← Book details Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 30

Sashe 14

Naga Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kashegari nima tashi na yi da azimin kawai na samu kai na da son yiwa Ustaz d’in girki, duk da ina ji a raina a ranar zan rok’e shi ya janye daga maganar aurena ko don dawo da farin cikin gidan mu, kuma Mami ta dawo gidan mijinta. Girkin na masa, Masa da sinasir sai miyar taushe na kuma yi kunun tsamiya da zob’o da ya ji kayan k’amshi. Haka kawai na ji gwara na masa abincin mu na gargajiya. Umma dai sai kallona take kafin ta gaji da shirun ta furta “AYSHA wa kike wa girki ne?” Kunyace ta kamani na ce “Umma cewa ya yi zai zo ya sha ruwa.” Gani na yi ta yi murmushi ta d’an’dana girkin da lemon ta girgiza kai ta furta “Kin yi k’ok’ari, sai ki ha’da masa da zogale tunda naga harkar gargajiya kika masa. Ko ke fa? Ki rabu da Mami zata dawo da ikon Allah, gobe ma Na ji Baffaninku suna za su je gidan…” Na d’aga kai kawai ba wai don zan janye maganar rabuwa da Ustaz ba da na shiryawa a yau.

Daidai lokacin da zai zo kuwa sai ga Yaya Ali ya shigo d’akina yana kallona ya furta “Bak’onki ya zo kandala.” Turo baki na yi ina fa’din “Kai Ya Ali me ye haka? Kai ma ya kamata ka yi aure ka bar gidan nan.” D’alle min baki ya yi yana furta sai ki aurar da ni, ashe dai kina son mutumin ji wani uban kwalliya da kika yi har da su jambaki?” Harararsa kawai na yi na shige na sauka k’asa. Kafin na je ma har Umma ta saka an kai masa abincin sitroom. Ina shiga yana zaune na same shi. Idonsa a lumshe sai dai daga yanayin fuskarsa na tabbatar akwai abinda ke damunsa. Sallamar da na yi bai saka ya bu’de idon ba ya dai amsa nima na ga haka ne ta hanyar d’aga lab’b’ansa da ya yi. Tsawon mintu biyu bai bu’de idon ba duk da a jikina na ji yana kallona da lumsassun idanun nasa. “Zuba min ruwan tea.ban sha ruwa ba dabino kawai na ci.” Ya fa’da still idanunsa a lumshe. A daburce na fara ha’da masa shayin. Ina shirin sake zuba sugar ya furta “Enough madam, wa ya gaya miki ana son maza su dinga shan zak’i sosai?” Ya fa’da yana ware idonsa ka’dan a kai na. Maik’on k’wallar ido yana k’arawa idonsa kyau. Hawaye naga sun d’an gangaro masa. Hakan ya saka jikina ya yi sanyi. Na ajiye cup d’in shayin a kan table da ke kusa da shi. “Na gode” ya furta cikin raunin muryar da ta saka har na ‘dago na kalleshi da sauri na ce “Kuka ka ke?” Ya ‘d’aga min kai. “Kuka nake AYSHA, dole na yi kuka me yasa ba kya so na? Kike wahalar da ni, kin san kalar azabar da kika bani a kwanakin nan, Sana’a na je yi k’asar mutane amma na zama sam bani da nutsuwar da zan gudanar da sana’ar na kira waya a kashe har na gaji na kira Abba. Amma still you don’t on your phone why? Me na miki da na yi deserving this kind of purnishment a wajenki? Kin san bana k’asar balle nazo na ji dalili. Ki gaya min gaskiya me ya faru kin daina so na ne?” Da sauri na d’aga kai ina kallon sanda ya matse tea cup d’in hannunsa duk da zafinsa na runtse idona. Sai na ji ya saki ajiyar zuciya ya ajiye cup d’in. Ya furta “Na gode AYSHA, amma may I know the reason?” Ji na yi na kasa b’oye masa na ce “Mami na bata son relationships d’inmu da kai, ta fi so na yi karatu…” “Maminki?” Ya furta yana kallona kallon da yasa na ji wani mugun tausayinsa ya kamani. Sai naga ya cije leb’ensa ya mik’e kawai ya ajiye cup d’in ya fice. Ji na yi kamar na bi shi amma k’afafuna sun kasa sai b’alle war hawaye na ji daga cikin idona. Ai kuwa na saka kukan sosai ina yi ina mayar da ajiyar zuciya….

Shikkenan na san na rabu da Ustaz idan ba’a yi wasa ba rabuwa ta har abada!

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢.

Kin fara karanta k’arfe a wuta kuwa? Kin ji da’din labarin Arfa da Viper? Idan baki fara ba maza ki fara tunda ke kan ki kin san Alk’alamin Aysha cool baya rubuta shirme. Rubutu ne take yi mai inganci wanda take rubuta abubuwan da suke faruwa zahiran da hanyar warwaruwar matsalar. Kada ki manta marubuciyar k’anwar Maza ce gaba da gabanta, cutarwa… maza ki fara ana kan free pages ina tabbatar muku ba zaku yi nadama ba.

K’ARFE A WUTA……..

Don samun page 12 na Naga rayuwa ga wanda ba za su iya jira ba, ku duba arewabooks an saka. Ga link d’in nan.

Nagode
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ

NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎

𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️

Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

Arewabooks @nazeefah

https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ

Wattpad@Nazeefah381

08033748387.

★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 10

‎Da daddare muna zaune a ‘daki ni da Mami. Kalba take min tana sake zuga ni akan kada na yarda na auri Ustaz. Umma ta yi sallama ta tura k’ofar ta shigo. Idanunta zube a kan mu. Mami kuwa tana ganinta ta tsuke fuska. Zama ta yi a gefen gadon Mamin tana furta “Yanzu Fateema abin har ya kai haka? Ni ban ga abin d’aga hankali a wannan maganar ba, har kike neman ki tsiro da wasu halaye na daban da ba masu kyau ba. Wa’dannan abinda kike bakomai ba ne sai raina Abban su, kin koma san sarai makomar macen da ta raina Mijinta. Ni ban ga aibun Abinda Abbansu zai yi ba. Kamar fa gata ya yi muku ke da y’ar taki, auren namiji kamar Ustaz Ai duk uwa ta gari zata so wa d’anta……” Kallon da Mamin ta mata ne yasa ta tsuke bakinta tana kallonta da mamaki a fuskarta… “”Ke ce dai baki ga abin tada jijiyar wuya ba, ni na hango shi, kuma kuka d’auki maganar nan k’arama ni na shirya fito na fito da duk wanda ya ce zai mata aure a wannan y’an shekarun nata, wallahi ko Human right sai na kai mutum, in dai da gaske har zuciyarku kun bar min y’ar, ai sai ku bar ni na yi abinda zan yi da ita, sai dai idan nuna min za ku yi, ban isa da ita ba don ba ni na haifeta ba….” “A’a Fateema, duk maganar bata kai ga haka ba, Allah ya baki hak’uri.” Umma ta fa’da tana mik’ewa ta fice daga d’akin. Wani tsaki da ya tab’an zuciya Mami ta ja tana furta “So kike ta yi zaman aure da gidahumanci kamar yarda ke kike yi…” Sai na ji kalmar ta min girma a kai, na kuma samu raina da b’aci Umman ce gidahuma kenan?

Sallamar Abba muka ji a kan mu bayan kusan mintuna 30 da fitar Umma, har a sannan kuma Mami bata fasa zuga ni ba. Ido ya zuba mana cikin tsukakkiyar fuskarsa da ban tab’a sanin yana da ita ba. “Tashi ki je sitroom kina da bak’o…” Mami ta ja hannuna ta rik’e k’am. Ba zata je ba..” Ta furta idanunta cikin na Abba. Wani kallo ya wurga mata mai cike da nuna zallar b’acin ransa ya furta “Kada mu yi haka da ke Fateema, kada ki kai ni bango, abin ba zai mana da kyau ba. Cika mata hannu…” Hannun ya fincike a nata hannun ya ja hannuna muka fice. Har d’aki ya raka ni. “Ki shirya sosai ki same shi a sitroom, idan kin so ki watsa min k’asa a ido ki zubar da martabar gidan nan…” Jikina kawai rawa yake, na kasa aikata komai sai share hawayen fuskata nake. Ga Abba ya ce yana tsaye a parlorn Mamin yana jira na. After dress kawai na zura akan kayan na fita duk zuciyata a furguce take ba ni da nutsuwa ko ka’dan. Don ban manta kashedin Mami ba na kada na yarda da zuwa wajen Ustaz idan kuwa na amince ta san na nuna mata bata isa da ni ba, kuma ba ita ta haifeni ba. Wannan magana ita take firgitani nake kuma rasa nutsuwa tabbas sun saka ni a tsaka mai wuya. Hannuna Abba ya sake ja, muka sauka ina kallon Mami da take tsaye ta saka hannu ta share hawayenta sai na ji nima nawa hawayen sun zubo. Na d’an tsaya Abba ya juyo yana kallona. “Kina son na b’ata miki rai AYSHA? Kada ki saka na d’aura miki aure da shi yanzun nan…” Da sauri na girgiza kai. Sai da ya ga na shiga sitroom d’in sannan ya juya ya koma cikin gida.
Chapter 14 · 0% Book details