← Book details Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 30

Sashe 12

Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Har na dawo daga makaranta ranar Mami bata mik’e daga saman gadonta ba. Ko kayan barcin bata cire ba. Na shiga na sameta na sanar da ita na dawo. Ta bi ni da kallo kafin ta saki ajiyar zuciya ta nuna min gefenta. “Zo AYSHA ki kwanta ki huta…” Ban k’i tayinta ba don ina buk’atar hakan na san kwanciya kusa da itan ne kawai zai saka na daina jin b’acin ran da nake ciki. Sau tari idan na saka jikina a jikinta ina samun nutsuwa idan ina cikin tashin hankali ko b’acin rai. Ta jawo ni na shiga jikin nata sosai. Hannu ta saka a bayana ta shafawa a hankali kamar yarda ta saba min. Muryata a k’asa sosai ta furta “Aysha me yasa kike son bujire min? Kada ki cuci kanki ki yi aure at your young age, zaki cuci kanki, zaki yi nadama nan gaba rayuwa ta canja. Ke ka’dai nake da hope a kanki AYSHA don Allah kada ki bujire min, ko me za’a miki kada ki amincewa auren Ustaz.. kin yarda.” Na d’aga kai sai naga ta saki ajiyar zuciya ta bani peck a kumatu tana sakin murmushi ta furta “Thanks my beautiful Baby, I love you..” Shiru na yi sai da ta d’an ja kumatu na ta furta “Ba zaki mayar min ba? Ko fushi kike da ni?” “I love you too Mamy..” na fa’da kamar yarda na saba fa’da koda yaushe idan ta furtar kalmar. Ta lumshe ido tana sake jana jikinta ta furta “Oya sleep…” zan yi magana ta furta “Shsssh!” A kunne na hakan yasa na lumshe idon dole. Take ni da Mamy barci ya d’auke mu. Barci da ba mu tashi farka wa ba sai da aka yi kiran sallahr la’asar. Na bu’de ido da sauri don na san tabbas yau na makara a makaranta. Mami bata san Ustaz yana koyarwa a makarantar mu don haka bata saka ido a kaina da zuwa makarantar ba. Ta bu’de idonta da k’yar tana kallona “Ya dai Aysha?” Na sauka daga gadon ina furta “An yi sallah Mamy, kuma zani Islamiyya.” Kanta ta rik’e a hankali tana d’aga min kai. Na fice da sauri.

A gaggauce na watsa ruwa na yi shirin Islamiyya na fito da sauri. A d’aki na samu Mami daga ita sai rigar wanka. Ta mudubi take kallona ta furta “Kin shirya Aysha?” Na d’aga mata kai. “Zo ku shafa min mai a baya na.” Na isa wajenta da d’an sauri na zuba nan a hannuna ta zame rigarta na fara shafa mata. Ban wani damu ba don na saba shafa mata d’in. Kuma Mami ba ta damuwa da suturce kanta koda ina wajen abinda ya danganci k’irjinta kam bata damu ta b’oyeshi ba. Tun ina jin kunya har na saba. “Ada lafiya ta fa’da tana mik’o min chocolates masu d’an yawa. Tana furta “Ki tabbata kin cika min alk’awarina Aysha, kada ki sake ki amince da auren Ustaz..”. Na amsa na fice da sauri..

Ina shiga makarantar na tabbatar Ustaz na nan don ga motarsa nan, gaba na ya fa’di don na san na makara ba ta wasa ba. Amma haka na d’aure na nufi ajin. Harabar makarantar shiru duk an yi sallah an koma aji. Zuciyata na bugawa na isa k’ofar ajin fuskata a ha’de don ya kamata na fara janyewa Ustaz don na cikawa Mami alk’awarinta, ya zama dole na mata halacci musamman ganin ita bata haihuwa kada zafin ya mata yawa…

Idanu y’an ajin suka zubo min, Har shi Ustaz d’in da ya tsayar da karatun da yake yana kallona. Na sake ha’de raina na nufi wajen zama na. “Aysha Imam Khaleel kin makara.” Ya fa’da cikin dakakkiyar muryarsa cak na tsaya ban k’arasa inda zan zauna d’in ba. Fuskata a ha’de na d’ago ina kallonsa. Ina ji kallon ne ya bashi mamaki. “Me yake damunki?” Juyawa na yi na fice kawai daga ajin. Ustaz na ji yana kiran “Aysha!” Na k’i na juyawa na koma saman step d’in na zauna kawai kaina a saman cinyata idanuna suna zubar da hawaye. “Tashi ki shiga aji.” Na ji muryarsa a kaina. Ban d’ago ba, ban kuma shiga ajin ba. “Ba kya ji ne Aysha?” Na d’ago a zafafe ina kallonsa na furta “Ni ba zan shiga ba, ka k’yale ni…” Cak ya tsaya yana kallona cikin narkakkun idanunsa ya furta “Ma Asabaki?” Wanda akan lab’b’ansa kawai na ji furucin. Ya lumshe idonsa ya furta “Tashi ki shiga..” Ba musu na mik’e jikina a sanyaye kamar zan shiga ajin sai na yi hanyar fita daga gate d’in. Ina ji Ustaz yana fa’din “Aysha tsaya…” Amma Ina na bawa banza ajiyar sa na fice har da d’an sauri na… Ina fita gate na juya naga Ustaz ya d’an rik’e kansa yana kallo na yana cije leb’ensa…..

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://www.arewabooks.com/chapter?id=669e462086c5cb5aff79fe08

https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ

NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎

𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️

Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

Arewabooks @nazeefah

https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ

Wattpad@Nazeefah381

08033748387.

★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 11

‎Runtse idonsa naga ya yi da sauri, kafin ya girgiza min kai, “Kada mu yi haka da ke Aysha, kada ki sakawa zuciyata ciwon da zai yi wahalar warkewa.” Sai naga ya durk’ushe a gabana idanunsa sun tara wata k’walla da ya k’ara idanun nasa kyau. Duk da akwai tazara a tsakani na da shi sosai ma, don na lura yana taka tsantsan k’warai da gaske wajen ganin ya kiyaye dokar Allah. “Ki taimaka min don Allah ki amince na aureki, ba yarda idan kin gama secondaryn sai Ai mana auren, duk da haka ma sai na yi k’ok’arin gaske kafin na iya daurewa, ni ka’dai na san me nake ji a kanki, ni na san irin yarda girman son ki yake a zuciyata, Please AYSHA will you marry me?” Runtse idona na yi ina jin yarda zuciyata ke matuk’ar gudu da tarin k’aunarsa a ciki, da gaske dauriya nima kawai nake da kuma son cika alk’awarin da na yiwa Mameey Amma ina ji a raina rashin Ustaz a rayuwata daidai yake da rasa rayuwar tawa. “Ki amsa min AYSHA, please za ki aure ni?” Wallahi ban san sanda na d’aga kai ba, Saboda wani irin kallo mai azababben kyau da Ustaz ya dinga zuba min da narkakkun idonsa. Gani ya yi ya dunk’ule hannunsa duka biyun yana sakin ajiyar zuciya ya furta “Shukran ya Rabbi, Shukran ilaiki Ayshata…”

Ya mik’e yana sake kallon Table bayan ya ajiye wata leda a kusa da ni. Ya furta “Yau ma AYSHA ko ruwa babu?” Sai kunya ta kama ni na yi k’asa da kai na, ina wasa da zoben hannuna. Murmushi mai sauti ya saki. “Shikkenan tunda rowa kike min, na gode..” ya yi furucin da karyayyiyar murya. Da sauri na girgiza kai ina furta “Ai ban san zaka zo ba…” “Ta ya zaki san zan zo bayan kin k’i picking call d’ina, kina hora ni saboda kina tunanin kin yi yarinya sa aure ko?” Ya furta yana d’an murmushi ha’de da cije leb’ensa ka’dan. “Allah ya nuna mana lokacin, Jibi zan wuce Egypt, zan samu one week a can. Idan na dawo kashegari zai kama litinin anan zan sha ruwa. Ina jiran girki mai kyau daga wajen kyakykyawar budurwata, za ki yi min?” D’aga kai na yi da sauri ya yi dariya “Kamar gaske Allah yasa kin iya girkin.” “Allah kuwa na iya..” Ya mik’a min hannunsa “Zamu gani ai, Allah ya kai mu ranar kuma ban amince kowa ya tayaki ba. Kina girkin muna vedio call, ba ni zoben hannunki.” Na waro ido ina girgiza kai. “Ai ya yi maka ka’dan, ji fa hannunka.” Ya kai duba zuwa hannunsa “In dai ba rowa zaki min ba, ai sai ki bani na gwada na gani, ko ya yi min ka’dan ina so zai min rakiya Egypt..” Na zare zoben ya nuna min gefen kujera “Ajiye a nan, Zan d’auka.” Na kuwa ajiye ina sake girmama halin Ustaz na kiyaye dokokin musulunci. Ya ‘d’au zoben ya saka a k’aramin yatsansa sai ga shi kuwa ya ‘dan shiga. Sumbatar zoben ya yi a hankali yana lumshe ido ya furta “Ina sonka zobe, Saboda ka fito a hannun AYSHA ta..” Ban san sanda na saki murmushi ba ina jin kamar ni Ustaz ya sumbata.. Daga haka ya fice daga sitroom d’in yana sakin murmushi…
Chapter 12 · 0% Book details