← Book details Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 30

Sashe 23

Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri na janye hannun nawa ganin yarda mutane suka fara fitowa daga k’ofofi daban daban an ware ki’dan larabawa suka zagaye mu da Ustaz. Sai fa’dar Marhababuki lale suke. Kana ganinsu kaga jinsin larabawa don farare ne k’al da su. Ustaz d’an murmushi ya saki ya yi saurin zamewa ya bar ni da su. Matar mai kama da Ustaz kwabo da kwabo ita ta k’araso inda nake ta kama hannuna tana ha’dani da jikinsa tana fa’din “Marhababuki Ibnateey…” Wani irin sahihin k’amshi ne kawai yake fita ko ta ina a gidan. Suka ja hannuna zuwa cikin gidan. Kaina a k’asa k’irjina sai bugu yake, amma matar bata cika hannuna ba. Sai da muka isa cikin babban parlorn gidan. Tabbas gidan su Ustaz ba k’arya ya ha’du kana ganinsa ka san sun ci sun tada kai da naira, babu gami sam tsakaninsa da namu gidan. A kan kujera ta zaunar da ni, amma sai na zame na zauna a k’asa. Ina gaishesu a kunyace.

Kishiya ta ce tazo kusa da ni ta zauna. Tana kama hannuna na ji kamar ta zubar garwashin wuta a hannun, da sauri na janye sai na ji ta yi dariya ta furta “Am not his wife, he was just joking… ni k’anwarsa ce the only Sis da yake da ita….” Innalillahi na furta a hankali kunyar rashin mutuncin da na mata nake ji, dana sani ya shige ni sosai. Ta yi dariya sosai ta fara bawa mutanen parlorn labarin acting d’in da nake idan ta ce musu ni matar Ahmad ce. A raina na ji ba zan k’yale Ustaz ba sai na rama, wannan ai ba wasa ba ne. Dariya sosai mutanen parlorn suka fara. Mommy ce ta ce “Ahmad ba zai miki kishiya ba, ke ka’dai kin ishesa In sha Allah, Son da Ahmad yake miki ba a kwatancensa Allah ya baku zaman lafiya da zuri’a d’ayyiba.” Ta juya tana kallon k’ofa. Ta furta “Ibnateey maza kirawo min shi, a yi addu’a kafin a fara cin abinci..” Da sauri kuwa naga Habibteey ta mik’e ta nufi inda zata kira shi.

Sai ga shi ya fito cikin wata jallabiya brown color yana shigowa da ni ya fara ha’da ido. Na d’an turo bakina ina masa hararar gefen ido, kafin na sake jan mayafi na rufe fuskata. “Ahmad kazo ka ciyar da matarka kamar yarda al’adarmu take at first day of marriage.” Wata mai kama da Mommyn ta fa’da tana sake janyo Ahmad zuwa inda nake. Zuciyata kawai bugu take ina tunanin ta yaya zai ciyar da ni? Daf da ni ta zaunar da shi har jikina yana ha’duwa da nasa. Ta kawo masa kayan abincin gabansa. Da kansa ya yi serving d’inmu. Kafin ya ‘dago yana kallon auntyn nasa, ta ‘d’aga masa kai “Oya ka fara mana, ina jira zan yi pic..” Hannunsa ya saka ya ‘d’aga mayafi na. Da sauri na runtse ido, ganin ya kai dabino guda baki na. A hankali ya furta bu’de bakin…” “Amma ka san ba haka muke ba ko?” Anty ta fa’da ranta a b’ace. Ina kallo ya d’an yi dariya, sai kuma ya mayar da dabinon bakinsa ya gutsira ka’dan ya tauna ban yi auneba na ji bakinsa cikin nawa yana zuba min taunannen dabinon. Jikina ne ya fara rawa da sauri na rik’e numfashina da yake son d’aukewa ganin still YUstaz bai cire bakinsa a cikin nawa ba sai juya harshensa yake cikin wani salo da lumsassun ido, sai da ya tabbatar na ha’diye sannan ya janye yana ‘dan murmushi. Ihu da Kabbara suke kawai a gidan. Aka dinga mana hotuna ni kuwa duk kunya ta saka jin jikina wani iri na sunkuyar da kaina kawai na kasa ha’da ido da kowa. Anty ce ta ce Khadija ta tafi da ni d’akinta sai a kai min abincin can tunda na kasa sakewa da su, su al’ada garinsu ce haka, ba abin kunya ba ce, rana ce mai mahimmanci a wajensu da ake wa saurayin da bai tab’a aure ba, don a ga yanayin da zai shiga a yi dariya idan an ga abinda zai yi a first deep kiss ‘d’insa. Ni dai tuni na bi bayan Khadija jikina na rawa muka isa ‘d’akinta.

Muna shiga ta janye mayafin fuskata tana dariya. “Bud’e fuskar Anty AYSHA na ganki da kyau, tunda dai nan daga ni sai ke..” Knocking muka ji. Khadeeja ta furta “Yes come in..” k’aninsu ne ya shigo yana d’an hararar Khadija ya furta “Mhmmn, I know kina nan kin saka ta a gaba da surutu kamar parrot…” ta wani waro ido tana furta “Ridwan am I play with you? Ni kake kira parrot iya get out from here…” Ya turo bakinsa ka’dan yana furta “Aiken Mommy ne, ta ce ki rakata part d’in Yaya Ahmad su ci abinci da shi tare…” Na wani irin waro ido, kamar na yi kuka nake kallon Khadija na ce “Ki gaya mata na k’oshi don Allah…” Khadija ta waro ido tana furta “Ban kai nan ba, idan ba so kike Ya Ahmad da Anty Danger su gididdiba ni ba..” tana jan hannuna amma na kasa ta shi. Sai kawai ta fita sai gata ta dawo da wacce na tabbatar ita suke cewa Anty Danger na ji ta ce “Anty Tasleem to gata nan, ki gaya mata da kan ki.” Murmushi ta saki tana jan hannuna ta furta “Ta so Inlaw, yau ranace mai muhimmanci ga duk mai son Ahmad, shima kuma yau rana ce da zai so ku kasance tare tunda dai ba yanzu za’a kai ki gidan sa ba. Muje ku ci abinci ku yi hira sosai.” A kunyace na mik’e na bi bayanta hannuna cikin nata, muka ratsa ta wata k’ofa, Khadija na bin mu a baya, sai da muka wuce wani fili mai kyau kafin mu dangana da wani d’an gini mai kyau duk da bai cika girma ba. Anty Danger ta saka hannu a k’ofar ta yi nocking sai ga shi kuwa ya bu’de ina ji Anty Danger ta furta “aka tabbatar ta ci ta k’oshi ka kuma bata gift mai tsadar gaske wanda ba zata manta ba, na san ka san me nake nufi ko?” Hannuna na ji cikin nasa kafin ya kalli Khadija ya furta “Ke bar nan..” Da sauri kuwa ta juya tana dariya ta furta “Su Ya.Ahmad da mata Ai sai Allah. Anty Danger ma ta juya ya ja hannuna zuwa cikin k’aramin parlorn mai masifar kyau na zata anan zamu tsaya sai naga ya shiga da ni wata k’ofa da ta kai mu ainahin wani babban bedroom d’insa… muna shiga naga ya jani jikinsa ya rungume sosai cikin wani irin sautin murya ya ra’da min “Bari na fara baki gift d’in da surikarki ta rok’a na baki…” k’ok’arin zame jikina nake Amma ina ji na yi kawai yana zame d’ankwalin kayana ya cusa hannunsa cikin gashin kaina a kunnena na ji yana furta “Alhamdulillah Eesh komanki is beautiful ina fatan cikinki yafi wajenki kyau….” Jikina rawa kawai yake shi kuma bai daina shinshina k’asan wuya na ba.. “AYSHA ina son ki sosai ke ce rayuwata ki amince min yau d’aya kawai….”

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ

NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 18.

𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️

Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

Arewabooks @nazeefah

https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ

Wattpad@Nazeefah381

08033748387.

★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 18.

‎Da sauri na kalleta kafin na girgiza kai na. Wasu hawaye na shirin zubo min, wanda bana komai ba ne sai na jin haushin tsanar da Mami na ta yiwa Ustaz, alhali shi yana sonta yana daraja ta, don kai tsaye zan iya cewa Ustaz kallon Uwa yake wa Mami. “Zaki amsa min, ko sai kin gama k’are min kallo? Na ce kin mik’a masa kanki ne?” Girgiza kaina na yi jin abinda Mamin ta ce. Sai naga ta saki wata ajiyar zuciya da har ta bayyana ta saman k’irjinta. Tana kallona ta furta “To wankan me kika yi? Ko da yake…” sai naga ta ‘dan cije leb’enta tana furta “Mhmn, ina ya kai ki bayan gidansu? Don naga da’dewar da kika yi ta yi yawa, kin saka na kasa barci fargaba ta d’aya kada ya mayar da ke cikakkiyar mace…•” K’asa na yi da kaina kurum. Na ce “Gidansu kawai ya kai ni, kuma na da’de ne saboda duk y’an uwansa suna gidan sun ‘dan ha’da Walima, wai su haka al’adarsu take, ranar da aka d’aura aure dole a yi Walima ta nuna godiya ga Allah…” Ta ‘dan tab’e baki. “Bayan walimar sai kuka zauna hira da mahaifiyarsa? A matsayinki na maras kunya ko?” Da sauri na girgiza kai na ce “Wallahi a’a Mameey, kawai dai ina zaune da sisters d’insa suna jana da hira…” na nuna mata kayan da suke kan gado na ce “Su suka bani.” Ko kallon kayan bata yi ba, ta fice da sauri daga ‘dakin tana furta “Ina ruwana da wasu kayansu, tunda dai bai kusanceki ba Ai shikkenan, ki gaya masa kuma fita an yi ta farko an yi k’arshe ba zai ya bu’dar miki da ido ba, ya zuba miki karatun da sam bana son ki fahimceshi a yanzu…” daga haka ta ja k’ofar da k’arfi ta bar ni da bu’dadden baki ina kallonta. Na saki ajiyar zuciya kafin na zura kayan sallah ta na tada sallahr isha’i da ban yi ba. Bayan na gama tunanin irin rigimar Mami, tabbas idan ka fahimci halinta tana da da’din zama amma kafin ka fuskanceta zaka saka ta a b’angaren mutane masu bau’dadden ra’ayi.
Chapter 23 · 0% Book details