Sashe 6
Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sai dai na makaro ina d’aga kai na hangota ta cikin mudubi fuskarta a ha’de take kallona. Ta iso inda nake zuciyata ce ta dinga harbawa da k’arfi. Saka hannu ta yi ta cire nik’ab d’in, ta kuma saka yatsa tana zagaye lab’b’ana tana sakin murmushi ta furta “Jambaki AYSHA? Jambaki kika saka zaki makaranta? Me kike son b’oye min ne?” Lumshe idona na yi ina jin zuciyata na bugu da mugun k’arfi. “Kada ki fara AYSHA, kada ki fara abinda zamu zo muna k’aramin yak’i da iyayenki a gidan nan. Goge shi tas idan baki yi wasa ba tsaf zan cireki daga Islamiyyar na samu Malamin da zai dinga koya miki…” Da sauri na rik’e hannunta “Don Allah Mami kiyi hak’uri kada ki raba ni da makarantata, In sha Allah ba zan sake sakawa ba. Kuma wallahi bana kula kowa ko Asma ki tambaya…” Murmushi kawai ta saki ta janye hannunta. “Zan bincika..” Daga haka ta fice bayan ta saka ni na goge jambakin dama ni ko kalli bana sakawa ina da kwallina daga indallahi. Na saki ajiyar zuciya ina fita daga d’akin.
Shiru makarantar da alama ni da Asma ne muka fara zuwa. Muna shiga aji Asma ta fice don itace da Duty ranar. Sai na zauna ni ka’dai na bu’de kur’ani na soma tilawa. Don dokar Tahfiz ce duk wanda ya fara zuwa shi yake fara karatu a lokacin….
K’amshin turarensa da sallamarsa ne ya saka ni yanke karatun cikin fa’duwar gaba. Na kuma kasa bu’de baki na amsa sallamar…
Tsaye ya yi yana kallona bai shigo ajin ba, ga shi nik’ab d’ina a d’age yake. Na saka hannu zan ja nik’ab d’in k’asa ya furta “Ba kya amsa sallama ne Malama…” Wallahi jin muryarsa ka’dai sai da ya razanar da zuciyata. Muryata na rawa na ce “Alaykassalam…” Murmushi ya d’an saki ya isa wajen zamansa. Sai da ya zauna ya furta “Ina sauran y’an ajin? Ni fa bana son makara, don haka dole a kiyaye…” shiru na masa don bani da nutuswar da zan iya cigaba da amsa masa. “Cigaba da karatunki…” Ji na yi kamar na zunduma ihu. Ta ina zan iya karatu wallahi ba zan iya karatu daga ni sai shi a yanayin da nake ciki ba… d’ago ido ya yi ya d’an kalleni ya sake furta “Cigaba na ce….” Ji na yi kamar na zunduma ihu. Allah ya taimake ni sai ga Asma ta ranga’da sallama cak ta tsaya ganin sabon Malamin. Gaisheshi ta yi ya amsa mata yana d’an tsuke fuska. “Kin makara ki juya…” Da sauri ta ce “Wallahi Malam ba makara na yi ba, na je duty ne ka tambayi AYSHA ma ka ji…” “AYSHA?” Muka ji ya fa’da, wanda yasa na yi saurin d’aga kai don a zatona kirana ya yi, sai naga kawai ya yi murmushi ya girgiza kai ya ce “Ku bu’de Manhajjul Muslim… A ina kuke?” Asma ce ta amsa ni kuwa sam hankalina baya wajen…
Tunda ya fara karatun bai ‘dago ya kallemu ba y’an aji kuma duk wacce tazo sai ya tsayar da ita ya ce ta makara… ga karatun da yake mana mai mugun saka kunya don karatu ne akan yarda ake wankan janaba da abinda yake sabbaba shi..
“Yanzu kun gane yarda ake wankan ko? Da kuma sabbabinsa?” Asma ce kawai ta ‘d’aga kai, ya juya yana d’an kallo na.. “AYSHA kin gane menene janaba, sababinta da kuma yarda ake wankanta?” Runtse idona na yi jikina har ya fara rawa musamman idanunsa duka ya zubesu a kaina. “Ba kya ji ne? D’auke wannan bak’in k’yallen ki min cikakken bayani….” “Ya ilahi na furta ina jin kamar na zunduma ihu ta ina zan fara wannan abin kunyar…. “Ke samo min ruwa a office mai sanyi, ke kuma ina jin ki?” Ina kallo Asma ta fice tana dariya k’asa-k’asa. Ji na yi kamar na ruga na gudu musamman da ya jawo kujerarsa daf da ni, ina sake shak’ar Mayen turarensa… “AYSHA” ya fa’da cikin wata irin husky voice “D’ago ki kalleni..” Da k’yar na d’ago sai dai na kasa kallon nasa. Kallona yake shi kuwa kamar ya samu Tv fuskarsa d’auke da murmushi ya furta “Answer my question before na ha’da duk makarantar nan ki musu lecture akan haka…. menene janaba? Hukuncin ta a musulunci da yarda ake wankanta?”
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
Albishirinku! Albishirinku!!
Yau ne fa! Yau ne litattafan Bright pens za su fara zuwa muku da izinin Ubangiji….
1.K’arfe a wuta. AYSHA cool marubuciyar k’anwar maza.
Hadarin gabas Nazeefa Sabo Nashe. marubuciyar Me Zan Yi da ita?
Mutallab daga harzik’ar marubuciya Nimcyluv
Zaytoon zai zo daga Alk’alamin Malamar Adabi Zee kumurya.
Za’a fara sakar muku K’arfe a wuta kafin zuwan sauran In sha Allah.
Don samunsa a sauk’ak’e ku yi joining wannan link d’in…
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/FTFuiA4woYJCgNQrcBYGX4
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Page d’in kacokam naki ne k’anwata Nimcyluv hope na goge lefina Masoyiya 🤣
Arewabooks @nazeefah
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 6
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR
Ji na yi zuciyata ta cigaba da bugu, na kasa amsa masa tambayar ya bi kuma ya tsare ni da ido. Hannayena kawai nake matsawa don ban san me zan ce masa ba. “Ba ki ji ba? D’age wannan bak’in k’yallen don ban sani ba ko hararara kike..” K’iris ya rage na fashe da kuka saboda yanayin da ya saka ni, ga mayen turarensa ya bi ya hana ni sukuni… “ki d’aga na ce, Are you dumb?” Hannuna na rawa na saka na d’age nik’ab d’in. Na runtse idona saboda har ga Allah ba zan iya cigaba da kallonsa ba… ina ji ya sauke ajiyar zuciya yana furta “Kin yi passing wannan Oya tashi ki fita sallah…” Tun kafin ya kai k’arshe na mik’e da sauri ban san yarda aka yi na isa bakin k’ofa ba, ni dai na gan ni a waje. Na tsaya ina sauke numfashi hannuna dafe da k’irjina da take matsanancin bugu… Ina jin k’amshin turarensa alamar nan yake tahowa na zuba sauri har da ‘dan gudu don kada ya riskeni a wajen…
Yanayin tsarin karatun nasa ya saka y’an aji aka daina makara saboda ana son karatun nasa sosai. Na san wasu y’an matan da yawa ba don Allah suke zuwa da wuri ba. Ga shi su cab’o Uban kwalliya a fuska a baza k’amshin turare ana yi ana zuba iyayi duk don Ustaz ya yaba. Shi kuwa sam baya kulasu idan zai shigo ma bak’in glass yake sakawa ya rufe idonsa…
Wata rana da ta kasance ranar Talata ce. Sam kasa yarda na yi na je makarantar saboda da na duba maddar da zamu yi sai naga fik’hu ce. A rayuwata ina kunyar Ustaz shi yasa sam ba zan iya zama ya karanta Fik’hun a gaba na ba, kada a yi irin ta ranar da muka karanta Babul janabati… Don haka yau ina duba littafin naga za’a yi bayani ne akan ruwa kashi uku da yake fitowa daga gaban mace na ji sam ba zan iya zuwa ba. Sanda Asma ta biyo min ta shiga d’akina tana kallona ta furta “AYSHA me ye haka?” Nima kallon nata na yi nace “Me kika gani?” Ta saki tsaki tana kallon agogo “Yau kuma wani sabon abu zaki tsiro da shi, makara? Abinda ba halinki ba. Kin san dai Ustaz Ahmad ya jaddada rashin son makara ko?” D’an yamutsa fuska na yi “Ke makarantar ce fa ba zani ba.” Ta waro ido “Dalili?” “Bana jin da’di ko na je ba fuskantar karatun zan yi ba. Ki ba shi uziri na.” Asma ta ‘d’au jakarta tana furta “Allah ya baki lafiya, amma kamar ciwon naki bai kai inda ba za’a iya zuwa makaranta ba..” Ban mata magana ba har ta fice daga d’akin. Na saki ajiyar zuciya duk ina son zuwa makarantar ko don naga Ustaz wannan karatun da zai yi yau ne zai hana ni zuwa. Allah ya san ba zan iya zama yana zayyano min karatun nan me saka kunya ba…
Kashegari da wuri na shirya musamman ganin maddar Hadith da Tajweed ne da mu. Asma ta biyu muka tafi..