← Book details Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 30

Sashe 24

Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanda na kwanta kuwa kiran wayar Ustaz ne ya isheni, kunyarsa da nake ji na abubuwan da suka wakana a tsakaninmu ne ya hana ni d’aga wayar, sai da ya yi kira ya kai biyar sannan na saka wayar a kunnena. Wata ajiyar zuciya ya saki. Yana furta “Na kasa barci Eeesh, kina ta yi min gizo duka surar jikinki ta baibaye tunani na, da na san haka ne da ban fara janyowa kaina ba….wani feeling nake ji mai zafin gaske AYSHA, na kasa controlling kaina na samu barci… please ki amince min even once… na kusanci halak d’ina..” K’it na kashe wayar ina mayar da numfashi. Lamarin Ystaz yana neman ya girmi kaina. Kiran duniya ban amsa ba. K’arshe ya turo min msg. “Shikkenan tunda ba zaki amsa ba, I really missed your cutable lips…. And…boo….” Sai ya yi alamar murmushi bai k’arasa ba. Wani irin waro ido na yi a fili na furta “Na shiga uku me yasa Ustaz sam bai da kunya, amma idan ka ganshi a fili ba zaka zaci zai aikata haka ba. A lumshe idona yake Amma duk wasu feeling ina jinsa nima kamar Ustaz d’in kawai daurewa nake don ban san ya zan yi ba idan ba dauriyar ba, na san ko giyar waje na sha ba zan amincewa buk’atar Ustaz ba, idan ba so nake Mami ta yi yaga yaga da nama na ba.

Da safe sanda na isa makaranta ashe labari tuni ya baza makarantar kunya ta dinga isata jin ana ta min Allah ya sanya alheri. A islamiyya ma kasa katab’us na yi duk da dai da nik’ab a fuskata.

Tunda aka d’aura aure sai gidanmu ya zama nasu Ustaz, don in dai yana gari baya jure rashin iya zuwa. Mami kuma ta kasa ta tsare don k’iri k’iri wani lokaci da ya tambayeta zan raka shi unguwa ta ce “Ahmad, ka saurareni da kyau ba zan amince ka dinga fita da AYSHA bata tare ba.” Ya ‘dan ware ido yana kallonta ita kuwa ba abinda ya dameta ta mik’e ta shige bedroom d’inta. Ustaz ya ‘dan dubeni yana sakin ajiyar zuciya. Na mik’a masa lemon da na ha’da masa, don anan saman Mamin muke zance da kanta Kuma ta buk’aci hakan. Ranar da yazo bayan d’aurin aure da kwana biyu zan fita sitroom ta ce “AYSHA hau da shi sama na, ai ya zama d’an gida, bai kyautu a dinga barinsa a parlorn waje ba, sai kace wanda yazo zance.” Gaba ‘d’aya wajen ba wanda bai d’ago ya kalleta ba, hatta Abba sai da zancen ya bashi mamaki. Ita kuwa ta maze tana murmushi ta ce “Da ne nake adawa da auren AYSHA, banda yanzu da k’addara ta Riga ta tabbatar da hakan. Allah ya sanya musu albarka a auren.” Abba murmushinsa ya kasa b’oyuwa kamar yarda bakin Umma ya kasa rufuwa.

Shikkenan tun daga ranar Ustaz ya samu sake, mafi yawan lokuta ma tare ake zama a ci abincin dare da shi. Ya d’auki iyayena kamar nasa kamar yarda nima kullum muke gaisawa da Mommynsa a waya idan har na sha’afa ban kira ba, da kanta take kira na. Khadija kuwa ta zama uwa k’awata tsabar shak’uwar da muka yi, duk da ta girme min.

Gefe guda al’amarin Mami na bani mamaki a zahiri a gaban kowa ta hak’ura amma a ba’dini ni ka’dai na san yarda muke zaune da ita, musamman duk ranar da Ustaz zai zo ta dinga ha’de rai kenan tana min masifa komai na yi kuma laifi yake zama a wajenta. Ban gayawa kowa ba, don bana son kowa ya sani balle a ji haushinta. Mafi yawan lokuta idan Umma ta fara mata zancen da ya rage na watannin tariyata tsam take mik’ewa ta bar wajen.

Wannan abu yana tab’a min ruhina har na ji sam ban ji da’din abinda take yi d’in ba. In dai batun karatu ne, da bakin Ustaz ya mata alk’awarin sai nayi karatu a gidansa har sai nace ya isheni, tunda shima ta wani fannin d’an boko ne da ake damawa da shi a bokon.

June-july, shine watannin da muke saka ran zamu gama makaranta. Kwanci tashi sai ga shi lokacin har yazo. Ina ji ko mu da zamu zana jarrabawar bamu kai Ustaz lissafa kwanakin ranar graduation d’in mu ba. Wata rana muna waya. Ya ce “AYSHA, na k’agu ki gama wannan makarantar na sauke buk’atar da ta min cunkoso a jikina….” Waro ido na yi kafin na furta “Wace buk’ata kuma?” Sai da busar da iskar da take bakinsa, har na ji sautin ta ta cikin waya sai na ji ya ce “Kashe mu yi vedio call, zan gaya miki buk’atar…” “Ni dai A’a, na yafe.” Na fa’da a shagwab’e. Ya saki murmushi kafin ya furta “Ashe kin san buk’atar tunda kina jin kunyar na gaya miki, bari na miki ta Malam bahaushe, wallahi AYSHA na gaji, gangar jikina tana buk’atar maha’dinta, ina son jin d’umin Aysha zahirinta ba tare da shamakin tufafi ba…” da sauri na kashe wayar ina mayar da ajiyar zuciya. Ni da kaina na san Ustaz ya yi hak’uri gashi yanzu ko rungumar baya samu ya yi min Mami ta kasa ta tsare, sau tari sai muna zance sai ta shigo parlorn da niyyar d’aukar wani abin. Wani lokacin Ustaz kasa sakin jiki yake yi. Shi yasa yace min sau da yawa shi yasa baya zaman Nigeria yake tafiyarsa wata k’asar ya kwana biyu.

Burina kawai na fito da A1 a duka subject d’in da nake, don haka na dage da karatu Ka’in da na’in. Ustaz ma a wannan lokacin ya mugun d’aga min k’afa sai dai ya kira ni a waya. Har rama na yi saboda bani da isashshen lokacin kaina ko waya a gaggauce nake amsa masa, sau tari sai ya nuna fushin sa sannan nake bashi lokaci na.

Ranar da muka gama makaranta, rana ce mai matuk’ar mahimmanci a wajena. Duk da Ustaz ya hana ni ko saka kwalli a ranar, hakan bai hana ni zuba wani Uban kyau ba na kwatance. Wata doguwar Riga mai masifar kyau na saka wacce Mommyn Ustaz ta kawo min. Da takalmi half cover wanda zai matching da adon rigar golden brown. Na yi rolling kaina. Sanda Ustaz yazo zamu tafi hararata ya dinga yi yana tsaki k’asa k’asa. Muna isa wajen ya kulle motar yana zuban narkakkun idanunsa. Kafin ya kaiwa bakina sumbata ya furta “Me yasa? Me yasa ko baki kwalliya ba sai kin yi attracting idon mutane..” Murmushi kawai na masa. Sai naga ya bu’de dashboard ya ciro nik’ab Sabo fil a leda da kansa ya saka min nik’ab d’in yana furta “fuskar Matata haramun ce ga dandazon maza.”

Ustaz ya kasa ya tsare ta dole ya nunawa mutane ni matarsa ce, don bai ji kunyar ko su Abba ba sanda za a bani kyauta ya rik’e hannuna muka hau kan step. Shi ya karb’i kyautar da Mataimakin governor ya bani sab’anin sauran matan da suka dinga amsa da kansu. Tafi aka dinga yi da wani irin ihu.

Da aka tashi bai barni na yi hotuna ba, ya saka ni a mota yana furta “Is enough kuma, idan ba so ake Ustaz zuciyarsa ta yi bombing ba..” ya tada Motar yana jan hannuna da yake saman cinyata yana murzawa a hankali ya furta “Saura 2 weeks na mallaki komai da komai na jikinki Ayshatu na, har nan ko?” Inda hannunsa ya sauka ne ya saka ni ware ido ina runtse su da sauri da k’arfi. Sai naga ya daki sitiyari yana murmushi ya furta “na godewa Ubangiji da ya mallaka min kamilar mace, da nake jin In sha Allah nine nan d’an mukullin wancan abin da ake killacewa, I love you Ayshatu na….ina son ki fiye da son da nake wa ruhina, I wish to spend the rest of my life with you…” ya fa’da yana d’an jan hancina. “Na kusa cire kunyar nan gaba d’aya. Just 2 weeks za’a saka, a haka ma ni ba haka na so ba na so a ce 1week after Graduation kawai, amma ya zan yi Mommy ta kafe basu gama shirye shirye ba.”

Gani na yi kawai ya ja gefen hanya ya yi parking. Ya kwantar da kujerar yana kallona da wasu lumsassun idanunsa. Tsigar jikina ce take tashi kawai. Iya zallar kallon Ustaz yana canja min yanayi inaga ranar da zan ganni da ga ni sai shi a matsayin ma’aurata. “Say something AYSHA, ko da yau ka’dai ne kice Ustaz I love you na ji sanyi a raina…” Lumshe idona na yi, Karon farko na ji yau ina son shayar da Ustaz mamaki. Murya a sark’afe cikin wani irin sauti na furta “I… Love…You Ustaz with All my heart Ustazu na.” Jina kawai na yi a jikinsa yana bani wasu zafafan kiss. A kunne ya ra’da min “Me kika tanadar min a ranar da zamu tare?” Na runtse idona. “Kada ki ji kunya My Eesh ba kunya tsakanin Miji da Mata say it…. Kin tanadar min duka kan ki…” na d’aga kai na na ji ya bani sumbata a forehead d’ina da tsinin hancina. Ya saki ajiyar zuciya a hankali ya mayar da seat d’in yarda ta ke ya ja muka tafi.

Sanda muka isa gida, na hau sama Mami na tarar tana cika tana batsewa a cikin parlornta, idanunta sun ka’da jajur tana kallona kafin ta zauna ta rik’e kan nata. Jikina a sanyaye na yi hanyar da zata kai ni d’akina, na ji muryar Mami a kaurare ta ce “AYSHA! Zo nan!” Cak na tsaya kafin na juya a hankali na isa inda ta ke. Na zauna a gefenta. Ta nuna min cards… “Ga cards d’in bikinki nan, burinki da na iyayenki ya cika, ina muku murna, ba zan b’oye miki ba AYSHA sam bana farin ciki da aurenki, zan kuma amince da aurenki ne idan kika amince da wasu shara’di da zan baki…. As from today zaki dawo kwana a d’akina ba kuma naso ki gayawa kowa, sannan ban amince ko gayawa kowa wannan shara’din nawa ba, sannan ki sanar da shi daga yau ba waya tsakaninku sai mesaage…….

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA 17.

https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ

NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎

𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Chapter 24 · 0% Book details