← Book details Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 30

Sashe 16

Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kashegari na lallab’a na yi shirin makaranta, don kawai na zame na je gidan su Mami na. K’arfin hali kawai nake don ko barcin kirki ban samu na yi ba. Don ma a ‘d’akin Umma nake kwana tunda Mami bata gidan. Ganin juye juyen da nake ya yi yawa, hakan yasa ina ji Umma ta saka baki ta kira suna na. “Mik’e AYSHA ki shiga toilet ki yi alwala ki yi sallolin nafila tunda barcin ya gagara. Na mik’e kuwa jikina a sanyaye na aikata abinda ta ce d’in, sai naga na samu sauk’in abinda nake ji a cikin raina.

A kitchen na sameta tana dama kunun gya’da. Na furta “Umma zan tafi.” Ta ‘dago tana kallona kafin ta mik’o min cup d’in hannunta mai cike da kunun gya’da mai zafin gaske. “Shanye shi tas kafin ki tafi, kina nan kin sakawa kan ki k’wazzaba duk kin bi kin rame.” Ban mata musu ba na sha kunun don ni da kaina ina ji a jikina na matuk’ar ramewa don har kamar iska zata kwasheni.

Ina shiga motar na ce da Baba Driver “Gidan su Mami zaka kai ni ba makaranta ba Baba.” Ya juyo yana kallona ya ce “Yau ba zaki makarantar ba Ayshatu?” Na d’aga masa kai, sai bai ce komai ba ya ja mota ya nufi da ni court road don anan gidan su Mamin yake.

Shiru gidan har na shiga cikin harabar gidan ba kowa, don gidan sam ba yara sai Maman su Mamin duk an musu aure mazan gidan kuma wasu suna k’asashen waje karatu. Na shiga Parlorn gidan da yake k’asa inda anan step d’in benen yake.

Mama ta dubeni tana bu’de baki. “Yarinyar Mami ce a gidan nan da safe haka, ina makarantar?” D’an murmushi na saki ban yi mata wasan da na saba mata ba ni jika da kaka. Na zauna a gefenta ina furta “Mama ina kwana?” Ba zan amsa ba Aysha, kin ga yarda kika dawo kuwa? Wace irin masifa ce kuka jefa kan ku haka ke da Uwar taki, ita ba nutsuwa ke ba nutsuwa, ku wato ba zaku yarda da hukuncin Allah ba kenan, dole sai kun ja da mahaifinki alhali dukkanku a k’ark’ashinsa kuke, ai ni ya min daidai wallahi wani Sokon Uba ne shi da alheri na binsa zai saka k’afa ya doke saboda wani bokon banza da wofi… ai idan nice a ranar da aka zo neman auren ma zan d’aura auren kowa ma bai ji ba bai gani ba. Mutum kamar Ustaz Ahmad da yake burge kowa, a cikin lafazin karatunsa zaka gane mutum ne mai nagarta…” idanuna ne suka kawo k’walla na yi shiru kawai ina jin zancenta. Ina ma y’arta zata zauna ta gane abinda Maman take fa’da. Amma Ai mun bari gini tun ran Zane, ni na san Ustaz ya yi zuciya ya bar ni daga yanayin kallon da ya min jiya. Ai shi ba k’aramin mutum bane da zai zauna ina masa walagigi da hankali. “Tashi ki je can wajen Uwarki, kada ki min kuka anan ba zan wani lallasheki ba, don ni bana bayan rashing gaskiya..” Na
Mik’e kawai ina harha’da hanya na hau saman don na san a can zan samu Mami har yanzu yaran gidan kowa da d’akinsa.

Na tura k’ofar na shiga, Mami tana kwance a saman carpet idanunta a lumshe kamar mai barci. Ta bu’de ido tana kallo na. Da sauri na isa wajenta, mik’ewa ta yi zaune tana bu’de min hannunta alamar na shiga. Na kuwa shiga ta Mayar ta rufe i ruf tana sakin ajiyar zuciya. “I missed you Mami na.” Ta lumshe ido tana furta “I mish you too Baby na.. Ina school d’in baki tafi ba kika biyo nan.” Hawaye na fara yi. Ta saka yatsa tana wasa da hawayen fuskata tana sakin murmushi a hankali ta kai min sumbata a gefen k’unci. “No more crying Baby na..” “Zaki koma gidan? Ni na yarda ba zan aure shi ba.” Ta saki murmushi ta ja hannuna ta matse cikin nata ta furta “Zan koma Aysha, don ba zan iya rayuwa ba tare da Baby na ba..” Murna na fara yi ina jin abinda ya tsaya min a zuciyata yana tafiya. So nake na tambayeta ta amincewa alak’ata da Ustaz amma sai na ja baki na yi shiru don bana son b’acin ranta. Ina kallo ta shiga wanka ta fito ta shirya a gabana sannan ta zura hijab d’inta muka sauka k’asa. Mama bin mu ta dinga yi da kallo ganin yarda nake jan akwatin Mamin. Murmushi kawai ta furta “Lallai Fateema, yanzu ba wanda bai rarrashekiba aka dinga baki hak’uri kika k’i komawa gidan mijinki sai yanzu da Aysha ta zo? Ai shikkenan Allah ya kiyaye hanya..” Mami murmusawa kawai ta yi muka fice daga gidan. Muka shiga cikin motar Mamin sai gida.

Umma tana tsakargida tana ware kayan miya da naman da za’a saka a freezer ta ji sallamar mu. Da mamaki ta ‘dago tana kallonmu. Mami murmushi ta saki tana furta “Kallon fa?” Umma ta ce “Ba dole na kalleki ba Fateema, yanzu ba wanda bai je biko ba har ni kishiya, amma kika k’i dawowa Mahaifinki ma ba yarda bai yi da ke ba, shima kika ja kika kafe sai yanzu kawai naga ficilar yarinyar ta dawo da ke..” Mami
Murmushi ta saki. Ta ce “Hakan zai nuna muku mahimmacin ta gareni a rayuwa ta…” Umma ta ce “Ba shakka, To Allah ya kyauta na gaba…”

Daga ranar da na furta masa ba zan aure shi ba, bai sake nemana ba har tsawon kwanaki biyar. Zuwa lokacin duk na fige na lalace sai kace wacce ta yi watanni tana ciwo. Ba wanda ya sake bi ta kaina balle a min zancen Ustaz.

Da yamma sai ga Yaya Muhammad ya shigo gidan muna tsakargida duk muna aiki. Ya d’an dubi Mami yana sosa kai ya furta “Hajiya Mami, Aron Aysha zaki bani, Khadija na fama da laulayi ni kuma tafiya kaduna ta kama ni zan kwana biyu a can…” Mami ta masa wani kallo kafin ta furta “Muhammad bana son jaye jayen magana, ita ina y’an gidansu ba za’a kai mata su ba, sai Aysha? AYSHA ce zata je ta mata wahalar laulayin kenan? To ba sai yiwu ba ka samar mata y’ar aiki idan ma bata da y’an uwan da zasu zauna mata.” Muhammad ya d’an rusuna, duk da ba wani girmansa Mami ta yi ba, bai fi 2 yrs ta bashi ba, amma yana girmamata a matsayinta na matar ubansa. “Ki taimaka, ko don nan gaba idan Aysha ta yi aure bata da y’an uwa mata itama fa y’an uwan Mijin ne zasu kula da ita.” Mami ta girgiza kai “Wallahi don dai kai ne, amma da Umar ne Allah ba zata gidansa ba..” Dariya Muhammad ya yi don ya san Mami da Umar sam basa shiri haka ma Usman. Ya dinga dariya yana kallona ya furta “Ke d’ebo kayan da zasu miki kwana biyar, ki yi sauri ina mota ina jiranki…”

Na mik’e na hau sama, a raina sam bana son zuwa saboda ina yawan fita da yamma naga ko zan ga Ustaz amma bana ganinsa. Na shirya kaya na na bi Yaya Muhammad gidansa.

A parlor na samu Anty Khadija daga yanayinta na hango tabbas laulayin take. Gaisheta na yi ta amsa tana murmushi na mata sannu. Da kanta ta raka ni ‘d’akin da zan zauna. Hijab d’ina na cire na fito parlorn ba mayafi a jikina sai hula. Tas na gyara gidan don ya yi k’ura ka’dan. Kafin na shiga kitchen na tuk’a musu tuwon semovita da Yaya Muhammad ya ce shi ka’dai take iya ci.
Chapter 16 · 0% Book details