Sashe 5
Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina SS 2… al’amarin ya faru. Mun taso daga Islamiyya ni da k’awata Asma’u, muna tafe muna hira a hankali cikin nutsuwa. Ranar ganin ba kowa a layin sai na ‘dage hijabi na. Asma’u ta kalleni da mamaki ta ce “Yau kuma Aysha? Lallai kina son idan Mami ta ji labari har ni ta ha’da ta ci mutunci na kenan?” Tab’e baki na yi, ina yamutsa na fuska na ce “Ai layin ba kowa….kuma ma waye bai sanni a layin nan ba?” Cigaba ta yi da bani labarin wani series da ake yi a Mbc bollywood wanda na yi missing ban kalla ba, sabida girki da Mami ta saka ni a daidai lokacin.
Murmushi kawai nake saki… Zuciyata ce ta wani irin bugawa daidai lokacin da muka ha’da ido da shi yana tsaye a gefen wani gida da ake gini ba’a k’arasa ba…” Da sauri na ja nik’ab d’ina na mayar ina jin yarda sautin bugun zuciyatta ya tsananta. Tabbas na san fuskarsa a sunna t.v matashin Malamine da yake tafseer a duk azimi. Ba wanda bai san Ustaz Ahmad ba. Saboda yarda yake d’an gayu komansa mai kyau ne yana kuma ji da tashen Naira. Asma’u ta furta k’asa k’asa “Ke AYSHA kamar Dr. Ahmad sulaiman ko?” Ban amsa mata ba, k’irjina dai ya cigaba da bugu. Sam zuciyata kasa cigaba ta yi da saurarar labarin da Asma take bani saboda wani yanayi da na fa’da mai girman gaske..
Tabbas tunda nake ban tab’a ganin mutumin da jallabiyya ta yiwa kyau kamar wannan mutumin ba. Ga wani azababben k’amshin turarensa da ya maye wajen gaba d’aya. A kallon da na masa sai naga ashe har ya fi kyau a fili. Yana da haske sai dai ba sosai ba. Idanunsa farare tas kuma mayalwata. Cikakkiyar gira ce da shi da gashin ido kamar yarda gashin kansa yake cikakke kuma bak’i si’dik. Duka wannan na gani ne a guntun kallon da na masa.
Asma tana shiga gida nima na fa’da gidanmu da sauri tunda mak’ota muke da su. Shi kuma Ustaz gidan da yazo gidan yana kallon gidanmu.
Ban bari kowa ya ji shigowata ba na haye sama da sauri na shiga d’akina. Haka kawai nake don sake ganinsa don na san windown d’akina yana kallon gidan da yazo. Ina d’aga labulan kuwa na hango shi yana tsaye still suna magana da Lawal da ya kasance d’an mak’otan mu. Idanunsa na ga ya juyo yana kallon gidan mu kamar mai nazarin wani abu… Daidai lokacin Mami ta shigo tana k’wala min kira. Da sauri na saki labulan windown alamar rashin gaskiya bayyane k’uru k’uru a cikin idanuna. Ba ta yi min magana ba sai takowa da ta yi zuwa gaban windown ta d’aga labulan tana furta “Uban me kike kallo anan d’in?” Idanunta ya sauka akan Ustaz da sauri ta juyo tana kallona baki sake ta furta “Namiji kike kallo Aysha? To Uban me ya ha’da ki da shi?”
Hantar cikina ta ka’da… bakina na rawa na furta “Babu komai Mami….
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
Wancan group d’in ya cika Wanda Bai samu Shiga group 1 ba ya Shiga 2. Amma don Allah idan kana group 1 kada ka Shiga 2 don duk Abu d’aya ne.
A shiga group, ba Zan juri posting a kowane group ba, ba kuma Zan juri a dinga cewa Na tura daga farko ta private ba. Hankalinka kwance ka shiga group kawai. Nagode[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 5.
Mami ta zabga tsaki tana sakin labulan tana kallo na ta furta “Idan ma shi kike kallon, ki tsaya ki saurareni da kyau.” Ta fa’da tana jan kunnena “Koda wasa kada ki sake ki saka wani namiji a ranki, a yanzu dai kam don ko me zai faru ba zan bari a aurar da ke ba, sai na cika burina na kin zama wani abu a fannin ilimin boko.” D’aga kai na na yi, ina lumshe idona. Ta fice da sauri ina jin b’acin rai ma ya mantar da ita abinda ya kawo ta.
Bu’de idona na yi a hankali ina sakin ajiyar zuciya. Ba tare da damuwa ba na sake yaye labulan d’akin. Daidai lokacin da Ustaz ya d’ago yana sake kallon gidan mu, ban damu ba na tsaya na kalleshi sosai don na san ba zai ganni ba, glass d’in yana da duhu daga waje ba’a ganin wanda yake ciki.
Na saki ajiyar zuciya ina kallon sanda ya shiga motar sa yana sake bawa Lawal hannu suka yi misabiha. Ya ja motar ya bar wajen. “Allah ya yi halitta…” Na furta a hankali ina kai wa saman gado na zauna. Har a lokacin yanayin bugun zuciyata bai koma daidai ba.
Shikkenan na samu abin yi tun daga ranar da na gan shi, ban sake komawa daidai ba. Kullum cikin tunaninsa nake da burin sake ganinsa koda sau ‘d’aya ne a rayuwata.
Ranar da sati ya zagayo ranar wata lahadi still mun dawo Islamiyya da Asma’u kamar wancan lokacin. Asma ce take ta surutunta ni kuwa bakina shiru, don wani irin yanayi nake ji a zuciyata ga bugun zuciyartawa ya sauya. Muna doso layinmu na ji mayataccen k’amshin turarensa wanda ba zan tab’a mantawa ba. Da sauri na sauke Nik’ab d’in don kuwa na tabbatar shine duk da bayansa kawai na gani still sanye yake da jallabiya mai kyau brown kansa da hula tashi ka fiya nace mai tsadar. Muna doso ta inda suke zamu wuce don dole sai ta nan d’in na ji k’afafuna sun fara rawa kamar ba zasu d’aukeni ba. Duk da nik’ab ne a idanuna na ga ya ‘dago yana kallon inda muke sai kuma suka yi shiru da hirar da suke. Da k’yar na saita kaina na nutsu muka shige su. Sai da na shiga gate d’in gidanmu sannan na saki ajiyar zuciya a hankali ina furta “Ya rabbi! Me ke faruwa da ni ne?”
Bayan kwana biyu ina zaune a ajin mu ja Islamiyya. Aka aiko kirana. A matsayin da nake kai na shugabar makaranta na san ba wani abu bane don an aiko kirana d’in, amma wannan karan sai na ji zuciyata ta buga sosai. Ido na tsurawa mai kiran nawa. Har ya ji haushi ya furta “AYSHA magana fa nake.” Da sauri na amsa da “To gani nan.”
A Office d’in Headmaster na tsaya ina knocking a hankali. Muryar Malam d’in na ji yana furta “Bismillah Ayshatu…” Na yi sallama na shiga, k’amshin turarensa ya doso hancina har ban san sanda na ware ido ganin Ustaz a zaune ba idonsa akan wani littafi da ke hannunsa. Wallahi Allah ne ya yi ba zan fa’di ba, Saboda zallar rashin nutsuwa. Sunkuyar da kaina na yi ina wasa da yatsuna. Har Malam ya gama rubutunsa ya d’ago yana kallona “Gaisuwa fa Ayshatu?” Da sauri na juya na kalli Ustaz da ya yi kamar bai san da ni ba a wajen. “Ina yini?” Bai d’ago ba na ji dai ya masa murya a k’asa “Lafiya..” D’an tab’e bakina na yi duk da na ji haushinsa, na mayar da hankalina kan Malam. “Ki je maza ki sanar da duk ajujuwa akwai assembly idan an idar da sallah..” Na amsa da sauri don burina fita daga office d’in kafin halin da nake ciki ya bayyana…”
Haka kuwa aka yi, ana idar da sallah ba wanda ya tashi daga babban filin harabar makarantar. Kowa ya zauna ya kuma nutsu ana jiran fara assembly. Duka Malaman makarantar suna zaune sun kame akan kujerunsu. Mu kuma muna tsaye don lura da masu surutu. Wajen tsit baka jin saurin komai. Malam Kawu ne ya nuna ni da nufin nazo wajensa. Ina isa ya furta “Ki fara karatu, Yanzu Malam Babba zai zo.” Na mik’e na d’au speaker d’in ina fara karatu ya yi daidai da shigowarsu. K’asa kawai na yi da kai na na cigaba da karatuna kawai cikin muryar Shureim da na k’ware da karatu da ita. Ina kallo Ustaz kawai ya lumshe idonsa yana jijjiga k’afa a hankali.
Sai da nace sadak’allahul azeem sannan ya bu’de idon nasa ya sauke su a kaina. Ji na yi tsigar jikina ta tashi. Da k’yar na ja jiki na koma inda nake na zauna don kam ba zan juri tsayuwa ba.
Malam Ahmad ne ya fara jawabi da sanar da su babban cigaban da makaranta da ta samu na zuwan Ustaz Ahmad da son d’aukar wani darasi a makarantar…” Kabbara da ihu d’aliban suka saka cikin matuk’ar murna da farin ciki.
Bayan ajiye loudspeaker d’insa Malam Kawu ne ya d’auka ya ‘dan yi barkwancinsa sannan ya sanar da cewa ya barwa Ustaz abinda har zuwa sanda zai bar makarantar.” Ta cikin nik’ab na ware ido jin abinda ya ce don ajin Malam kawu nan ne ajin mu, gefe guda kuwa na zuciyata wani irin farin ciki ne mara misali a cikinta. Haka aka tashi zuciyar kowa cike da farin ciki. Ina ji y’an mata suna ta yaba Ustaz haka kawai sai na ji raina ya b’aci tsananin haushi ya shiga zuciyata, ban sani ba ashe wannan shine kishi.
Kashegari da wani irin ‘doki na yi shirin makaranta, karo na farko har da mutstsika Lipstick a lab’b’ana sai naga na yi kyau da sauri na saki nik’ab d’ina tun kafin Mami ta gan ni da jambaki ta min masifa.