← Book details Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 30

Sashe 25

Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

Arewabooks @nazeefah

https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ

Wattpad@Nazeefah381

08033748387.

★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 17.


Jikina na rawa na kauce fuskata daga sumbatar da yake kai min. “Ustaz shine ka min k’arya?” Na fa’da ina janye jikina daga nasa na zauna a kan kujera. Zaman dirshan ya yi a gabana ya zuba hannunsa a kan cinyata yana kallona cikin wani yanayi ya furta “AYSHA k’arya kuma? K’aryar me?”
Magana yake cikin wata irin murya da na kasa tantance a wani mahalli zan sakata.
“Kace min Khadija matarka ce.” Na fa’da ina yin k’asa da idona don bana jin zan iya jure wannan kallon da yake min. Wani murmushi ya saki da har ina iya juyo sautinsa da numfashin da ya sakar min ya ratsa fuskata. Yana dariyar ya furta “D’ago ki kalleni…” na k’i d’agowar da ba zan jure ba. Hannuna ya kama ya matse cikin nasa. A hankali ya furta “Ranar da kika ce ba kya so na, kin fasa aurena hankalina tashe na taho gida. Ni da kaina na tabbatar ikon Allah ne kawai ya kawo ni gida, Saboda tashin hankalin da zuciyata take ciki.

Sanda na isa gida ko ciki ban shiga ba kamar yarda na saba. Na shiga part d’ina na zauna hankalina a tashe. Duk na ji duniyar bata min da’di. Ashe Mommy taga shigowata ta camera ta aiko Khadija taga ko lafiya ban shigo ba kamar yarda na saba. Yanayin da Habibteey ta ganni ne ya sata zubewa cikin tashin hankali a gabana tana kama hannuna ta furta “Subhanallah Ya Ahmad lafiya kuwa?” Na ‘dago idona da suka yi jajir na zube a kanta sai kawai na ga ta ru’de ta fara magana “Ya Ahmad ka yi magana me ya sameka?” Ajiyar zuciya na saki cikin wani irin rauni na sanar da ita dukkan damuwata. Madadin naga ta cigaba da damuwar sai naga ta tuntsire da dariya ta furta “Ya Ahmad wallahi AYSHA na sanka, kawai dai akwai wani dalili da yake nema ya mata Katanga da son naka zai kuma iya togaceku daga aure idan baka yi gaggawar sakawa a d’aura muku aure ba ina tabbatar maka nan gaba zaka rasa AYSHA…” shiru na yi ina murza goshina kafin na ce “Khadija ta yaya kike zaton Iyayenta zasu yarda su aurar da ita a S.S 2.” Ta sake murmushi ta ce “Ka je musu da buk’atar auren kawai banda tariya idan yaso idan ta gama secondary school sai ku tare…” Shiru na yi ina nazarin zuciyata duk gwiwata ta yi sanyi don na san mawuyacin abu ne Abbanki ya yarda da abinda zan je masa, ni kaina ina tunanin yarda zan yi aure na kuma zuba miki ido bayan auren a zuwan sai an tare na kusanceki ko ba so akwai sha’awa balle ke da nake so nake kuma mafarki kullum
Akan wancan gwadaben sai na ji abin da kamar wuya. Gefe guda kuma ina jin tsoron ko kin daina so na don ba zan iya auren matar da bata so na ba, don haka kai tsaye na ce da Khadija “Idan kuma bata so na fa?” Dariya ta yi sosai, dariyar da ta dinga saka min wani irin d’aci a zuciya, a zafafe na ce “Khadija wai meye haka? Ya nazo miki da matsalata zaki saka ni a gaba kina dariya?” Dariyar ta sake yi kafin ta ce Tabbas Ya Ahmad na yarda kai sabon shiga ne a fagen soyayya, duk mutumin da zai Soka da farko ya dawo ya k’i ka da k’arshe to ba k’in ka yake ba sai dai idan akwai wani dalilin da zai saka ya janye soyayyar… ka bincika kuma zaka ce na gaya maka. Kana so ka gane tana sonka ko bata son ka?” Da sauri na ‘d’aga kai, don shi na fi buk’ata. Ta gya’da kai ta furta “zan baka hotona, ka kaiwa AYSHA a zuwan ni ce matar da zaka aura, idan har kaga ta shiga tashin hankali to tabbas tana son ka, idan kuwa kaga bata damu ba to gaskiya sonka bai je ko ina ba a zuciyarta.” “Good idea!” Na furta cikin jin da’di.

Da k’yar na bari kashegari ta yi, kafin na kai kaina gidanku, sai dai me? Ina zuwa aka ce min kina gidan Yaya Muhammad. Wani farin ciki na ji. Na saka aka min kwatance sai gidan Muhammad. Sanda na baki hoton Khadija, lab’e wa na yi ba tafiya nayi ba, ina son naga reaction d’inki. Wani farin ciki ya mamaye ni ganin yarda kika nuna damuwa da hoton da kika gani. Ya Muhd shi ya sanar da ni komai da abinda ake ciki game da Maminki. Hakan shi ya bani k’warin gwiwar zuwa na tari Daddy na da zancen son zuwa a nema min aurenki. Da fari bai amince ba sai da na masa rantsuwar zan amince na barki ki yi karatu sannan ya yarda zai je nema min aurenki da shara’din idan Abbanki bai amince ba zan hak’ura. Na yarda da hakan.

Kashegari kuwa aka je nema min aurenki, abin mamaki take Abbanki ya ce ya amince banda ma yana tausayawa Maminki kada zafin ya mata yawa da yace na tare da matata kawai. Bokon me? Bokon Ai ba fa’dar Allah ba ce. Na ji da’din wannan labarin na tabbatar na auri y’ar babban gida irin matar da Manzon Allah ya kwa’daita mana mu aura. Muhd ne ya bani shawarar zai ‘d’auke ki ya kai ki gidansa har sai bayan an ‘d’aura auren don ya lura kamar damuwar da Mami take ciki ne yake neman tunzira zuciyarki. Ki bujirewa auren. Wannan shine abinda ya faru My Eeesh dafatan zaki yafe min?” Na lumshe idona kawai ina jin yarda yake murzar min hannuna a hankali. “Ana ahubbuki kaseer kaseer Eesh.” Murmushi kawai na saki ina janye hannuna na ce “Ustaz mu tafi gida kada dare ya yi.” Sumbata ya kaiwa hannun yana furta “wani gida kuma Aysha? Kina da gidan da ya wuce nan ne?” Idona na ne ya kawo ruwa na zare hannuna ina furta “Please Ustaz! Kada mu yi haka da kai mana..” Shiru ya yi yana sake matsar da hannuna saitin bakinsa idanunsa a lumshe yake sumbatar yatsun yana furta “Shshsh, idan kika cigaba da min magiya you will spend your night anan…” na waro ido. Jin abinda ya ce bai fasa kissing hannun nawa ba. Sai da ya gaji don kansa ya janye hannun yana sakin ajiyar zuciya ha’de da kallona da burkitattun idanunsa ya mik’e naga ya shiga wata k’ofa da na tabbatar toilet ne, bai wani jima ba naga ya fito da rigar wanka a jikinsa yana goge jikin. Da sauri na runtse idona na ji ya saki dariya mai k’aramin sauti ya furta “Idan baki wasa ba zaki shafa min mai….” Ai ban san sanda na isa bakin k’ofa ba, ina sakin haki na tsaya a bakin k’ofar da zata fitar da kai daga parlorn. Tsawon mintuna biyu sai ga shi ya fito sai zabga k’amshi yake fuskarsa very fresh. Ina ganinsa na yi saurin murza handle d’in k’ofar zan fita sai dai hakan bai samu ba don key ‘din na hannunsa ya k’araso daf da ni, kansa a saman wuya na ya rungumeni ta baya yana sakin ajiyar zuciya, a kunne ya ra’da min. “Kin saka ni wankan dole Ayshata…” wani irin runtse ido na yi na furta “Please Ustazu Ka Bari am too young fa..” naga ya d’an yi murmushi kawai ya kaiwa bakina sumbata ya furta “Mu je kafin Maminki ta k’arar da charging wayarki ta miki missed calls ya fi hamsin…” waro ido na yi ina kallon wayar da Ustaz yake mik’o min, a raina na furta shikkenan na ka’de yau har ganyena….

Da zan tafi Mommynsa da Aunty’s d’insa suka ha’da ni sha tara ta arziki. Tabbas a idanunsu na hango sun yi na’am da ni.

Sanda muka isa k’ofar gida, da sauri na kai hannu zan bu’de k’ofar sai na ji ta a kulle gam. Na juyo ina kallon Ustaz na ce ya haka?” D’an lumshe ido ya yi yana turo min lab’bansa “I need kiss AYSHA in dai kina son ki fita, ina son ki min abinda zan dinga tunawa da shi da zarar na rufe ido da niyyar barci…” “Allah Ustaz ba zan iya ba…” Ji na yi kawai ya yi baya da seat ‘d’insa ya janyo ni da k’arfi na zube jikinsa a hankali ya fara bani wani irin passionate Kiss. Mun d’au tsawon mintuna biyar a haka kafin ya sake ni. Ya danna lock motar ta bu’de “Sweet dream Ayshata, ki yi mafarki na pls…. I mean romantic mafarki…” Da sauri na fice daga motar. Don kamar lamarin Ustaz yana neman girman kwanyata.

Sa’daf Sad’af na shige bedroom ‘dina. Don bana son na yi k’wak’wkwaran motsin da Mami zata ji ni. Ina shiga d’akin kuwa kayan jikina na cire da duk suke k’amshin turaren Ustazu, idan ba hanci na bane ya ji ba daidai ba, sai na ji kamar jikina ma k’amshinsa yake. Da sauri na fa’da toilet don a jikina nake jin ya wajaba na yi wanka.

Ina wankan na dinga jin ana buga k’ofar toilet d’in da k’arfi gabana na wani irin fa’duwa na fito. Ina fitowa kuwa idanuna suka sark’e da na Mami da yake wurga min wani irin kallo mai nuni da zallar jin haushi. Idanunta a burkice banda bata shaye shaye sai na ce ma a buge take… cikin rawar murya na furta “Sannu…sannu Mami, ke ce?” Ta sake wurga min kallon tana mik’ewa ta iso daf da ni. Kallon sama da k’asa take min kafin ta saka hannunta cikin sumar gashi na ta furta “Wanka AYSHA? Wankan me kika yi na ji gashinki a jik’e don’t tell me kin mik’awa wancan wawan kan ki?”

★✍️ 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 19.

𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️

Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

Arewabooks @nazeefah

https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ

Wattpad@Nazeefah381

08033748387.

★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 19.

19.
Chapter 25 · 0% Book details