Sashe 2
Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun a shagon ta saka min d’aya daga cikin dogayen hijabs d’in da aka d’inka min. Ta Kuma saka sabon nik’ab. Farin ciki ne ya cika zuciyata don ni kaina ina son yin shigar da dinga suturce jikina musamman tuni na gano
Na fara shiga sahun y’an matanci.
Muka dawo gida. Umma da su Yaya suna zaune suka bi mu da kallo baki sake, don kuwa na d’age Nik’ab d’in ina kallonsu ina murmushi. Mami itama dariya take tana bin su da kallo. “Lokaci ya yi da AYSHA zata dinga suturce jikinta ba don komai ba sabida bana son wani ya min shigar sauri. AYSHA ba zata yi aure ba sai ta yi masters, don haka har fuskarta ban amince ta bayyanata a waje wani ya gani ba……”
Ga duk mai son bibiyar littafin nan don Allah ya shiga link d’in nan don ba lallai na jure yawon tafiya group group yin posting ba. Abin da yawa Nagode…🤗
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NAGA RAYUWA♥︎♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 1★
Wannan page kacokam d’insa sadaukarwa ne ga members na MIKIYA WRITERS…
★★★★★★★★★★★★★★
Yau ne k’arshen shagalin da ake gudanarwa a ranakun bikin aurena, yau ne dinner party wacce aka shirya ta ta mata zalla a Amani Event center.
Ban ha’da dinner ta da maza ba kasancewar daga ni har angon ustazai da bama son gurb’ata bikinmu da abubuwan da suka sab’awa shari’a da Addinin musulunci. Neman albarkar auren kawai muke ba neman suna a duniyar social media ba, don haka bikin nawa ya zama kamar lami miya ba nama saboda rashin warwasawa da na k’i bari y’an mata su yi. Asalima ko ki’da baa saka ba sai ranar kamu ne ma aka saka ki’dan k’warya shima na hana kowa ya yi vedio gudun ya’da b’arna a bayan k’asa. Hakan da na yi ya burge mutane da dama yayin da wasu suke ganin tsabar iyayine da son a sani ba wai addini ba. Ban da mu ba don na san Allah da zuciya yake aiki. Kuma mahaifina ya yi farin ciki da hakan sosai musamman ganin k’ank’antar shekaruna bai saka na ajiye addini da koyarwar Manzon Allah ba.
Hankalina gaba d’aya ba ya wajen dinnerr duk da ina tsintar wa’azin da Malama Zainab Jafar take yi a wajen Dinnerr ka’dan-ka’dan. Farin cikin da nake ciki ne ya yi min yawa sanin cewa yau zan angwance da masoyina wanda nake mafarkin kasancewa matarsa a koda yaushe. Ji nake kamar na jawo lokaci a tashi daga dinnerr ko ma koma gida mu je mu shirya a sada ni da gidan Mijina wanda nake matuk’ar d’oki shauk’i da son gani. Tabbas fuskata kawai zaka kalla ka tabbatar da zakwa’din da zuciyata take ciki.
Duk da gefe guda na zuciyar tawa a sanyaye yake da kuma rauni wanda zan iya cewa ina jin sa har k’asan raina ba na komai ba ne sai na rabuwa da gidan mu da Ahalin da suke cikinsa. Ina son iyayena kamar yarda zuciyata bata son rabuwa da Yayyena maza da na kasance mace k’wal a cikinsu.
Ashe ban sani ba wayo a kai min daga wajen Dinnerr zaa kai ni gidan Mijina ba don komai ba sai don an san yanayin shak’uwata da Abbu a lokacin rabuwarmu tabbas sai mun saka jama’a kuka, musamman kuma kada Yayyena maza suji labari.
Mamana da Mamina suna wajen su sun halarci wajen Dinnerr don haka bayan tashi daga dinnerr suka zame suma ban sake ganinsu ba sai jin hannun Aunty Sharifa na yi tana fa’din “Tashi Aysha mu je daga nan sai gidan Mijinki kuma shikkenan Aysha ta girma.” Sai sannan zuciyata ta sake tsinkewa fargaba ta shige ni sanin cewa da na yi daga nan sai gidan Mijina shikkenan ana nufin na yi sallama da iyayena? Idanuna na zubawa Aunty Sharifa murya a raunane na ce “Mami na fa..” “Mami ta tafi gida Aysha ba zata iya ganin kukan ki ba..” Jikina ne ya yi sanyi don tun safiyar ranar na lura da rashin walwalar Mami duk da k’ok’arin dannewa da take, amma hakan bai b’uya a cikin k’wayar idanunta da suka tara ruwa ba. Ni na san Mami bata son wannan auren don dai ba yarda zata yi ne a matsayin ta na marik’iyata kawai kuma kishiyar uwa ba wacce ta haife ni ba. Shi yasa bata da damar da zata nuna hakan.
Wata ajiyar zuciya na saki da na hango Mamina na tahowa fuskarta d’auke da damuwa sai dai tana k’ok’arin dannewa wajen sakin murmushi ta iso wajen. Ta zare hannuna daga na cikin Aunty Sharifa ta maye da nata ta ja ni ba tare da ta yi magana ba muka wuce. Hakan da mutane suka gani yasa suka biyo mu wasu da yawa a wajen Mamina ta burgesu yayin da wasu na san ba mamaki abinda ta yi d’in su kira shi da iyayi.
Mamina da kanta ta shigar da ni d’akin aurena, hannuna damk’e cikin nata tana gaya min addu’oin da zan yi a cikin kunne na. Na lumshe ido ina fa’dar addu’ar da duk da na iya ta a yau saboda raunin zuciya sai na ji ta b’ace min b’at. Lokacin tafiya na yi wani kuka ya kufecewa Mami ta rungumeni ina kuka tana kuka da k’yar mutane suka lallashemu aka samu aka b’anb’are Mami daga jikina aka fita da ita. Kukan na sake ruhshewa dashi ba wanda ya yi mamaki don an san shak’uwar da take tsakaninmu da Mamina.
Haka ina ji ina gani kowa ya tafi daga gidan aka bar ni ni ka’dai kamar mayya. Sai sannan fargaba ta sake shiga jikina saboda ina da tsoro musamman na san gidan babban gaske ne. Tun ina saka ran shigowar ango har na saduda na yaye mayafin dake jikina zuciyata cike da mamakin ko me ya hanashi shigowa haka. Har na d’au wayata zan kira shi sai na ji ina jin kunya kada ya ce har na matsu da ganinsa na kira shi don haka sai na mayar da wayar kawai na ajiye na cigaba da kewaye d’akin da idona, wani irin farin ciki ya ratsani ganin irin namijin k’ok’arin da iyayena suka yi don su fitar da ni kunya.
Sai sha biyun dare sannan na dinga jin takunsa kamar daga corridor hakan yasa na yi saurin jan mayafi na na suturce jikina.
Daga jin yarda yanayin bugun zuciyata ya sauya na san shi ya shigo jikina kuma ya ba ni ni yake kallo, amma ko me ya hana shi k’arasawa inda nake. Ta cikin mayafi na dinga lek’ashi sanye yake cikin wata irin Alkyabba mai kyau da santsi kalar blue black da ta amshi farar fatarsa. Saman jallabiyar Alkyabba ce golden kamar yarda dai ya saba shigarsa a kullun yauma hakan ne. Kansa da hula mai shegen kyan tsiya wacce hausawa suke cewa Tashi ka fiye naci sai dai wannan mai tsadar ce. Tuni d’akin ya baje da wani irin k’amshin turaruka da ya danne nawa da na wutan da aka saka a d’akin. Kana jin k’amshin turaren zaka san mai tsada ne na masifa…
Sai da na kai idona kan fuskarsa sannan gaba na ya yi wani irin fa’duwa ganin yarda fuskarsa take a ha’de murtuk kamar bai tab’a dariya ba. Kamar ba Ustazuna mai yawan fara’a ba. Me zai saka ya ha’de rai a wannan daren da yafi ni zakwad’in zuwansa? Duk da dama ba ma’abocin dariya da k’yakyatawa bane amma ma’abocin murmushi ne don ya ce dariya na rage imanin Mumini.
Ganin ya fara taku zuwa inda nake yasa na sake jan mayafi na k’udundune fuskata don ban shirya amsa sunan mara kunya a wajen Ustazuna ba.
Yanayin takunsa yanayin yarda bugun zuciyata ke sauyawa da k’arfin gaske don na san dai ba mamaki yau Ustaz ya kai min runguma abinda muka da’de muna mafarki don da gani har shi na san mun yi dauriya…
“AYSHA!” Ya fa’da cikin jarumar muryarsa da take bayyana kasantuwarsa Namijin gaske..
Mamaki ne ya kusan kasheni jin a yau ya ambaci sunana gatsau ba wani sakayawa kamar yarda ya saba kira na da “Eesha ko ya ce Aysha ta..” Duk da haka ban yi nawar d’agowa ba na zuba masa ido ina kallon yarda yake kallona fuskarsa a ha’de ya mik’a min takardar hannunsa tabbas yanayinsa ya firgita ni…
“Ungo wannan.” Ya fa’da da wata irin shak’akkiyar murya, yana d’auke kallonsa daga gani na. Leda ce ya mik’a min. Daga haka ya juya ya fice a zatona zuwa zai yi shirya ya dawo. Duk da zuciyarta na gaya min akwai matsala ba haka Ustazuna ya kamata ya tare ni ba ni da nayi zaton runguma da kyakykyawan kiss da na da’de ina mafarki…. Ko dai na masa wani laifi ne da ban sani ba?
Ajiyar zuciya na saki ina jan ledar da sauri. K’amshin kazar Yahuza suya ya dake ni da Ice cream masu sanyi. Jikina har rawa yake don idan ban manta ba rabona da abinci tun safiyar ranar don haka kawai sai na samu kai na da fara cin kazar na sha ice cream d’in. Na saka hannu na jawo leda zan d’au lemo idona ya kai kan wata farar enveloped. A zatona mantawa ya yi don haka ban ma bu’de ba na ajiye a gefe ina jan kwalin exotic na fara d’addaka shi a cikina. Na tattare kayan idona ya sake sauka kan enveloped da a bayansa na ga sunana b’aro b’aro. AYSHA IMAM KHALIL… murmushi na saki ina tunanin ko wata kyauta Ustaz d’in ya bani don haka na jawo da sauri na farke enveloped d’in da yake ta zuba k’amshin turarensa.
𝒜𝓈𝓈𝒶𝓁𝒶𝓂𝓊 𝒶𝓁𝒶𝒾𝓀𝓊𝓂.... 𝒩𝒾 𝒜𝒽𝓂𝒶𝒹 𝒮𝓊𝓁𝒶𝒾𝓂𝒶𝓃 𝒮𝒶ℯℯ𝒹 𝓃𝒶 𝓈𝒶𝓀𝒾 𝓂𝒶𝓉𝒶𝓉𝒶 𝒜𝓎𝓈𝒽𝒶 ℐ𝓂𝒶𝓂 𝒦𝒽𝒶𝓁𝒾𝓁 𝓈𝒶𝓀𝒾 𝒹𝒶𝓎𝒶 𝒷𝒶𝓉𝒶 𝒹𝒶 𝒾𝒹𝒹𝒶𝓉𝒶 𝒾𝒹𝒶𝓃 𝓉𝒶 𝓈𝒶𝓂𝓊 𝓂𝒾𝒿𝒾 𝓉𝒶 𝓎𝒾 𝒶𝓊𝓇ℯ......
Kasa k’arasawa na yi saboda yarda na ji numfashi na yana neman d’aukewa na dinga ware ido ina jin zuciyata na wani irin bugu..