← Book details Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 30

Sashe 3

Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tabbas NAGA RAYUWA Me yake shirin faruwa da ni ne? Saki a daren aurena daren da muke d’oki da zakwa’din zuwansa ni da mijina ya da’de yana gaya min yana jiran ranar da zai rungumeni dtazo saboda kiyeye dokar Ubangiji. Me na yiwa Ustazuna ya sake ni? Na shiga uku!! Haka na furta a zuciyata..

To fa! ko me AYSHA ta yiwa Ustaz Ahmad ya zabga mata saki a daren aurenta? Duka yana cikin littafin NAGA RAYUWA da zai dinga zuwa muku daga Alk’alamin…..

𝒥𝒾𝓀𝒶𝓇 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NAGA RAYUWA♥︎♥︎♥︎

𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

Arewabooks @nazeefah

Wattpad@Nazeefah381

08033748387.

★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 2.

★…..✍🏽

Kuka ne sosai ya kufce min, irin kukan nan da kake jin d’acinsa har k’asan ranka. Kuka mai sauti da Amon muryar karaya a cikinsa. Me Na masa? Shine tambayar da nake wa kaina na kuma kasa lalubo amsar. Abinda zuciyata take gaya min nake k’aryatawa ko nak’i ko na so dole ne na gasagata zuciyar tawa dole Butulcin d’a namiji ne ya biyo ta kai na. Ko kuma ya yi haka ne don ya gwada mizanin soyayyarsa a zuciyata. Amma ya rasa ta hanyar da zai gwada sai ta kalmar saki? Kai abinda kamar wuya Ustaz da wayonsa ba zai yi wasa da saki ba Halak d’in da ya san Allah baya so, kuma idan aka aikata shi ar’ashi tana girgiza. Dole ba don na so ba na amince da shawarar da zuciyata take ba ni, na danganawa sashensa na je na tambayeshi abinda ke faruwa…

Tsam na mik’e na shiga laliben sashennasa, kasancewata bak’uwa a gidan bai saka na sha wahalar gane k’ofar sashen nasa ba. Daga can corridor tsakanin k’ofar da zata kai ka nawa sashen. A hankali na tura k’ofar na shiga. Shiru babban parlorn nasa baka jin k’arar komai sai na A.c da take ta aiki ba ji ba gani. Fitulun wajen ma a kashe suke. Karatun k’ur’ani ne kawai yake tashi a parlourn cikin k’ira’ar shureim. Na gama zagaye parlorn da idona ban gan shi ba, don haka na isa k’ofa guda da take parlorn da na tabbatar nan ne d’akin nasa.

Yana zaune a gefen gadon daga k’asa saman sallaya ya kifa kansa a jikin gadon. Jin motsina ya saka shi d’aga kai. Wata irin fa’duwar gaba ce ta same ni ganin yarda idanunsa suka ka’da suka yi jawur kamar gaurashi. Idan ba idanu na ne suka min gizo ba sai naga kamar hawaye ne a kwance a k’asan idanun. Mayar da idonsa ya yi ya lumshe bai sake kallona ba alamu sun nuna baya son gani na.

Zuciyata a jagule tana wani irin bugu da k’arfin gaske na k’arasa wajensa. Zama na yi a gefen gadon murya cike da rauni na furta “Ustazuna, wata takarda na gani a cikin kayan da ka kawo, zuciyata ta kasa amincewa hannunka ne ya rubuta ta. Ban kuma fahimceka ba.”

Shiru kamar ba zai amsa ba, idanun dai still a lumshe daga inda nake ina ganin yarda k’irjinsa yake bugu. “Ustaz, magana fa nake.” “Taki ce.” Ya fa’da muryarsa a shak’e. Ido na waro ina furta “Saki Ustaz!” Ya bu’de idon nasa ya nutsasu cikin nawa, a hankali ya d’aga lab’b’ansa kamar baya so ya furta “K’warai kuwa AYSHA, don haka ki tabbata kin fice kin daga gida k’arfe bakwai na safe….”

Ina daga zaunen na dinga jin wani irin jiri yana d’ibana. “Ko zan san dalili?” Wannan karan madadin amsa min mik’ewa ya yi yana zabga tsaki ya furta “Ban sani ba…” Shiru na yi na lumshe idona ina hak’ilo da yak’i da b’acin ran da yake son dannen numfashi. “Tashi ki fita zan rufe k’ofata..” Ya furta yana nuna min k’ofa.. Ya fa’da yana juya min baya… Jikina a salub’e na mik’e ina jin kamar k’afarta wa ba Zata iya d’aukata ba saboda rawar da jikina yake yi na zallar tashin hankali. Da k’yar na ja jiki na isa bak’in k’ofar daidai lokacin da na jiyo ina kallon Ustaz ina cije leb’ena shima kallon nawa yake hawaye ba zuba daga idonsa. Na ja k’ofar da k’arfin gaske na fice daga d’akin.

Zuciyata har Tafasa take saboda tsananin b’acin rai. Na zauna a gefen gadona ina mayar da numfashi tabbas Uztaz ya cuceni a shekaruna sha takwas kacal ya mayar da ni k’aramar bazawara? Shin halaccin da zai yiwa Iyayena kenan? Tabbas ya amsa sunansa Butulu? Yanzu me Zan je na ce a gidan mu? Ya rasa irin sakin da zai yi min sai irin wannan na tozarci da wulak’anci saki a ranar aurenka daren amarcinka? Yaya mutane za su yiwa abin fassara? Dole ne a jefa min ayar tambaya musamman kowa da ya san Ustaz ya san Babban Malami na da ake watsa tafseer d’insa a gidajen sunna na t.v. Babban Malami ne da gwamnatin k’asa baki d’aya take ji da shi duk da dai ba wani shekaru ne da shi ba ba zai wuce shekaru 32 ba.

Toilet na shiga bayan da zuciyata ta tabbatar min ba ni da wanda zan fuskanta a wannan gab’ar sai Ubangiji. Don haka na yi alwala na fito na tada sallah akan daddumar da Abba ya bani d’azu da safe ita da Alk’ur’ani da Riga da Hijab na sallah farare tas har da carbi da wani turare mai k’amshin gaske, yana furta “AYSHA, kin ga wa’dannan sune garkuwarki a gidan miji idan kika rik’esu kin samu makamin k’are dangi.” Ina sallahr ina hawaye na kaiwa Allah kuka na, na bayyana masa rauni na na kuma rok’eshi ya shige min gaba a dukkan lamari na.”

Ban tashi daga sallaya ba sai k’arfe uku da naji kaina ya fara ciwo abin mamaki sai na ji na samu k’arfi da nutsuwar zuciya. Na ji komai ya faru gareni daga Allah yake duk da tabbas Ustaz ya cuceni. Abu guda nafi buk’ata a yanzu na ji dalilin sakin da ya yi min, sai dai na yi alk’awarin ni da kai na ba zan sake tambayarsa ba don ko don ganinsa bana yi.

Barci ne sosai ya d’auke ni, kasancewar garin sanyi ne dare yana tsawaita don haka sallar asuba sa daf da k’arfe shidda ake yi, shi yasa na samu barci sosai duk da ba wai zance na yi isashshe ba ne. Ina sallame sallahr ko kayan sallar ban cire ba na fice da su da sauri a jikina.

Shiru layin amma a haka na dinga tattaki har na je bakin titi. Allah kuma ya taimakeni na samu adaidaita sahu. “Shara’da phase 2 kawai nace masa.

Har k’ofar gidanmu ya ajiye ni ta hanyar kwatance da na masa.

Duk da a tsorace nake da ganin Abbana hakan bai hana ni shiga gidan da k’warin gwiwata ba. Y’an biki ko watsewa ba su yi ba, don wasu daga garuruwa daban daban suka zo. Sai dai gidan shiru da alama kowa gajiyar biki ta saka ana sallah an kwanta sai wa’danda suke aiki a bayan gidan ta can na dinga jin d’an hayaniya da sautin kwanuka na tashi.

Jama’ar da suke kwance a
Parlor wa’danda duk k’annen Mami na ne da na Umma na suka dinga bi na da kallon mamaki baki a sake. Anty Sharifa ta ce “Ke AYSHA lafiya?” Mami da fitowarta daga d’akinta kenan itama hangame bakin ta yi tana ware ido ta furta “Ni Fa’dima me Zan gani haka? Ke Aysha Uban me ya fito da ke da sassafe haka?” Ta fa’da tana jan hannuna hankali a tashe ta furta “Ai dama sai da na gayawa Abbanku kin yi k’ank’anta da aure, shekara sha bakwai don ko sha takwas d’in baki cika ba, yanzu haka wani bak’on al’amari kika gani da yafi k’arfinki yasa kika gudo?” Anty Sharifa k’anwar Umma ta ce “Ah haba! Sai kace ba y’ar yanzu ba, ai duk da take k’anwar Maza na san ta san me aure ya k’unsa ko da ta hanyar k’awaye da karance karancen littafine…” Mami ta d’an harareta “Me AYSHA ta sani? Karatun littafin take ita? Ko k’awayen arziki AYSHA bata da su balle su sanar da ita aure da abinda ya k’unsa…” Ta fa’da tana jan hannuna muka shige Uwar d’akinta.

Zaunar da ni ta yi a bakin gado, bayan ta koma ta rufe d’akin da key tana furta “Bana son saka ido da munafunci yanzu duk ido zai dawo kan ki, kema kin yi wauta Aysha. Me ya kai ki fitowa don kawai Mijinki ya kusanceki Ai shine auren muma duk haka ake mana da haka kuma kowa yake sabawa… kowace macen aure da kika gani haka ne yake faruwa da ita koda yaushe, don haka tun kafin sauran mutane da Ubanki su ji ki tashi maza naje na mayar da ke, bana son na ji komai wannan sirrinki ne ke da Mijinki. Maza tashi mu tafi kafin mutane su fara miki kallon mara wayo mai gudun
Miji.”

Hawaye ne suka fara zuba min, ganin ita Mami na inda take hange daban da abinda ya kawo ni gidan. Na turo bakina ina furta “Ni fa ba wannan bane, ko hannu bai rik’e min ba fa.”
Chapter 3 · 0% Book details