Sashe 22
Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sallah na yi ina idar da sallahr na sauka k’asa wajen Umma. Har lokacin jira nake na ji Ustaz ya kira ni amma bai kira ba. Kawai sai zuciyata ta dinga bani yana can wajen amaryarsa. Don takaici har wata k’walla ce ta so zubo min. Na matse ha’de da tura k’ofata parlorn Umma. Ba kowa a parlorn da alama duk bak’in sun tafi. Sai Umma ita ka’dai da k’anwarta suka ‘dago suna kallo na. Umma ta d’auke kanta. Sai Anty Zee ce ta ce “Shigo mana Aysha kin ci abinci?” Na ‘d’aga kai na “Na ci Anty.” Ta yi murmushi tana fa’din amaryar da ba lalle, wannan aure naki Aysha Ai shine bagatatan. Yaushe ya ce zaki ki gaida iyayensa?” Wani farin ciki ya shige ni don abinda nake son na ce kenan, amma ba kasa gayawa Mami balle Umma. Na gyara zamana ina furta “Yau ya ce Anty..” Ta saki murmushi tana fa’din “Kin ji ko Yaya, ai na san wallahi kawai zan ce ne, ace kawai mutum ya auri mace sai ya zuba mata ido alhali sabon shiga ne a aure a ce wani sai ta k’arasa karatu, karatun me Allah na tuba a gidanta ba zata yi karatun ba, wallahi kada ki bi ta wani karatu ki tattara y’a ki mik’a d’akin Mijinta….” Umma ta waro idonta tana furta “Rufa ni ki saya, ni meye nawa da za’ace ni zan saka a kaita d’akin Miji, ki bar uwarta y’ar a lallab’a da yaya ma aka samu aka shawo kanta a yau d’in. Shekara kamar yau ne, Idan Allah ya kai mu.” Anty ta yi d’an tsaki tana kallon Umman ta ce “Allah ya kai mun, idan da rabon an yi taron suna ne ba taron biki ba sai mu ce san barka…” Da sauri na mik’e na fice daga ‘dakin cikin matsananciyar kunya. Na koma saman Mami. Bak’in sun tafi sai ita ka’dai zaune ta zuba hannunta a k’unci. Har na zauna daf da ita ba ta sani ba sai da ba dafa ta sannan ta juyo a razane tana d’an kallo na. Ta furta “Aysha ce?” Cike da tausayinta na ce “Mami kin ci abinci?” Ta ‘d’aga min kai tana d’an murmushi. Na yi shiru ina wasa da yatsuna na furta “Mami Ustaz ya rok’i alfarmar yana son na je gidan su yau after magriba….” Mami ta ‘dago tana kallona, idanunta suka bayyana tashin hankalin da zuciyarta take ciki. Ta gyara zamanta tana sakin ajiyar zuciya sai kuma ta kama hannuna murya a raunane ta ce “Ba zan hanaki bin sa ba AYSHA, don yanzu duk duniya ba wanda yake da iko da ke sama da shi. Sai dai zan rok’i alfarmar ki tsare jikinki, don maza mayaudara ne idan dama jikin naki yake so da zarar ya kusanceki zai iya sakin ki tun kafin ki tare…. Ki min alk’awarin ba zaki bari Ustaz ya kusanceki ba..” Na d’aga kai na, ina ji har a zuciyata na amince da abinda Mamin ta ce. Ta sakar min murmushi ta furta sai ki shirya da wuri kada yazo yana jiranki amma banda saka turare… na d’aga kai.
Da magriba ina idar da sallah Mami ta shigo d’akin hannunta d’auke da wata leda. Ta zauna a gefen gado. Tana bu’de ledar wata doguwar Riga ce mai masifar kyau kalar bak’a da stone golden ta yi matuk’ar kyau. “Ki saka wannan, sai ki je gidan nasu, idan kin je kuma bana son rawar kai ki nuna musu ke mai tarbiyyace.” Na amsa ina godiya. Bata amsa ba ta wuce ta fita.
Da wata irin murna na zura rigar a jikina na shafa powder sama sama, sai na yi rolling. Ba k’aramin kyau na yi ba ni da kai na na sani. Sanda na fita parlor sai naga Mami bata nan. Na san tana k’asa na sauka k’asan don Ustaz ya isheni da kiran waya.
Yarda na zata kuwa suna tsaye a kitchen ita da Umma. Suka juyo suna kallo na. Anty Small ta furta “Ma sha Allah, Allah ya yi halitta.” Mami ta dafa ni tana furta A dawo lafiya, and take care AYSHA. Ga wata leda nan ki kaiwa Inlaw d’inki abinda ke ciki…” Na d’au ledar ina murmushi na fita k’ofar gida don na san Abba yana masallachi sai dai su Umma su gaya masa.
Cikin takun nutsuwa na isa bakin motar na saka hannu na bu’de k’ofar gaban motar. Gaba na ya yi wani irin mugun fa’duwa ganin Habibteeyn Ustaz a gaban motar, ta sha kwalliya ta yi masifar kyau tana zabga k’amshi. Murmushi ta ‘dan saki ni kuwa fuskata a tsuke na juya da nufin komawa gidanmu don wallahi in dai da wannan za’a ba zan je ba…. Kai bana jin ma zan iya kishi da zanka’ded’iyar mace irin wannan habibteeyn ta Ustaz ba. Ta ko ina ta fi ni….
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 16.
16…
AYSHA! Na ji Ustaz ya fa’da cikin muryarsa da take bayyana ginshira. Na ja na tsaya sai dai ban jiyo ba, Saboda bana son na jiyo d’in naga Habibteeyn Ustaz. Rufe k’ofar Motar da aka yi ya tabbatar min da ya zo wajen. A daf da ni ya tsaya. Kafin na juyo na ji hannunsa a cikin nawa hannun. Da kansa ya juyo da ni yana k’ok’arin lalubar idanuna ni kuwa na ja na runtse idon. “Wuce mu tafi.” Ya ce cikin wani cool voice da ta so ta saka raunin da yake zuciyata ya bayyana… “Ni ba zan shiga ba..” “Me yasa?” Ya fa’da bayan jin abinda na ce. Na d’an turo bakina ina furta “Ka je kawai, ka je ka kaita ni na hak’ura..” wani murmushi ya saki yana furta “Tafiya da ita ne ba kya so?” Na d’aga kai na. “Me yasa zaka zo da ita?” Na fa’da hawaye suna son zubo min. Ustaz murmushi kawai ya saki ya ce “Maza ki yi kuka a gabanta ta raina ki.” Na matse hawayen ina kallon cikin idonsa da suke lumshewa kamar me… “Ku je zan saka Ya Aliyu ya kai ni a motar Abba..” cute smile d’in ya sake yi yana jan hannuna har kamar zan fa’da jikinsa. Ya furta “Yanzu dai ba kya son Third Party a
Cikin tafiyar mu ko?” Da sauri na d’aga kai. Sai naga ya saki hannuna yana murza goshinsa a hankali. Kallon k’asan ido yake min kafin ya jefa min tambayar da ta so saka ni zubewa a k’asa tsabar yarda jikina ke rawa. Cewa ya yi “Kina so mu ka’daice, in har kika yarda muka tafi mu ka’dai zaki min deep kiss a cikin motar…” ya fa’da yana murza hannuna. Da sauri na janye hannun ina furta “Mu je kawai, amma ta koma baya tunda nice Uwargida.” “Done wifey ya furta yana dariya k’asa-k’asa. “Hannunki AYSHA so soft, har bana son na daina tab’awa…” Da sauri na janye hannun ina dubawa naga ko Maigadi ya ji, sai na ga ma baya wajen. Muka isa bakin motar hannuna cikin nasa yana ta murzawa. Ja na yi na tsaya ina jin zuciyata kamar ta buga, ganin yarda Ustaz ya durk’usa daf da ita yana gaya mata magana. Sai naga ta ‘dan ha’de rai ta fito tana min wani kallon banza ta shiga bayan motar. Murmushi na saki ina jin duk wani bak’in cikina ya yaye. Na shiga gaban Motar cikin jin haushin yarda da ta zauna a motar…
“Baku gaisa ba?” Muka ji muryar Ustza daga sama bayan
Mun fara tafiya. Shiru kowa ya yi har sai da ya sake furta “Ba kwa ji ne ina magana…” Sannan ta furta “Ina yini?” A ciki na amsa don sai naga kamar ta fini sauk’in kishi.
Wani irin wawakeken gate muka shiga, inda muka tarar da makeken fili. Ustaz ya yi Parkin ina kallo ta fice cikin takun isa da son ta nuna min ita ta san gidan tunda cousin ‘d’insa ce. Na d’an ha’de rai ina cije leb’ena idona suka kawo ruwa. Ustaz ya sunkuya yana kallona ka’dan, tunda mu ba mu fita daga cikin motar ba. Ji na yi ya kaiwa bakina sumbata ya kuma lashi d’an guntun hawayen da ya zubo min. “Kukan menene?” Ya furta a cikin kunnuwa na. Da sauri na rintse idon, don na lura Ustaz so yake ya kashe ni da salonsa. “Mu je mana Zauj, ko sai na d’aukeki..” na d’an turo bakina ina furta “Ba ga shi can har ta wuce ba, so take ta nuna min lallai ta fi ni iko da gidan ku.” Yatsa ya saka yana zagaye lab’b’ana. “Wato ashe bakin nan ya iya tsiwa? Amma da kike kasa sak’at idan kin ganni a wuri. Mu je na raka ki kin ji tunda ita ta nuna mana gidansu ne ta tafi ta barki.” Ya fita ya zaga ya bu’de min mota. Zai rik’e min hannuna na janye ina d’an duban hanya na furta “Ka bari mana, kada wani ya gan mu?” “And so what? Idan an gan mu Ai ba haramci muka aikata ba ko?” Ya fa’da yana tsotsar bakina ka’dan. Na lura lips d’ina suna burgeshi. “Ke halak d’ina ce Aysha, a yanzu ba wani shamaki tsakaninmu da ke, sai wancan karatun da Maminki ta kafe sai kin yi,
Wallahi ba ruwana duk ranar da ta wayi gari ta ganki da ciki….” Da sauri na waro ido jin abinda ya fa’da. Ya lumshe ido yana d’aga kai ya ce “Am serious Eesh baki san yarda nake ji akan ki ba…” ya fa’da yana jan hannuna.