← Book details Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 48

Sashe 9

Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin daren ranan har an fara samun different campaign tweets akan a sake Asiya, Asiya is innocent.
Wasu kuma ba abinda ya ke ransu irin labarin soyayyar Gwamna da Asiya. Video da É—ibbin jama'a suka gani ya zama shaida akan irin soyayyar da Gwamna SSK ke yiwa Asiya.
A ɗaya ɓangaren kuwa wasu gani su ke renin hankali ne duk abinda yake faruwa, tun daga kulle Asiya da aka yi har zuwa yanzu da wannan abu ya faru..

***

Washegari dakatar da Chief wardress na kurkukun mata da aka yi ya sake tabbatar da zancen mutane na cewa Gwamna ya fara dawo da hankalinsa kan lamarin Asiya. Yayinda wasu kuma ke ganin cewa duk shirin Bilkisu Kachallah ne saboda a interview É—inta ta yi maganar za a hukunta waÉ—anda su ke da hannu akan abinda ya faru.

A ɓangaren Asiya kuwa duk abinda yake faruwa ana sanar da ita. Tsakanin abinda bai cika awa ashirin da huɗu ba Asiya ta zamo tamkar sarauniya a cikin kurkukun. Tunda aka kori Chief wardress kowa sai ya shiga taitayinsa. Hatta warden Maida ta rasa nitsuwarta tun jiya har zuwa wayewar gari, idan ta rasa aikinta ba ƙaramin tashin hankali zata shiga ba saboda aikinta yana mugun rufa musu asiri ita da 'ya'yanta.

Asiya da kanta ta zaɓi a maidata ɗakin Madam Chess saboda ta saba da zaman chan, sabon ɗakin da aka bata ya mata faɗi.

Warden Maida da ta gama tufka da warwara akan lamarin da zai fishsheta sai ta shirya sanar da Asiya duk abubuwan da ta sani.

Warden Bisola ta roƙa ta je ta taho da Asiya office ɗin su. Da farko kame-kame ta fara yi, sai daga baya ta faɗi abubuwan da ta sani tunda ita ɗin ta hannun daman Ogan su ne. Asiya ba ta girgiza da jin cewa Bilkisu Kachallah ce ummul aba'isil komai ba. Abu ɗaya kawai ta nema a wajen warden Maida wato Hansa'u.

Ko minti goma bai cika da fitan warden Maida ba ta shigo da Hansa'u.

Hansa'u da Asiya su ka shiga kallon-kallo sai kuma a tare su ka fashe da dariya...

***

Bilkisu Kachallah na shirin shiga mota wayarta ya shiga ringing, bata É—auki kiran ba sai da ta shiga ciki ta zauna da kyau sannan ta amsa.

"Yes ina ji"

Daga ɗaya ɓangaren aka faɗa mata saƙo.

"Ina zuwa office yanzu, ka sameni a office"...

Office of the first lady of Congo State babban ofishine mai zaman kansa wanda yake da full staff da officials. Tunda aka sanar da wanda ya ci zaɓe Bilkisu Kachallah ta sa aka fara gyara mata wajen, tsohon state library ne da aka kashe ta siya ta maida shi ofishin first lady. Ta yi alƙawarin bayan sun yi shekaru takwas akan mulki bazata bari wata shegiya ta gaji wajen ba, zata maida shi main office ɗinta ne, amma for now nan ne ofishin first lady Bilkisu Kachallah.

Tana isa office É—in ta tarar da COS yana jiranta, tun kafin ta zauna a kujera tace " Lamara mi hakan ke nufi?"

"It means akwai yiwuwar fitowar Asiya nan kusa"

"Ban gane ba. An samu ƙwayoyi a cikin kayanta that should count"

Mr Lamara yai dariya yace " kin manta cewa za a fara binciken account É—in Billy Sanny"

"No way. Ba za su iya linking ɗin account ɗin da ni ba. Inada different account names a ciki da wajen ƙasar nan"

"Boss Lady ina zargin akwai international body da su ka saka hannu a wannan bincike, idan ba haka ba taya za a samo bank details É—in nan ba tareda kin sani ba"

Bilkisu Kachallah ta dunƙule hannunta tana cizon leɓe. Ba damuwarta asirinta zai tonu ba, dan ta san babu yadda za ayi hakan ya faru saboda back up da take da shi, amma kuma idan aka fito da Asiya kaman aikinta ya dawo baya ne

"I don't want Asiya out. Inaga kawai a kashe Timothy Igwe"

Bilkisu ta faÉ—a bayan dogon nazari.

Lamara Damana yace "Wrong idea"

"Kaman ya?"

"Idan aka kashe Timothy Igwe zai kawo zargi"

"To ko a kashe Asiyar ne kawai?"

COS ya sheƙe da dariya yace " idan aka kashe Asiya zaki ruguza komai. Ni dai idan zaki karɓi shawarata, inaga ki bari Asiya ta fito, sai mu maida zancen kan 'yan adawa tunda kinga kotu tayi watsi da ƙaran da Umaru Kwom ya shigar na rashin karɓan sakamakon zaɓe..."

"Bana son attention ya koma kanta idan ta fito, she's better off a prison"

"Zaɓi dai ya rage naki"

Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Chief of Staff Lamara Damana, ko da bata yarda da kowa ba za ta iya cewa ta bawa COS yardanta kaso casa'in cikin É—ari. Idan har wani zai cuceta to banda COS saboda manufarsu É—aya ce...

07

A yau Litinin ne aka yi zama na farko a kotun ɗaukaka ƙara. Yadda aka bijiro da wasu sabbin hujjoji ya bawa ɗaukacin magoya bayan Asiya hope na samun nasara a wannan shari'a.

Kotu ta tashi ne da ɗaga ƙara zuwa wata sati inda za a sake gabatar da Timothy Igwe domin ya amsa wasu tambayoyi.

A ɓangaren Asiya kuwa ta duƙufa ne wajen tsara yadda za ta aiwatar da ɗaukan fansa, bisa shawaran Madam Chess ta yi alƙawarin adana hujjojin da Hansa'u ta bayyana mata zuwa lokacin daya dace a bayyana su.

A bisa gigin son ganin ta samu 'yancinta lokacin da Badawiyya (Hansa'u) ta sanar da ita cewa akwai backup copies na hujjojin da ta tara wanda ta saving a cloud yunƙurin kiran CY Asiya ta yi dan ya retrieving information ɗin ya bawa Barr Zaytoonah a gabatar da su a kotu, amma sai Madam Chess ta nuna mata illar yin hakan.

"Ashe ba ki koyi darasi ba zaman ki a wannan gida Asiya, kina ganin idan an gabatar da hujjojin nan za a kama Bilkisu Kachallah ne?"

Asiya ta ajiye littafin da ke hannunta ta tsurawa Madam Chess ido.

"It seems kin manta mi yake faruwa a jahar nan, Bilkisu Kachallah ke juya jahar nan and there's no way zata bari asirinta ya tonu har ma a ma ta hukuncin daya dace"

"Mommy ya zan yi? Ba zan taɓa yafe mata abubuwan da ta yi min ba"

Madam Chess ta ɗan saki ajiyar zuciya sannan tace " ko dai ki zaɓi tunkaranta gaba da gaba, wanda ina miki albishir da ɗayan biyu. Imma dai a dawo da ke gidan nan ki cigaba da zama ba tareda laifi ba. Ko kuma ki rasa rayuwarki gaba ɗaya. Ko kuma ki zaɓi yafiya, ki haƙura da duk abinda ta miki sannan kina fita daga gidan nan ki nemi Gwamna ya sake ki, idan kika rabu da mijinta za ta bar ki kiyi rayuwarki ba tareda ta takuraki ba"

Dukkan zaɓin da Madam Chess ta kawo babu na ɗauka a ciki, dan kuwa bata ji a ranta koda a mafarki ne zata iya yafewa Bilkisu Kachallah ba.

"to mi zan yi Mommy? Help me please"

Madam Chess ta yi murmushi irin na manya sannan ta ce " wait"

Cikin rashin fahimta Asiya ta ce " wait kuma?"

"Ki jira lokacin ki Asiya, ki jira lokacin da zaki samu abinda ta ke da shi, ki jira zuwa lokacin da sunan ki kaÉ—ai idan ta ji sai hanjinta sun kaÉ—a saboda tsoro"

"Kada ki taɓa nunawa Bilkisu Kachallah manufarki a kanta. Infact ki nuna mata kinada rauni kuma kina buƙatar tallafi. Idan kika bari ta san fiskarki za ta yaƙe ki duk inda za ki shiga, amma idan kika ɓoye mata fiskarki zata nemeki a ko'ina amma ba za ta same ki ba. For the mean time you have to become blind, deaf and dumb to everything"
Asiya ta sunkuyar da kai tana nazari.
Madam Chess ta ƙara da cewa "If you want to be invincible Asiya, you have to wait for your moment"

Chan Asiya ta nisa ta tambayi Madam Chess akan mi Bilkisu Kachallah ke da shi. Kalma É—aya tak ta furta mata, wato "mutane"

Ta ina za ta samu mutane ita ba 'yar kowa ba? Tukunna ma wasu irin mutane Madam Chess ke nufi? Tambayoyin da ya zamowa Asiya assignment kenan saboda Madam Chess ta ƙi yi mata ƙarin bayani akan kalmar data faɗa.

***

A ranan uku ga watan Satumba da misalin ƙarfe shaɗaya da rabi na safe kotu ta wanke sunan Asiya Shahida Faruƙ Baba bisa dukkan wani laifi da aka tuhumeta da shi a baya. Yayinda aka yankewa Timothy Igwe hukuncin zama a gidan kaso na shekaru ishirin. Ita kuwa Uwani Maikifi wacce ta amsa laifinta bisa saka ƙwayoyi cikin akwatin kayan Asiya, kotu ta yanke mata hukuncin shekaru uku a kurkuku.

Duk da yanayi na matsi da ake ciki, duk da mutane dayawa na sukar Gwamnatin Saifuddeen Kachallah saboda rashin biyan albashi da kuma tauye hakkin talakawa da ya ke yi hakan bai hana mutane fitowa domin taya Asiya murna ba. ÆŠaukacin mutanen da su ka yi cincirindo a bakin kotu suna jiran fitowar Asiya kuwa, kace taron kamfen ne da ake raba buhuhhunan shinkafa.

Tun lokacin da aka watsa videon Asiya ana shafa mata kwata tauraronta ya ƙara haskaka a idon mutane, musamman saboda yadda Bilkisu Kachallah ta-kasa-ta-tsare, ta yi kane-kane a kan mulkin jihar.

Fosta fosta na hotunan Asiya sun zagaye lungu da saƙo na cikin jahar, ko ina ka ga hoton Asiya sai dai kaga ana yabonta.

Ga wanda su ke da burbuÉ—in jahilci a tunaninsu kuwa ganin Asiya su ke a matsayin wata waliyyiyar Allah ko kuma Shahidiya. Suna kambamata fiye da kima, har abun ya wuce gona-da-iri.

Barrister Zaytoonah ta fito daga cikin kotu da tsohon cikinta da ke nuni da haihuwa ko yau ko gobe, biye da ita kuma Asiya ce wacce watanni uku da sati biyu na zaman gidan kurkuku ya koɗar da farar fatarta, ga wasu ƙananun ƙuraje da suka ɓata mata fiska.
Chapter 9 · 0% Book details