Sashe 8
Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duum haka na ji maganar Ustaz ta min saukar bazata a kunnena. Na sunkuyar da kaina ina mamakin yarda shi Sam ba ya Jin kunyar fa’dar duk abinda ke bakinsa. “Ina Jin ki…” Ya fa’da yana sake sanya idanunsa cikin nawa. Muryata na rawa na furta “I can’t..” kafin na yi aune hawaye ya fara zubowa a fuskata don har ga Allah ya fara takura min. Shi bai san duk sanda ya rutsa ni ba, Wani irin yanayi nake shiga mai wuyar kwatance… “Kuka ki ke? Daga tambaya?” Ya furta muryarsa a k’asa sosai. Na sake runtse idona na k’ara k’arfin kukan nawa. “Ki min shiru.. tunda ba amsa just wipe your tears..” ya fa’da yana mik’a min handky d’insa. Amsa na yi na shiga goge idon nawa amma hawayen still basu tsaya ba. “Ki tsayar da hawayen nan yanzun nan bana son shagwab’a. Me aka miki daga cewa ki yi karatu..” Ya furta a hankali cikin wani husky voice da zan iya cewa yana sane yake min magana da ita.. “Zan gaya miki Laa Haya’u fiddeeni, idan baki tsaya kin koya ba ta ina zaki iya? Ko ni ne ba kya son na koya miki?” Da sauri na d’aga kai, murmushi ya saki mai kyan gaske.. yana furta “Why?” Yana shigar da idonsa cikin nawa “Gaya min dalili sai na k’yaleki..” Shiru na masa idona a k’asa ina cigaba da wasa da handky d’in hannunsa.. ina ji ya saki ajiyar zuciya bayan ya gama k’are min kallo tas, don a jikina na ji ni yake kallo… “Dole zai fito muku a exam don haka dole ki saurareni na miki gamsashshen bayani. Kuma bana son ki rufe min ido. Ki tsaya ki kalleni kamar yarda kowace d’aliba take sauraran malaminta idan yana mata karatu. Tunda ni ba saurayinki ba ne, balle ki ce kina jin kunyata…..AYSHA..” Na d’ago da niyyar kallon nasa sai dai sam idanuna sun kasa ba ni dama. “Kalleni ki saurareni..” Na girgiza kai “Don Allah Ustaz ka yi hak’uri zan je Asma ta koya min, inda ban gane ba..” ta gefen ido naga ya tab’e baki. “Ban yarda ba Aysha, na Riga na d’au alk’awari zan karantar da ku don haka dolena ne na yi miki yarda na yiwa kowa..” “To ka ha’da ni da wani Malamin.” Na furta muryata na rawa. “Saboda ni surikin ki ne? Ko saurayin ki?. Ruwa uku ne yake fitowa daga al’aura akwai Maniyyi, akwai wadiyyi akwai maziyyi kina ji na? Maniyyi shine ruwan da yake fitowa mutum yayin babbar sha’awa, saduwar aure wato jima’i….” Ban san sanda na kai kaina bakin k’ofa ba, na fice da sauri don na lura Ustaz so yake kawai ya kashe ni da salonsa. Saboda wani irin abu da na dinga ji a jikina. Ina ji yana k’wala min kira amma na k’i komawa na shige wani lungu ina mayar da haki. Ina goge hawayena da handky d’insa da ya cika da k’amshin turarensa sai sannan ma na lura da handkerchief d’in. Na cusa shi cikin aljihun hijab d’ina ina mayar da haki. In dai zan shiga aji a haka dole ne ma a fuskanci bana cikin nutsuwa don haka kawai na fice daga makarantar don ba zan iya sake ha’da ido da Ustaz ba, a dai ranar yau…
Ina zuwa gida d’aki kawai na shige ba tare da na bari su Mami da suke kitchen su ganni ba. Na shige toilet saboda wani irin fitsari da na ji ya matseni. Ban yi mamakin ganin discharge mai yawan gaske a undies d’ina ba. Kwanciya na yi saman gadon ina sakin haki tare da shak’ar k’amshin Ustaz da yake jikin Handky d’in. Murmushi nake saki ni ka’dai ina tuna drammerr da muka sha da Ustaz d’in. Gwara ya dokeni akan na zauna yana min wannan karatun nasa… na raya a zuciyata.
A kwancen nake har 6:30. Daidai lokacin da na ji shigowar Mami da Asma. Tana fa’din “Wani irin ta taho gida, ni ban ganta ba amma bari na duba d’akinta.” Turus ta yi tana kallona “Ke lafiyarki kika taho daga Islamiyya tun kafin a tashi.” Lumshe idona da ya yi nauyi na yi na furta “‘Mami bana jin da’di ne.” Ta saki ranta tana kallon Asma da take tsaye da Jakata a hannu. “Shine zaki shigo d’aki ki kwanta? Anan wa ya san baki da lafiya?” Ta yi tsaki tana ficewa daga d’akin “Dama ki taso ki sha magani yanzunnan, don na san rashin son magani ne yasa kika k’ulle kanki a d’aki.” Asma Mami na fita ta tuntsire da dariya “Daga zuwa wajen Ustaz kuma sai ki gudo gida.. ko ya fasa miki sirrin zuciyarsa ne?” Na wurga mata harara “Mhmn” ta furta tana zama gefen gadon “Ni sai na ji ma d’akin kamar k’amshin ustaz d’in yake..” Da sauri na danne handky d’insa da k’afata ina furta “A’a Ustaz d’in ne na b’oye ba k’amshinsa ba, y’ar rainin hankali kawai…” “Zaki ga y’ar rainin hankali, Dama ya ce na gaya miki gobe kada yaga k’afarki cikin ajinsa..” “Ta fi Nono fari wallahi, Sai na canja aji..” Asma ta tsira min ido tana furta “Ke ce zaki iya barin Ibn kaseer? Ki dai ba shi hak’uri kawai ki koma. Wai me ya miki?” Zama na yi na bata labari ta dinga tuntsira dariya tana kifawa ta furta “Wallahi Aysha mutumin nan sonki yake, shi kuma tasa salon soyayyar kenan, kan bala’i Amma fa ya burgeni…” kallo na watsa mata ina nuna mata k’ofa. “Maza ki ta surutu Mami ta ji ta tsireni, ni ba wani so na da yake.. kawai dai ya lura ina jin kunyarsa ne..” “Kema aI sonsa kike tunda kina jin kunyar ya miki irin wannan karatun…” Ta furta tana dariya duka na kai mata ina jan hannunta na furta “Fice min daga d’aki Malama..” Ta fita tana furta “Ko baki ce ba, amma wallahi kun dace wai! Ai kuwa zuciyar y’an matan ajin nan zata buga don yau ma baki ji zagin da kika sha ba, da kika bi shi office..” Na tab’e bakina ina furta “Y’an wahala, su suka ga zasu iya. Don Allah Asma tafi gida kawai..” ta fita tana murmushi.. Na zauna ina nawa murmushin nima. Ina ma ya furta yana so na da nafi kowace mace sa’a…
Kashegari ma k’in zuwa makarantar na yi na fake da bani da lafiya don sam ban ji zan iya zuwa na kalleshi ba. Tsawon kwana uku ina k’aryar ciwo kullum Asma ta dawo sai ta biyo gida ta koya min abinda aka yi. Ranar laraba ta shigo d’akina tana murmushi ta ce “Aysha yau fa Ustaz ya kasa dauriya, sai da ya tambayeni ina kike bayan ya kira ni office d’insa. Na ce masa baki da lafiya baki ga murmushin da ya saki ba na irin na raina masa hankali ya furta “Ki gaya mata ranar asabar ta dawo makaranta…” Murmushi kawai na saki na ce “Allah ya kai mu. Asma ta fita tana furta “Ke mutumin nan da gaske ya faller kawai furtawa ne bai yi ba..” samun kai na na yi da sakin murmushin nima ina furta “Allah yasa.
Kashegari ya kasance ranar alhamis ce, na tashi da wuri na yi shirin makaranta don Exams zamu fara third term SS 2.
A gaggauce na sauko daga sama ganin lokaci ya ja. Na isa kitchen wajen Umma da Mami da na tabbatar suna kitchen d’in. Saboda koda yaushe tare suke girkin su. Wani kallo Mami ta zuba min mai cike da zargi da tuhuma, na lura kwana biyu irin kallon da take min kenan. Na yi k’asa da kai na ina sake gaishesu. Na mik’e ina cewa sai na dawo bayan sun amsa gaisuwar. “Abincin fa?” Mami ta fa’da tana tsare da kallo. Na d’an girgiza kai ina turo baki na ce “Mami, yau bana son yin breakfast fast…” “Wasa kenan, wuce Malama ki ha’da tea ki sha ga chips nan ki cinye tas kafin ki wuce… ina lura da ke kwana biyu ba wani abincin kirki kike ci ba, jiki kamar sillen kara… Uban me ke damunki?” Da sauri na furta “Allah bakomai Mami..” K’wafa ta yi, ta cigaba da aikinta kafin ta furta “Ina fatan Bakoman ta zama bakomai d’in…” Umma da take jin mu dariya ta yi tana furta “Ke ma dai Fateema, kamar AYSHA ce sai an tsaya cewa ta ci abinci sai ka ce yarinya, idan kika ga bata ci ba ta k’oshi ne…” Mami a tunzire ta furta “To Ayshan nawa take? Shekara sha bakwai Ai har yanzu yarinya ce, ko yanzu ta kama d’aukarta zan yi na cafeta na goyata da zani. Gaskiya a daina jawo mata girma balle ido ya dawo kanta…” Umma d’auke kanta ta yi tana furta “Allah ya taimaka, aure dai idan lokacinsa ya yi ko an jawo girma ko baa jawo ba yinsa za’a yi…” Mami wani kallo ta yiwa Umma sai kuma ta furta “Allah Umma kada ki fa’di maganar nan wajen Abbansu ya ji, don wallahi ko sama da k’asa zata ha’de a shekaru dai irin na Aysha ba zan bari a mata aure ba, sai na ‘dauketa mu bar garin ina dalili?” Ni dai ina daga gefe dariya tana son kama ni, koda yaushe drammerr Umma da Mami na kenan.
Na gama kurb’ar tea d’in a gaggauce na fice ina amsa addu’ar da suke min da ameen..
Ina zaune a ajin mu na makarantar boko intercontinental nake zuwa.
Aka turo kira na daga office d’in principal. Ban wani damu ba sanin cewa ina da mik’amin da zaa iya nemane koda yaushe.