← Book details Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 30

Sashe 10

Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Ustaz ya saki ya furta “Ni na sani ai, da kin san ni ne kwalliya mai kyau zaki cab’a min ki fito kina iyayi irin yarda budurwa take wa Habibinta ko?” “Kai Ustaz!” Na furta ina d’an satar kallonsa “Kai ko gaskiya, next zuwan da zan yi dama ki tabbatar kin fito min a y’an matanki caras a bu’de min kuma jiki tunda ya halatta ko sau d’aya ne kaga matar da zaka aura ki saka min kaya mai kyau.. Kin ji ni ina ta surutu ban tabbatar ma ana so na ko a’a ba…. AYSHA d’ago ki kalleni…” na d’ago a hankali ba don zan iya kallon nasa ba, sai don bana son na masa gaddama. “Kina so na za ki aure ni?” K’asa na yi da kai na in furta “Kana da mata?” Wata irin dariya ya yi da har sai da ya bayyana wasu points a gefen hancinsa. Ya furta “Kishi kumallon mata, kada dai ace AYSHA na da kishi?” Girgiza kai na yi “Ni ba ni da kishi, ni dai kawai ba zan auri mai mata ba..” Dariya ya yi sosai ya furta “Mhmn, ba amsa kenan, don wannan amsar bata cika gamsashshiya ba.” In a serious tone ya furta “I have a wife AYSHA da yara biyar…” wani irin waro ido na yi, k’walla na taruwa a k’asan idon nawa. Na girgiza kai. Ustaz kuwa idanunsa ya kafa min yana sakin murmushi k’asa k’asa. “Gaskiya na gaya miki, ki je ki yi shawara zan dawo jibi idan kin amince sai ki gaya min. Ko ta cikin waya ne.” Ya fa’da yana ajiye min wani kwali a cikin leda “Idan kin kunna akwai layi a ciki, na yi setting komai, ban amince da Instagram da duk wasu tarkacen Social media ba sai whatsapp kawai. I repeat Whatsapp only AYSHA…. Anjima zan kira na san a waya dai may be zaki amsa min sosai ba za’a dinga min maganar bebaye ba, mai rowar murya kawai…” Murmushi kawai na saki ha’de da fa’din “Na gode.” Cikin sanyin murya don kam Ustaz ya sanyayar da ita, tunda ya gaya min yana da mata. “Numberta kawai, Sai Siblings d’inki da parents ban da su bana son ganin any number.” Na ce “Toh!” Ya ‘dan kalli table ya tab’e baki “Budurwar k’auye ba ruwa ba lemo haka ake saukar saurayi ko?” Da sauri na girgiza kai ina y’ar dariya ka’dan. Na lura Ustaz sam bai da bak’unta. Komansa free yake. “Ki gaida kowa na cikin gida sai na dawo.” Ya fa’da yana ficewa daga d’akin. Sakin ajiyar zuciya na yi, ina lumshe ido. A wata duniya na dinga ji na, mai girman gaske. Da na san Ustaz ne yazo wajena ba ta yarda za’a yi na zubar da hawaye na a banza, tunda Burina ne dama burina zuwan wannan ranar. Abu guda ke fa’dar min da gaba Mami na! Ban san yarda zata fuskanci lamarin ba. Ni kam ina son Ustaz kuma na shirya Aurensa koda Ba Abba ne ya ce ba, balle shi ya ce.

Na ‘d’au kwalin wayar, ba kowa a tsakargida shiru gidan, dama Mami ce mai son hirar tsakargida da alama tunda bata da sukuni a zuciyar ta sai kowa ma ya kama kansa. Umma dai itace da girki na san tana wajen Abba. Step na fara hawa ina jin tsoro na yana sake yawaita. A hankali na tura k’ofar parlorn Mami, Kamar yarda na zata tana zaune tana kallon tashar Arewa24. Ta amsa sallamar ba tare da ta kalleni ba. Jikina a sanyaye na zauna a gefenta ina nazarin fuskarta na ji ta furta “Yaya kika ganshi? Wani dattijo ko? Mai gemu buya-buya tunda na ji ance Ustaz ne, yanzu haka ma k’azami ne..” Kallon Mami ina mamakin kalamanta, tabbas bata san Ustaz ba, da bata yi wani furucin ba, ba mamaki da zata gan shi taga kamanninsa itama ta so ya zama surikinta.. ina cikin ko a cikin maza millions za’a tsame Ustazu na a matsayin wanda yafi kowa kyau da tsafta.. Mami ta zaci in dai ance mutum Ustaz ne sai ya zama wani mara fasali. Ai yanzu Ustazai akwai d’aukan wanka da kwalliya sosai ma. Ban san me yasa ba sai na ji wasu siraran hawaye suna zubo min, wanda na san ba hawayen komai ba ne sai na zallar farin cikin cikar burina, tunda na ji sanyinsu har k’asan raina da cikin jikina..

A zaton Mami kukan bak’in ciki nake. Ta mik’e tsam daga kujerar ta ta dawo inda nake ha’de da dafa ni, ta furta. “Daina zubar da hawayenki a banza Aysha, in dai ina numfashi babu mai miki wannan auren tozarcin ko me ma zai faru ya faru… wani irin tsalle zuciyata ta buga, na ‘dago da sauri ina kallonta na furta “Mami, kada ki ce haka, Mu yi hak’uri kawai mu yarda da k’addara, Saboda ba mu san abinda Allah ya b’oye ba….”

“Rufe min baki Aysha…” Ta furta cikin wani irin zafin rai, da har huci take fesar wa. “Kada kice min zuciyarki har ta amince da wannan mutumin? Wato har kin ji a zuciyarki zaki iya aurensa? So kike ki ba’da min k’asa a ido? Duk da yak’i da hak’ilon da nake na nema miki y’anci a wajen iyayenki da ba su san mutuncin ki ba? To bu’de kunnenki ki ji da kyau, ko son sa zai kasheki ba zaki auresa ba…” Ta fa’da tana fancakalar da hannu na ta mik’e a zuciye ta shige d’aki. Shiru na yi zuciyata na harbawa na zubawa hanyar da ta bi ido. Ina mamakin duk furucinta. “Anya Mami tana cikin hankalinta kuwa?” Ras take” zuciyata ta bani amsa tsabar son boko ne da ak’idar bokon yaja mata haka.

Na d’an tab’e baki ba ina tunanin tabbas za’a samu matsala, don yarda nake son Ustaz bana jin wani hargitsin Mami zai saka na rabu da shi. Na shige d’akina. Ina bu’de ledar da ya ajiye min. Waya ce mai kyau IPhone 13 sai turaruka masu kyau guda biyu. Na shinshina turaren d’aya irin turarensa ne sak, a jikinsa ya rubuta “For Night only…” Murmushi na saki, ina tunanin sabida me zai ce sai dare kawai zan saka.. Na san Abba ya kwanta, don haka sai da safe zan kai masa wayar ya gani, idan ya amince sai na cigaba da rik’ewa idan kuma bai amince ba sai na mayar wa Ustaz.

Wanka na yi na saka sleeping dress sannan na fesa turaren da Ustaz ya sanar da ni sai dare kawai zan dinga sakawa. Sai da na kwanta sannan na gane dalilinsa na cewa For Night d’in. Don k’amshin sosai ya dinga tuno min da Ustazun. Na dinga sakin murmushi ni ka’dai. Kafin na ji wayar na vibrating. Idona na kai kan screen d’in wayar sai ga hoton Ustaz a ciki yana sakin murmushi an rubuta “Farhatul K’alb..” (Farin cikin zuciya) ina sallama ya saki ajiyar zuciya kafin ya amsa ya furta “murya mai da’di…” shiru na yi “Ba gaisuwa AYSHA? Me ya hanaki bacci k’arfe d’ayan dare?” Da zan iya cewa zan yi Tunaninka. Sai dai na ji na kasa na furta “Bakomai…” “Gaskiya ban yarda ba.. ni na san me ya hanaki barci..” “To menene?” Na fa’da cikin sanyin murya. “Cewa zaki yi To menene Habibeey?” Ya fa’da yana koyan muryar y’an mata dariya ya bani sosai na dinga yi kuwa ba k’akkautawa “Tunanin D’an Ugly saurayinki ko?” Na ware ido.. “Ba zaki amsa ba. Zaki iya vedio call please.” Da sauri na girgiza kai ina cije leb’ena na furta “A’a” “Me yasa?” Duban jikina na yi na ce “Ni dai bana so…” “Mhmn..” Ya ce cikin wata irin murya “Allah ya baki hak’uri, amma ki saka Hijab mana mu yi, wallahi son ganin ki kawai nake ko zan iya barci, kin bi kin rufe idona ke kawai nake gani.” “Shikkenan ma, kaga ba sai ka ganni ba kenan…” Dariya ya saki ya ce “Aysha!” Sunan da na ji ya tsarga har k’aramin yatsan k’afata “Kin san sunana?” “Uhm” na ce masa. “Okay fa’da na ji please, ni dage sai fa’dar naki nake kamar ni na ra’da miki. Ya sunana?” “Ustaz!” Na fa’da cikin muryar da ni kaina ban san na iya ta ba. Shiru ya yi tsawon seconds Hamsin har na zata ko ya kashe ne. Na furta “Hello..” ya saki ajiyar zuciya yana firta “Ina jin ki Aysha… kin tafi da numfashi na ne, Allah ya baki wata irin murya da zan yi kishin wasu mazan su gaba da jinta in dai za su yi feeling abinda nake ji yanzu… Ba zan iya ba, ki tashi ki yi sallah yanzu ki rok’a mana dukkan alheran da suke cikin neman auren nan kin ji?” “Toh” na amsa “Kina sallahr ai ko? Ko ba kya sallar dare?” “Ina yi.” To maza ki yi sallahrki zan kira da safe na ji feedback akan maganarmu.” Ya fa’da yana kashe wayar bayan ya furta “I love you…” cikin k’asa da murya. Sai da na ware ido ina tunanin Anya kuwa Ustaz ne.. ashe Ustazan nan suma ba baya ba wajen bawa soyayya hakkinta? In dai kuwa haka ne tabbas na dace.. Sallahr na yi na dinga rok’on Allah musamman akan Mami da niyyar Allah ya karkato mata da zuciyarta ta amince ta kuma so auren nan.

Da sassafe na tashi, cikin matuk’ar karsashi da wani farin ciki da ya kasa b’oyuwa a fuskata.
Idona kawai zaka kalla ka karanta abinda yake k’asan raina na zallar farin ciki. Kasancewar lahadi ce na fita Parlorn Abba inda anan ake zama duk ranar lahadi a karya.
Chapter 10 · 0% Book details