← Book details Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 30

Sashe 1

Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/EZyeAwHEGGhJz1pRBmmale

NAGA RAYUWA♥︎♥︎♥︎

𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️

Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

Arewabooks @nazeefah

Wattpad@Nazeefah381

08033748387.

★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 3

Da k’yar Umma Ta runtse idonta ta furta “Innalillahi wa inna ilaihirraji’una…” wasu hawaye na zubo mata. Abba cikin k’arfin hali ya saki kansa da ya ji ya masa wani irin duum ya furta “Uban me kika masa ya sake ki”
Ban amsa ba illa damk’e hannun Mami da na yi a cikin nata hannun cikin tashin hankali kaf jikina rawa kawai yake yi.

“Kin ga ko Fateemah abinda nake gaya miki, wannan shagawab’atan da kike yi ba hanya bace mai b’illewa, ga shi nan yanzu abin da ta janyowa mana ba mamaki bata kai budurcinta gidan Miji ba”

Umma ta furta cikin wata irin karyayyiyar murya da ta bayyana karyewar zuciyarta.

Mami a kufule ta furta “To hasashenki bai zama gaskiya ba, tunda ga shi a rubuce ya furta da kansa bai d’ora mata idda ba, idan kuwa haka ne ta ya zai san bata kai wani budurci ba? Kawai dai butulcin y’ay’a maza zai nuna muku.”

Abba ya saka hannu ya wafce takardar da take hannun Mamin idanunsa ya zuba akan gajeran rubutun mai saka dubban bak’in ciki a zuciya. Ya lumshe idonsa bayan ya tabbatar da abinda Mamin ta fa’da. Wani irin bak’in ciki ne yake nuk’urk’usar zuciyarsa don har yana jin wata irin suka a zuciyar tasa. Ya lumshe idonsa yana tunanin Halaccin da Ustaz Ahmad zai yi masa kenan? Duk da k’ank’antar y’arsa ya cireta a makaranta ya ba shi aurenta shine yau daga tarewarta ya saketa?

Ya d’ago idanunsa jajur yana kallona ya furta “To me kika masa ya sake ki Aysha? Don kalmar bakomai ba zan yarda da ita ba ko duk jikina kunne ne.”

Na runtse idona ina sake jin takaicin Ahmad a raina. Ji dai yadda ya sanya iyayena b’acin rai. Umma da Mamina hawaye suke. Shi kuma Abba nasa idanun ya tara hawayen sai dai ba su kai ga zubowa ba. Amma bakinsa har rawa yake. “Wallahi Abba ba abinda na masa, ka kirasa ka tambayesa ka ji idan baka yarda da ni ba…” “kira kam Ai ya zama dole….” Ya fa’da yana mik’ewa ya fice daga parlorn yana danna wayarsa fuskarsa a murtuke. Umma kallo guda ta mana ni da Mami itama ta mik’e ta shige d’akin Abba. Ni na san a lokacin ji take kamar zuciyarta ta fito don tsananin b’acin rai.

Mami na ta dafa ni tana furta “Share hawayen ki Aysha, ni na san ba abinda kika masa. Iskancine kawai da kuma nunawa mutane isa, ba su suka nuna masa sha d’in wata tsiya ba ce. Kwanta abinki ki yi barci don na san jiyan ba wani isashshen barci kika samu ba. Bari na je na samu dandazon munafukancan y’an saka ido na san me Zan gaya musu.

Daga haka itama ta mik’e ta fice tana d’an murmushi tana cije bakinta ha’de da k’wafa duka lokaci guda.

Lumshe idona na yi wasu hawaye suna zubo min. Na saka hannu na share hawayen ina sake tsinewa Ahmad a zuciyata.

Madadin barci tunanin rayuwata ne ya dawo min daki-daki cikin kwanyata girmana k’iruciyata da ha’duwata da Ahmad da zan ce a yanzu ha’duwar tamu ta zame min mummunar k’addarar da zan ce da ina da iko da na koma baya na goge ta tas daga cikin shagon rayuwata…..

★★★

Alhaji Imam Khalil shi ne sunan mahaifina, da kowa ya san shi. Asalin sunan Abdurrahman ne, amma sakamakon ya ci sunan kakansa ne yasa ake ce masa Imam. Mahaifina su biyu ne kacal a wajen iyayensa, daga shi sai k’anwarsa Dije, da muke kira Umma Dije, sun taso cikin tsananin soyayyar Iyayensu game da kulawa. Kasancewar mahaifinsa babban malami hakan ya sa ba su ingantacciyar tarbiyya, don duk wanda ya ha’da da su dole ne ya yaba da nutsuwarsu, da hankalinsu. Mahaifina tun yana shekara ashirin da uku aka masa auren fari, da Ummana Sa’adatu, y’ar k’anin Babansa wanda da kansu suka k’ulla soyayyarsu, kuma kowa ya yi tsananin murna da farin ciki da hakan ta kasance. Abbana da Ummana sun yi zaman aminci, ta yadda suke ganin girman junansu, suka kuma gina rayuwar aurensu da soyayya mai tsafta da babu algus a cikinta.

A shekara ta biyu da aurensu ne Umma ta ta samu cikin Yaya Muhammad, bayan shi aka haifi Yaya Sadik, sai Yaya Umar, sai Yaya Usman, lokacin da aka haifi Yaya Usman babu da’dewa Abba na ya auro Fateema Mami na, haifaffiyar fulanin yola. Su kuwa su Abbana fulanin potiskum ne.

Tunda Mami ta shigo gidan ta fuskanci Umma na bata kishi da ita matsayin k’anwarta ta d’auketa, sai itama ta zubar da shawara da zugar k’awaye itama ta kwantar da kanta suke zaune lafiya.

Shekararta d’aya a gidan, Umma ta sake haifo Yaya Ali ita
Kuma ko b’atan wata bata yi ba tunda ta zo gidan. Bayan shekara d’aya da rabi sai Umma ta sake samun ciki ta haifo Yaya Hamza. A kansa ne Umma ta ce ta bawa Mami shi duniya da lahira lokacin da ta tabbatar da shigar cikina bayan wata uku da haihuwarsa. Sai dai me? Wani ikon Allah yana komawa hannun Mami da wata d’aya Ubangigji ya karb’i ransa.

Mami ta shiga damuwa sosai, don haka Umma ta ce ta kwantar da hankalinta tana haihuwa zata bata abinda ta haifa. Tunda likitoci sun tabbatar Mami ita da haihuwa sai wani ikon Allah.
Cikin farin ciki ta dubi Umma na ta ce “Ko mace ce?” Umma ta ‘d’aga kai duk da a k’asan ranta tana jin Anya zata iya bada y’a mace, tunda abu ne da take mafarkin son samunsa saboda duka yaranta maza ne. Shima Abba ya sha furta mata duk sanda ta haifi Mace zata sha gatan da baa tab’a yiwa wani a gidan ba.

Lokacin da aka tabbatarwa Umma da ta haihu kuma mace ta ce da ni ta ji hankalinta ya tashi matuk’a, ta kuma yi dana sanin furtawa Mami bada kyautar abinda ke cikinta. Sai dai ba yarda ta iya ba zata iya kallon idon Mami ta ce ta janye kyautar ta ba. Ga likitoci sun tabbatar mata ya zama dole ta hak’ura da haihuwa in dai tana son lafiyarta ta ‘dore.

Don haka ranar suna Umma ta ce ta bawa Mami ni. Ba wanda bai dinga mata kallon mamaki ba. Mami kuwa tsabar murna rungume Umma ta yi tana hawayen farin ciki. Ba wanda bai fa’di wautar Umma ba sai dai ta saka yatsa ta toshe kunnenta ta kuma kulle duk wata k’ofa da y’an gulma zasu mata tasiri. Ta mik’awa Mami ni ta ce “Na bar miki ita Fateema duniya da lahira shayar da ita kawai zan dinga yi.” Mami ta rungumeni tsam a k’irjinta cikin tsabar farin ciki tana yi mata godiya don da gaske ta ji da’din kyautar.

Mami da kanta ta saka min suna Nana Ayshatu, Saboda ta da’de tana son sunan. Ba wanda ya k’i amincewa tsakanin Umma da Abba duk da su ma cikin su kowa nada sunan da yake burin saka min. Amma suka amince da Ayshatu da Umma ta saka min.

Ta mayar da ni hannunta, sai dai idan ina son Nono ta kai ni na sha wajen Umma da daddare kuwa k’arfi da yaji ta mayar da madara ce abincina don ba zata yarda na dinga kwana a wajen Umma ba.

A farkon shekaruna na taso cikin matuk’ar shagwab’a da sangarta, Don Mami bata son ko fa’da a min balle duka yanzu duk girmanka zata maka rashin
Mutunci. Ana min magana zata ce a k’yaleni yarinya ce, Ko Umma da take yawan tsawatar min sai da suka yi tashin hankalin da ta tattara ni ta watsar ta daina yi min fa’da. Ta ce min sai dai kawai a koda yaushe bakinta cikin yi min addu’a take. Idan kuma ta faki ido ko idan Mami bata nan tas take wanke ni da fa’da. Wani lokacin nasiha.

Tun ina yarinya ban saba saka manyan kaya ba sai k’ananan kaya don haka na tashi kamar y’ar turawa, musamman ina da hasken fulani da gashi mai tsayi. Ina da tsiwa ta gasken gaske da rashin kunya don haka yayyena ke cin Uba na. Adon gashi Mami take min sosai a wannan shekarun duk inda na shiga sai an yaba ni. Mami cikin jin da’di da farin ciki Zata ce “Tubarkallah, maye ya ci kansa kurwar AYSHA ya fi gaban ci.”

Umma da taga na yi shekara goma cikin kwantar da murya ta dinga bawa Mami shawarar a dinga saka min kayan hausawa ko na saba da su. Amma Mami ta yi funfurunfus ta k’i har ma ta fa’dawa Umman maganar da ta tsaya mata a rai cewa ta yi “Umma kada wata rana fa ki ce zaki karb’e AYSHA a wajena, don naga kamar kina tantama da tarbiyyar da nake bata?” Hankali tash Umma ta dinga bata hak’uri tana furta “Ba nufi na kenan ba Fatima, amma Allah ya baki hak’uri In sha Allah ba zan sake magana akan abinda ya shafi AYSHA ba.” “Ya dai fi.” Mami ta fa’da fuskarta a ha’de ta kuma ja hannuna muka bar wajen. Tun daga ranar bata sake magana ba. Su Yaya Muhammad ne ma basa gani su k’yale su kuwa Mami wankesu take tas.

A makaranta na taso da hazak’a da wata irin kwanya mai d’auke karatu duk girmansa. Ina shekara goma na sauke Alkur’ani. Shekara sha d’aya kuwa ina Js One.

Sanda na shekara sha biyu ne, ba zan manta ranar da komai ya sauya a gidan mu ba. Aka wayi gari Mami na ta tattara duk wasu kayan sawata ta rabar da su. Na sha kuka a ranar don ina matuk’ar son kaya na. Bata kulani ba ta dai ja ni mun fita. Kasuwa muka shiga ta dinga siya min atamfofi da laces da yadin Hijabai. Da after dress masu kyau. Muka biya wajen tailor ta saka ya auna ni don a yi min d’inki. Ta kuma ce masa urgent take so.
Chapter 1 · 0% Book details