nutse da sallama. “Good morning sir!” Na furta muryata a nutse. Ina satar kallon Ustaz da ya yi kamar bai ganni ba. “Morning AYSHA Imam. Baki ga bak’o ba?” Na juya ina satar kallonsa murya a k’asa na furta “Good morning.” Ya d’ago daga kallon wayar da yake fuskarsa a ‘dan tsuke ya furta “Morning…” Daga haka bai sake magana ba ya mayar da kansa kan abinda yake na daddanna waya. Principal ya mik’e min wasu files “Maza ki kaiwa Emeka, ki ce masa ya yi signing before a fita break..”

Na amshi files d’in ina d’an durk’usawa. Na fita raina a b’ace. Zuciyata cike da mamakin kallon da Ustaz ya min kamar bai sanni ba. Sai na ji sam ban ji da’di ba.

Haka dole na koma Islamiyya ba don raina na so ba, sai don zuciyata ta kasa dauriyar rashin ganin ustaz. Ranar ma ko kallo ban ishesa ba, ya yi karatunsa ya fita fuskarsa a d’an tsuke.

Ina komawa gida na tarar da abinda ya kusa fasa min zuciya. Tun daga bakin gate nake jiyo hayaniya a cikin gidan mu. Muryar Mami a sama take sake furta “Wannan ma ai zance ne, kuma ba mai yiwuwa ba, Ayshan nawa take da za’a d’auko maganar aurenta yanzu, to wallahi in dai ina numfashi ba mai aurar da ita a wannan lokacin..komai zai faru sai dai ya faru….

Gabana ne ya yi wani irin mugun fa’duwa na waro ido a hankali na furta “Aure kuma? Ni Ayshan za’a yiwa aure yanzu?” Murya a sanyaye na yi sallama, gaba d’aya suka zubo min ido, kamar sun samu Tv. Take na gasgata abinda zuciyata ta gaya min. Aurar da ni za’a yi. Gefe na ja na zauna idanuna tuni suka fara bulbular da hawaye ina kallon Mami na na ce “Mami aure za’a min?” Mami da itama nata idanun suka yi jajir suna son zubo da hawayen, ta furta “Kul Aysha! Kada ki sake ki zubar min da hawaye anan, wannan maganar ki ‘dauketa tatsuniya wallahi in dai sunana Fateemah y’ar halak kuma cikin iyayena sai na cika burina a kan ki… babu wanda ya isa ya aurar da ke a wannan k’ananan shekarun sai kace a karkara. Ko su karkarar yanzu an daina irin wannan auren. Wuce ciki ki zauna…” Na kasa wucewa cikin zuciyata sai kakkarwa take, ni na san halin Abba yana da kafiya da naci akan abinda ya saka gaba, ba wanda ya isa ya canja masa ra’ayi, baya ma tank’waruwa ko ka’dan, irin mutanannan ne da ake cewa taurin kai kamar mutanen farko. Don haka ban san sanda na kece da wani irin kuka ba musamman da na tuna shikkenan son da nake wa Ustaz ya zama tarihi kenan, ba zan aureshi ba? Mami hankalinta ya sake tashi, ta ja hannu da k’arfi muka hau sama cikin b’acin rai da k’unar zuciya take furta “Ba zai yiwu ba, ki gaya masa ma tun farko kada ya yi abinda zamu zo muna samun sab’ani da shi.

“An da’de baa samu sab’anin ba, aure ne dai ba fashi sai dai ki yi duk abinda za ki yi. Haka kawai ba zan ga samu naga rashi ba. Nagartaccen mutum irin wannan ya zo neman auren y’ata ko a primary take tsigeta zan yi na ba shi…” muka ji muryar Abba a sama yana fa’da yana tsaye a k’ofar shigowa…

Mami ta juya a fusace tana furta “Kada mu yi haka da kai Abban Aysha….

Tsaki ya ja kawai ya shige parlor jin ana kiran sallah.

Bayan Sallahr Isha, a al’ada irin ta gidanmu bazuwa ake, a tsakargida kan tabarma a ci abinci. Yau d’in ma haka ce ta kasance sai dai ni ina daga wani d’an lungu a zaune kamar yarda Mami ta umarce ni. Abba ya juya yaga kowa bai ganni ba. Ya kalli Mami ya ce “Ina Aysha?” “Ina zaka ga Aysha anan? Alhali ka birkita mata kwanya tun d’azu take kuka..” “Ta shirya fara na jini, don aure ba fashi, ki kuma sanar da ita k’arfe takwas bak’onta zai zo. Don Allah ki sata ta wulak’anta martabar gidan nan kiga abinda zan
Aikata.. Babban mutum ne da ba zai juri rashin kunya ba…” Daga haka bai saurari surutun Mami ba ya wanke hannunsa ya saka a cikin tuwo ya fara ci…

Ina tsaye ina jin k’afata na rawa. Babban mutum nake ta nanatawa a zuciyata it means mai iyali dattijo. Na runtse idona ina jin wani zafi a k’asan zuciyata. Ina jin yaro ya yi sallama aka amsa masa ya ce “Wai akwai bak’o a waje…” Na ji zuciyata ta wani irin hantsilawa har sai da na dafe k’irjina. Muryar Abba na ji yana cewa “Kai ALIYU jeka ka shiga da shi sitroom, kai kuma Usman jeka ka kira min Aysha… Ji na yi kai na ya wani irin sarawa. Usman da ya nufo inda nake ya tsaya yana kallo na. “Au da kina tsaye kina ji?” Hawayen idona na d’auke na d’aga masa kai na. “Ki je in ji Abba kina da bak’o… Saura ki je masa da wannan banzan hawayen shashasha tun baki san wa ne me neman aurenki ba kin sakawa kan ki damuwa…” Ban bi ta kansa ba na nufi inda Abba yake. Mami kuka take tana sake rok’onsa ya janye maganar sa. Kallona Abba ya yi ya ce “Ki je ki shirya ki je sitroom kina da bak’o saura ki je ki nuna masa rashin tarbiyya…” Na juya jikina a sanyaye madadin na je na canja kayan Wucewa na yi wajen haka idona a damalmale da hawaye na tura k’ofar, muryata cike da k’unci na masa sallama.. k’amshin turaren Ustaz na ji ya baibaye hancina zuciyata na bugu nake son d’agowa naga ko shine ban dawo daga tunanin da nake ba, na ji ya ce “Aysha Imam ya gida?” Ko daga barci na tashi na san muryar Ustaz na yi saurin d’ago kaina idona ya sark’e cikin nasa, yana zaune yana matse yatsunsa cikin na juna fuskarsa d’auke da murmushi…..
Cikin mamaki na furta “Ustaz!” Ya d’aga gira yana murmur ya furta “Ayshatu….

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️


Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎

𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️

Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

Arewabooks @nazeefah

Wattpad@Nazeefah381

08033748387.

★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 8

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR

Kasak’e na yi ina kallonsa, shi kuma sai sakin murmushi yake ya firta “Kin yi mamakin gani na ko? Koda yake na san ba lallai ki yi mamakin ba don tini zuciyarki ta sanar da ke zan zo d’in ko ina so ko bana so, haka ne?” kallonsa kawai nake kafin na
Ankara da abin kunyar da na so aikatawa na runtse idona ina jin yarda zuciyata ke harbawa da k’arfin gaske. Bana son na bu’de idona balle na tarar da
Mafarkin da na saba ne.. “Ki yi hak’uri nazo gidanku ba tare da saninki ba, ban kuma nemi amincewarki ba ko? Na yi hakane saboda koyi da sunnar manzon Allah s.a.w, na fara
Neman izinin iyayen yarinya kafin ita yarinyar. Na san tuni ki fuskanci manufata ba ke ba ma wasu da dama a ajinku sun san inda zuciyata da ruhina suka karkata, kema kuma a idonki na gano zallar son Ustaz da k’aunarsa…” Da sauri na waro idona ina kallonsa. Ya ‘daga min girarsa guda da ta bada wani shape mai kyan gaske. Yana lumshe idon. “Don't pretend Aysha na san kina so na, albushir guda da zan miki ina miki so ninkin miliyoyin naki…” wani sanyi na ji yana ratsa zuciyata ban san sanda na saki wata siririyar ajiyar zuciya ba. “Ba ki ce komai ba?” Na sunkuyar da kai na wani murmushi da ban shirya zuwa masa ba yana kufce min. Cikin siririyar murya na furta “Me Zan ce Ustaz…” “Ki ce I love you too…” Da sauri na saka tafin hannu na rufe fuskarta, ina ji Ustaz ya saki ajiyar zuciya ya furta “Yawaitar kunyata a idanunki ya tabbatar min da zazzafar soyayyata a ranki. Amma naga kafin ki fito kamar kin yi kuka ko dai baki so fitowar ba ne?” “Ai ban san kai ba ne…” Na yi saurin toshe bakina jin abinda bakin ya furta.
Chapter 9 · 0% Book details