← Book details Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 30

Sashe 19

Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sallama na shiga parlorn yana zaune ya tank’washe k’afa suna hira da Ya. Muhd har ya fara cin abincinsa. Ya ‘dago kai ya kalleni ya mayar kan abincinsa. Ya. Muhd mik’ewa ya yi ya fita. Ni kuma na zube a k’asa daga gefensa ‘dan nesa da shi ka’dan. “Ina yini?” Ya ‘dago yana kallona. Kafin ya furta “Lafiya Lau Ukhteey..” Turo baki na yi, na ce “Ni ba y’ar uwarka ba ce..” ware idonsa ya yi ka’dan ya furta “Then ke mecece?” Sunkuyar da kai na na yi ina wasa da yatsun hannuna. Ustaz bai bar kallona ba don ina ‘d’agowa muke sake ha’da ido da shi. “Amsa min mana ke mecece? Tunda kin ce ba kya so na, ni yanzu kallon k’anwa nake miki..” Idona ne ya kawo ruwa na zuba masa idanun nawa da naga ya k’ank’ance nasa idon ya saka cikin nawa ya Kuma lumshe su. Cikin wata irin murya ya furta “Matsayin Yayan ma ba zaki bani ba kenan?” D’aga kai na yi. Ya yi dariya sosai har wushiryarsa na bayyana ya ce “Shikkenan nagode. Matsayin me zaki ba ni? Gaya min AYSHA?” Mutsu-mutsu na fara yi shi kuma ganin hakan bai saka ya d’auke idonsa ba. Kallona yake kawai yana murmushi yana kuma kurb’ar ruwan zob’onsa. “Ba zaki gaya min ba? Ai shikkenan bari na tashi na tafi Habibteey na jira na, na gode da girki ya yi da’di sosai mijinki ya ji da’dinsa Wallahi na masa murna. Nima Allah yasa dai Habibteey ta iya girki…” Turo bakina na yi na furta “Ni ka daina min zancen zabiyar nan…” ware idonsa ya yi yana furta “Habibteeyn ce zabiya? Lallai ma, to idan ita zabiya ce ke kuma mecece?” Ban san sanda na harareshi ba. Na furta “Allah ya sawwake ni Ai fari na ba irin nata ba ne. Fari na yafi nata kyau…” Ya tab’e baki yana dariya ya ce “Ko dai kishi ne? Idan banda haka kiga yarinya zubin larabawa ki ha’da kanki da ita. Zan tafi ta ce ma
Na gaisheki, amma kafin na tafi ina son na san matsayina sannan don Allah a min alfarma ki halarci event ‘dinmu ko guda ‘d’aya ne….” “Wallahi ba zani ba…” Na furta da sauri, har muryata na sark’e wa saboda tsabar takaici da bak’in cikin da zuciyata take ciki. Na lura ba k’aramin so yake mata ba kuma duk ni na jawowa kai na. Da sauri na fice daga ‘dakin ina sake fa’din “Ba zan je ba, sai kace wata mara zuciya…” Ban san sanda hawaye ya dinga rigegeniya a kan fuskata ba…
Ranar kam ba barcin da ya ‘daukeni, ko b’arawon ma hak’ura ya yi ya k’yaleni.

Da safe kam da ciwon kai na tashi. Kuma ko shara ban yi ba. Ina kwance a ‘d’aki Anty Khadija ta shigo tana kallona ta ce “AYSHA kin tashi, naga yau ko fitowa ba ki yi ba. Ki je in ji Yayanki.” Ban amsa mata ba, don haka kawai na samu kaina da k’uncin zuciya da jin haushin kowa ma. Na mik’e da rigar Barcin da take jikina na fita parlorn. Kaina ko gyara babu. Idona ya yi k’ozai-k’ozai.

Zuba min ido Yaya Muhd ya yi kafin ya furta “Ke baiwar Allah, lafiya kike? Kinga yarda kika dawo kuwa?” Kallonsa kawai nake ban amsa ba ganin yarda yake walainiya cikin sabuwar shadda fara k’al da ita. Ya tab’e baki ganin bani da niyyar amsawa ya ce “Allah ya kawo sauk’i, ke Khadija mu je na sauke ki a asibitin tunda ita bata shirya ba, balle ta raka ki, ni zan wuce wajen d’aurin auren Ustaz… Hararar gefen ido kawai nake watsa masa, ina ganin Ya Muhd d’in kamar wani gagarumin mak’iyina. Ganin ba zan amsa ba ina kallo Suka fice shi da matarsa suka rufo min k’ofa…

Na cusa hannuna cikin gashin kaina ina jin zuciyata na wata irin suya. Hawayen ma k’in zubowa suka yi. Kawai wani irin kuka nake na zuci. Ban san iya lokacin da na ‘d’auka a kwance a wajen ba, sai ji na yi wata ta yi k’ara na duba naga msg d’in Ustaz ne ya shigo wayata. Tsaki na zuba kamar ba zan karanta ba sai dai na bu’de sai naga ya saka “Alhamdulillah an ‘d’aura aure na, ina jiran fatan alheri daga k’anwata…..

Duum naji na daina ji da gani…
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: Hello! We are Tinysteps _ng do well by joining our group for updates on our unique kid’s dress back to school supplies toys and lots more

https://chat.whatsapp.com/FuUV3xjAcKgDaquGHnOnjw

https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ

NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎

𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️

Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

Arewabooks @nazeefah

https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ

Wattpad@Nazeefah381

08033748387.

★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 14

14…..

Tun daga kwanyata nake jin wani irin zafi, har k’asan zuciyata. Jikina ya yi sanyi sosai kukan ma ya kasa zuwa sai wani b’acin rai nake ji mai dugunzuma zuciya, ya raunata gabban jiki. Da k’yar na sulale na zame na kwanta a k’asan carpet ina lumshe idona. Tafarfasar da zuciyata take yi yasa na dinga jin kai na yana neman yin tsawa. Gashin kaina na burkita gaba d’aya ina jan gashin da k’arfi kamar shi ya min laifin. Kuka nake son yi amma kukan ya k’i zuwa. Rigar barci ce a jikina ban kuma damu da na cireta ba, don bata wankan nake ba. Sai yanzu na ji ina jin haushin biyayyar da na yiwa Mameey, kamar na cuci kai na kamar ni na jawowa kai na.

Ina kwancen cikin tafasar zuciya idanu na a kulle. Na ji kamar wani na tsaye a kai na. Da k’yar na dinga bu’de lumsassun idanuna sai na ga Ustaz ne a tsaye sake mayar da idon na yi na kulle don ina tunanin imagination d’in da na saba ne.

Daf da ni na dinga jin k’amshin mayataccen turarensa, don haka na ware idona sosai na zuba su a kansa. Yana zaune daf da ni idanunsa a kaina yana sakar min murmushi. Da sauri na mik’e cikin razana ina neman ko Hijab ne da zan suturce jikina don rigar barci ce a jikina itama iya gwiwa mai santsin gaske, sanda suka tafi na ji abin duniya ya min zafi ban san sanda na wancakalar da Hijabin can gefe ba. Hijabin yana daga can bakin k’ofa. Ga shi sam ba zan iya tashi ba. Na takure gefe guda ina rufe jikina duk da na san ba abinda bai gani ba, don ban san tsawon wani lokaci ya ‘d’auka a wajen ba. Murya a sark’e na furta “Ya zaka shigo min haka? Ba sallama ka bani Hijab ‘dina…” Still kallona yake yana murmushi kawai bai kuma mik’o min Hijab d’in ba. “Please Ustaz, ka bani Hijab ‘dina….” Na furta kamar na yi kuka. Muryarsa a sark’e ya lumshe ido… ya furta “Idan na k’i fa?” A tunzire na furta “Amma dai ka san haramun kake kalla ko?” Sake k’ura min ido ya yi kafin murya can k’asa ya furta “Da jikin da Mai jikin yau duk mallaki na ne, Matar Ustazunta…” wani irin ware ido na yi don ni duk ban fuskanci manufarsa ba. “Tashi ki ‘dau Hijabin naki…bari na rufe ido na..” Ya fa’da yana rufe idon nasa. Ban san sanda na wani irin mik’ewa da sauri ba don ‘d’aukar Hijabin, sai ji na yi kawai ya jawo ni na fa’do jikinsa ya saka hannu ya rungumeni sosai yana sakin ajiyar zuciya. Idona a waje nake furta Ustaz me ye haka? Ina matar taka?” “D’aya matar tawa tana gidansu Aysha, ga uwargidan anan.” Ya fa’da min cikin wata murya a kunnena. Da sauri na wani kalar Zillo na bar jikinsa ina kallo ya yi baya ya jingina da kujera idanunsa a lumshe yana sakin ajiyar zuciya… ni kuwa kallonsa kawai nake ina mamakin jin abinda ya ce da gaske an ‘d’aura mana aure shi? Kuma mu biyu da wata. Duk da na yi farin ciki amma kishi bai barni na bayyana farin cikin ba. Zuciyata na sama da k’asa na dinga kallonsa still idonsa a lumshe.. na furta “Wai da gaske aurena aka ‘d’aura ni da kai da wata kuma?” Idanunsa a lumshen ya ‘d’aga kai. A zafafe na ce “Tab’di! Ni Allah ban ce maka ina son mai mata ba…” “Aysha bana son surutu, ki tashi ki shirya mu je gidanku, Abba yana jiranki abokai na suna jira su ga matata za su koma garuruwansu. Ba lallai ku sake ha’duwa ba sai lokacin tariya.” Ya fa’da yana mik’o min wata leda mai kyan gaske. Ledar na bi da kallo ina amsa ya jawo ni jikinsa. Kissing ‘din lips ‘dina ya yi ka’dan yana jan karan hancina ya furta “Am sorry for this, na da’de ina jiran wannan ranar. Sai ga shi Allah ya bani ku ku biyu… “ Turo baki na na yi cikin matuk’ar jin kunya na sauka daga jikinsa. “Wa yace ki sauka? Kin san dai ba haramun ba ne ko?” “Ni dai bana so, ka je wajen waccan matar.” Na fa’da idona na zubar da hawaye. Murmushi ya yi yana furta “Don kuwa baki ga yarda ta yi kyau ba, ta yi kwalliya sai zabga wani irin k’amshi take mai sanya tunani a rai. Ke kuwa ko wankan bana jin yau kin yi, saboda kina
Cikin tashin hankalin kin yi rashin santalelen saurayi irina ko?” Turo baki na yi na shige ciki da sauri. Ina jin sautin murmushin Ustaz.
Chapter 19 · 0% Book details