← Book details Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 30

Sashe 26

Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani iri na ji kaina ya yi, na kasa d’aga ko ido na kalli Mami jin yarda nake jin wani irin d’aci a mak’ogwaro na, na tabbatar b’acin rai ne ya haddasa min haka. Bata jira jin abinda zan ce naga ta mik’e ta shige bedroom d’inta hakan ya tabbatar min bata buk’atar yarda ta ko rashin yarda, umarni ne kai tsaye ta bani da take tunanin tilas ne na bi shi. Hawaye naji suna zubo min masu d’imin gaske wanda suke narkar da duk wata damuwata da take k’asan zuciyata. Jikina a salub’e na shige d’aki, Ina ji lokaci ya yi da ya kamata na nunawa Mami nima y’ar Zamani ce, zan iya jurar komai banda rashin waya da Ustaz, ya Riga ya saba narkar da zuciyata da kalamai masu narkar da zuciya. Furucinta kam tamkar d’igar dalma ne cikin zuciyata gwara ta min komai banda hana ni jin muryar ustaz wallahi.

Bayan Isha, still Ustaz yazo gidan mu. Kamar yarda ya saba wannan karan ma da shi aka ci abincin dare. Ya kalleni bayan ya mik’e bai ji kunyar Abba ba balle su Mami ya furta “AYSHA, zo mota ki amshi sak’o.” Ta gefen ido nake kallon Mami da take zuba masa banzan kallo. Na mik’e jikina a salub’e na bi bayansa. Har ya shiga cikin mota. Hakan yasa na masa knocking glass. Bu’de motar ya yi ya furta “Shigo mu fara tsara yarda shirin bikin zai kasance, bana son hira a saman Mami, I can’t feel comfortable…” Na shiga Motar jikina a sanyaye. Ya janyo paper da biro ya mik’o min. “Lissafo min abinda duk kike so a yi a bikin, da duk abinda za’a kashe.” Ya furta yana kallona. Kafin ya d’an tab’e baki ya ce “Why are you so quiet yau ne? Ko har kin fara tunanin aure ne?” Lumshe idona na yi ina girgiza kai. Na furta “Bakomai fa, kawai stress d’in exams ne yake tambaya ta.” Ya girgiza kai yana jan hab’ata ya furta “Oh I see, am so sorry dana sani ban zo yau ba. Jeki gida zan shigo gobe ko jibi, ina hoping by that time kin wartsake stress mu samu mu shirya bikin sosai, duk da bana son event da za’a ha’da maza da mata please ko hoto mace nake so.” Na d’aga kai. Ya ja hannuna ya yi kissing kafin ya mik’a min ledar hannunsa. Mai kyan gaske tun kafin na bu’de na san turare ne a ciki saboda wani k’amshi na fitar hankali da naji yana fita a ciki. “Sweet dream…” Ya furta a hankali cikin
Wata husky voice mai dashewa. Na amsa ta hanyar d’aga kai. Na fita daga mota.

Sanda na shiga gida duk sun watse daga tsakargida, na hau saman Mami bayan na lek’a na yiwa Umma sallama. Mamin bata parlor na shiga d’akina.

Kyaututtukan da na samu na dinga bu’dewa ina binsu da kallo. Sai daga k’arshe na bu’de ledar Ustaz wani rantsatstsen turarena da charbi da sallaya da aka saka sunana a jiki da haruffan larabci “Zaujaty Ayshatu…” Murmushi na yi ina rungume d’an zoben gold d’in a k’irjina bayan na fesa turaren mai k’amshin na Ustaz sak sai dai shi wannan na mata ne k’amshin bai kai na Ustaz k’arfi ba. Lumshe idona na yi. Sai jin tafi na yi a kai na. Da sauri na ware idona ganin Mami a tsaye idonta a kaina. Ta furta “Weldone Aysha, kin kuma burge ni.” A daburce na furta “Mami me na yi?”

Ta tako zuwa inda nake, ta saka k’afarta d’aya ta tokare a saman gado tana kallona ta furta “Me kuwa kika yi AYSHA? Ba abinda kika yi illa kina so ki nuna min ke ma kin girma. Ahmad ya fara shayar da ke da’di da zumar da ke cikin aure, tunda ga shi har kin san ki rungume kyautar sa a jikinsa, alamu ya nuna kin fara sanin soyayya kin kuna san menene sha’awa, tabbas lokaci ya zo…” Ta fa’da tana lasar leb’enta “Uban me kika tuno da yasa ki lumshe ido da murmushi? Kin hango yarda yake rungumeki ko? Ke a tunaninki wai na amince da aurenki ne? Ko ka’dan har yanzu zuciyata bata so ina kuma adawa da haka. Na k’i jinin tarayyarki da wannan mutumin da yazo ya wargaza min duk wani tanadi na a kan ki….

Sak na yi ina jin furucin Mamin kamar d’igar dalma a cikin k’irjina. Ji nake kamar ana soya zuciyata saboda tsananin hucin da nake ji a k’asan raina.

“Mik’o min turaren.” Ta yi furucin cikin b’acin rai. Na saka hannu na mik’a mata turaren. Ta fice da shi tana furta “Kin bar amfani da duk wani abu da zai baki, musamman turare waya sani ma ko asiri ya miki a cikinsa. Shegen mutum mai azababben naci..” Ta gama zaginsa ta fice daga d’akin sai sannan naji wani kuka mai tafe da takaici ya zo min, ba shiri na saka kukan kuwa sosai. Raina ya b’aci sosai don haka bayan na yi wanka na shirya nan je ‘dakin nata ba kamar yarda ta min umarni na yi zama na a ‘d’aki.

Wajen sha biyun dare ta shigo d’akin cikin shigar wasu silk kayan barci sai baza k’amshin gabbasa take. Ina kwancen ta zauna a gefen gadon. Da sauri na lumshe idona don ko ganin Mamin naji bana son yi. Sunkuyo da kanta ta yi saman fuskata ta bani kyakykyawan kiss a gefen kumatu. A kunne ta ra’da min “Tashi Babyn Mameey, don’t tell me fushi kike da ni, na san dai idonki biyu.” K’in motsa wa na yi. “Ba zaki tashi ba?” Ta sake furucin a hankali sai ji na yi kawai ta burkito ni jikinta a hankali ta saka hannunta a gefen cikina ta min cakulkuli da sauri na bu’de idon ina d’an ja jikina ba furta “Kai Mammy, am not that young fa…” Sake janyo ni ta yi jikinta tana ha’da fuskata da tata ta furta “You are still my little Aysha, har yanzu kallon Babyn Mameey nake miki. Sau tari raina ne yake b’aci bana son kusancinki da Ustaz wallahi ina jin haushin hakan sosai a raina. A yanzu ba zan k’i ki auri wani ba ki bar Ustaz ba don komai ba sai don na san zai yi tsauri zai kuma takura miki zamantowarsa Malami, ba zai bari ki mori rayuwarki ba, balle….” Sai naga ta ciji leb’en bakinta na k’asa ta yi shiru bata k’arasa ba. Ta d’an girgiza kai sai naga ta ja pillow kawai ta kwanta ta furta “A dole za’a raba mu abinda bana so, ba yarda zan yi ne, shi yasa nake so mu dinga kwana tare ina jin ki kusa da ni, don na san wata rana ba zan samu damar hakan ba….” Kafin na yi wani yunk’uri naji Mami ta kwanta daf da ni sosai tana sakin ajiyar zuciya… ni dai a ‘darare na yi barci a ranar da mamakin wasu daga halayyar Mamin…

Bayan kwana biyu da faruwar hakan aka ce za’a kawo lefe don haka ranar da wuri na shirya duk raina ba da’di musamman takura ni da Mami take yi na kwana a d’akina ko nata ko itace da girki sau tari sai ta dawo don kawai ta hanani waya da Ustaz. Waya kam sai a sace nake yi da shi.

K’asa na sauka cikin shigar doguwar Rigar abaya da na na’de kaina da mayafinta, na saka nik’ab kuma. Mami da Umma na gani a kitchen sai masu aikin mu suna ta hidimar ha’da abubuwan da za’a tarbi bak’i da su. Bayan gaishesu Umma naga ta zuba min ido kafin ta juya wajen Mami ta ce “Fateemah, wani abu ke damun y’ar taki naga tayi wata Uban rama? Ko dai duk tunanin auren ne?”
Mami ta d’an tab’e baki tana kallon Umma ta furta “Me kike tsammani daga yarinya kamarta da za’a mata aure a k’ananun shekaru, ba dole ta yi tunani ba tunda ta san abinda zata tarar gidan Mijin ba mai sauk’i ba ne…” Umma d’auke kanta ta yi tana furta “Allah ya kyauta, aure ne fa ba rayuwar azaba ba, menene na sakawa kai tunanin? Sanda aka yi aurena shekaru sha biyar gareni kuma ba abinda ya same ni, ku san dai na yi gaskiya ko Sabaya ki fara d’irka mata gaskiya… don ramar ta yi yawa.”

Mami ta tab’e baki ta furta “Idan taje gidan Mijin, ta fara samun abinda kuke so ta samu Ai zata ciko. Zo ki wuce AYSHA kafin mutane su zo su tarar da ke, ki gaida Aseeyar sai kuma yamma zaki dawo. Driver na nan a waje ya sauke ki.” Na d’aga kaina ina fita daga kitchen d’in. Bayan na sake kallon Umma da ta zubo min ido…

A waje na tarar da Asma don tare zamu tafi. Driver ya taso don ya kai mu, na girgiza masa kaina “Bar shi ma Baba, Ustaz zai kai mu, amma don Allah kada ka gayawa Mami na.” Murmushi ya yi ya d’aga kai jin abinda na ce. Da sauri na ja hannun Asma muka fice don Ustaz ya isheni da kiran waya. Muna isa kuwa ya wurga min harara gaisuwata ma bai amsa ba sai ta Asma. Ban wani damu ba don na san laifukan da na yiwa Ustaz a lokutan nan ba zasu lissafu ba. A hanya Asma ta masa zancen zamu je fitar da anko. Ji nayi yana furta “Waye zai je kasuwar? Ba dai AYSHA ba wallahi gwara na rasa miliyoyin naira da na barta ta shiga kasuwa ku fa’di colorn da kuke so da adadin ku zan saka a kawo muku.” Asma murmushi ta yi ta kuma furta “Mun gode Allah ya k’ara arziki.”
Chapter 26 · 0% Book details