← Book details Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 30

Sashe 18

Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kashegari da k’yar na tashi na hau gyaran gidan don duk kawai na kawar da abinda nake ji a raina. Da yamma sai ga Mami na tazo gidan. Da sallama ta shigo na yi saurin ‘d’aga kai ina kallonta. Zama ta yi tana tana jikinta ta furta “Ke Baby!
What happened to you na ganki so pale haka?” Daurewa na yi ban sakar mata hawayen da suke son zubo min na ce mata bakomai…” Sai sannan ta amsa gaisuwar da Khadija ta mata. Tana fa’din “Ina Muhammad ‘din?” Anty Khadija ta ce “Ai bai dawo ba..” Gani nayi Mami ta girgiza kai ta ce “Yaushe ya ce zai dawo daga Kadunan?” Khadija ta ce “May be gobe.” Ni mamaki nake yi don dai Yaya Muhd yana nan a cikin gidan nan me yasa Anty Khadija zata ce bata nan… Mami ta ‘dan ja tsaki ta furta “D’an bamu waje Khadija zan yi magana da ita…” Kamar jira take tayi saurin mik’ewa ta fice. Mami ta saki ajiyar zuciya tana jawo wata leda a jakarta. “Dama yana dawowa ki dawo gida, a goben, kin ji na gaya miki.” Na ‘daga kaina ta zaro wata roba mai cike da wani abu kamar rubutu tana furta “Bu’de ki shanye, ban yarda da lamarin wancan mutumin ba..” Na karb’a hannuna na rawa na bu’de na sha duk da sam hankalina ya kasa yarda da rubutun, abu ne da na sani a gidan mu Abba d’an izala ne shi yasa baa ta’ammali da rubutu, zan iya cewa tun tashi na ma ban tab’a ganin rubutu a gidan ba. Yana dai yin tofi. Ina shanyewa ta saki ajiyar zuciya sannan ta ciro wani turare a jakarta ta shafa min. Turaren sam ba shi da da’din k’amshi. Daga haka ta mik’e bayan ta bani chocolates da ta siyo min da biscuit da yawa ta ta ce “Zan tafi AYSHA na gaya miki ki taho yana dawowa gobe..” Na ‘daga kaina ko sallama bata yi da Khadija ba ta fice.

Sai ga Yaya Muhd ya fito daga bedroom fuskarsa a ha’de ya zuba min ido yana kallona. “Me ta baki kika sha?” Na waro ido ina furta “Bakomai fa…” “Bakomai d’in Uwaki, ba ina kallo ta baki abu roba kika shanye ba…” ya furta yana tsare ni da ido.
Yana bu’de k’ofofin hancinsa da alama k’amshin turaren yake shak’a. “Wannan wani irin turare ne kamar na y’an bori? Tashi kije ki yi wanka don Ubanki shashasha da bata san ciwon kanta ba…” Yaya Muhd ya furta a zafafe kamar ya mangare ni. Da sauri na shige d’aki ina turo bakina alamar na ji haushin abinda ya yi min ‘din. Ina ji ya zabga tsaki.

Da na yi wankan, zama na na yi a ‘d’aki fuskata a ha’de don na ji zafin abinda ya yi min. Sai gashi ya shigo d’akin yana kallona ya furta tashi magana zamu yi AYSHA….” Na mik’e na zauna still fuskata a ha’de. “Haushi kike ji ko? Baki da hankali yarinya har yanzu baki san me duniya take ciki ba, ina sane na kawoki nan don ban yarda da wannan matar ba…” Wani irin waro ido na yi na furta “Mamin nawa?” Harara ya zuba min,
Yana fa’din “Saura kuma don Ubanki ki je ki gaya mata, na ce ban yarda da ita ba, tunda da alama ta shanye miki zuciya har kina k’ok’arin gasa taki zuciyar saboda ki sanyaya tata, kan ki
Kika cuta ba wani ba na tabbatar ko gama karatun kika yi ba zaki samu kamar Ustaz Ahmad ba, shi na daban ne ina gaya miki, gashi nan kin cuci kanki zai yi aure ya bar ki, saboda ko farantawa wata k’atuwa rai shi kuma Abba da hakkin ki masa biyayya yake kanki kin bak’anta masa nasa ran a matsayinsa na mahaifinki,
Kin nunawa duniya bai isa da ke ba. Ina sane na kawo ki nan amma nan ‘din ma sai da ta biyoki. To wallahi ki kiyaye kan ki na gaya miki bakomai zata sake baki ki yi amfani da shi ba. Ki ‘dau waya kuma ki kira Ustaz idan ya amince yazo gidan nan sai na tayaki bashi hak’uri, Allah yasa ya hak’ura ya aureki.” “Ameen” na furta ba tare da na san ameen ‘din ta fito ba. Ya Muhd ya bi ni da wani irin kallo kafin ya yi murmushi ya ce “Shashasha, kina so kina kai wa kasuwa..” Na sunkuyar da kai ina d’an dariya. Ya furta “Ki kira shi yanzu.” Ya fita daga d’akin.

Sai da na yi addu’a sosai sannan na kira shi, Ringing ta yi sosai kafin ya ‘d’aga. Cikin Husky Voice ‘d’insa ya ce “Assalamu Alaiki, K’anwata AYSHA ya aka yi?” Wani irin waro ido na yi raina ya b’aci da sunan da ya kira ni da shi. Wai k’anwata ina ma laifin Habibteeyn… da yake fa’da. Ba dai ji haushi ba na furta “Ina yini?” Sai da ya yi ‘dan jum sannan ya furta “Lafiya lau, Babyn Mamy me ya faru na ji muryarki so weak…” Hawaye na ji sun silalo min na yi k’ok’arin tsayar da su ina furta “Zaka zo yau please…” “Ina zan zo?” Ya furta a hankali cikin k’asa da murya “Gidan Ya Muhd please Ustaz…” Sai da ya ja fasali sosai sannan ya furta “Me Zan zo na yi? Ko kin shirya amincewa aurena ne?” Shiru na masa zuciyata na bugawa da sauri na ce “Ni dai kazo don Allah…” ya saki wata malalaciyar ajiyar zuciya. Yana fa’din. “Sai dai gobe yau a gidan su Habibteey zan sha ruwa..” wani irin wuntsilawa zuciyata ta yi don haka naja baki na tsuke ina hucin da na tabbatar yana jin sa ta cikin waya.. “Kada ki fashe, don naji fushin ya bayyana har ta numfashinki, zan zo Amma ina son a min irin funkaso da masar rannan ki saka man shanu a cikin miyar.” Ya furta a hankali. Wani farin ciki naji na ce “Ai baka ci abincin ran nan d’in ba, ta ya aka yi ka gani? Bayan baka bu’de ba…” Y’ar k’aramar dariya ya saki ya furta “Little girl, bayan kin gama kuka a sitroom na saka Drivernku ya ‘dauko min Warmers ‘din na tafi gida da su, ranar duka kowa a gidan mu sai da ya ci abincin AYSHA Momeey na ta mamakin iya girkin ki da murnar ki zama surikarta ashe ba zaki zama ba….” “Wa yace ba zan zama ba?” Na furta da sauri. Na ‘dan Jim ya yi bai ce komai ba, kamar ma ba zai ce ‘din ba sai kuma ya ce… “Ke kika zab’i rabuwarmu Aysha… Ga shi Yanzu it’s too late, koda yake sai nazo za mu yi magana, take care ki ha’da min zob’o bana son kunun aya…”Ina ji ya kashe wayar. Nima ajiye wayar na yi cikin sanyin jiki, ina runtse idona wasu zafafan hawaye suna zubo min..

Na dubi agogo naga akwai sauran lokacin da zan iya masa da funkaso, tunda sai a lokacin ma 3:30 ta yi. Da sauri na mik’e na isa kitchen ‘din Anty Khadija. “Alhamdulillah” na fa’da ganin duk abinda nake buk’ata akwai shi a kitchen d’in.
Nan da nan na fara shirin girki, don kam Alhamdulilah Umma da Mami sun hora ni da girke girke iri-iri, don haka duk inda na je basu da fargabar a bani girki. Sai shidda daidai na gama girkin. Gidan sai zuba k’amshi yake. Wanka kawai na yi na samu kaina da tsantsara kwalliya ta fitar hankali, wai duk don na kamo matar Ustaz a kyau. Amma still walainiyar fuskarta kawai nake gani. Don haka na saki tsaki na goge makeup ‘din tas hawaye na bin idona. Sanda aka yi sallah kuwa dabino kawai na samu na ci, don nima na yi azimin. Zaman dafi’an na yi akan sallaya. Ina ta lazimi da addu’ar Allah ya ‘dorani akan Ustazuna ya janye batun auren waccan yarinyar mai kama da zabiya, idan har ya amince ni na yarda ko kashegarin ranar ne a ‘daura min aure da shi. Daga baya zan san yarda na yi muka shirya da Mami.

Ina zaunen akan sallaya Ya. Muhd ya shigo, ‘Dan duba na ya yi sai kuma naga ya tab’e baki ya furta “Ki taso Malama, bak’onki ya zo.” D’aga kai na yi gabana na cigaba da matsanancin bugu. Na mik’e cikin mutuwar jiki da kasala. Dama na jera masa komai a sitroom ‘din.

Fuskata fayau ko kwalli babu na fita wajensa cikin shigar doguwar riga bak’a da na yi rolling da mayafinta. Jikina ruf ba inda ake gani sai fuskata don hatta k’afata a rufe take.
Chapter 18 · 0% Book details