Sashe 12
Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Matar ƙoƙarin ƙarisa haɗa lecture note ɗinta take, daga gefe tana sauraron recording da ta yi na amsoshin tambayoyi da guest lecturer ɗin yai ɗazu a aji. Ba ta da komai yanzu sai ƙarfe biyar na yamma inda su ke da zama a study group na su. Ba sallah ta ke ba shiyasa ba ta damu da tashi daga ɗakin taron ba duk da kuwa ɗazu da ta duba agogon da ke manne a ɗakin taron ya nuna mata ƙarfe biyu ne da minti goma na rana.
"Asiya Kachallah" Asiya ta yi firgigit dan ba ta tsammanci akwai mutum a É—akin taron ba, a zaton ta kowa ya tafi.
Ta É—an juyo a hankali ta kalleshi sai kuma ta haÉ—a rai. Tunda ta fara karatu a wannan waje Colonel Modi ke takura mata, ba shi kaÉ—ai ba ne amma na shi yayi yawa. Wani lokaci ta kan yi tunanin ko dai ta manna tag a goshinta cewa ita matar aure ce ko hakan zai sa su dena yi mata maganar banza. To amma dukkansu ba yara bane sun san mi su ke sun san tanada aure sun kuma san wa ta ke aure.
"Tambayar da kika yi É—azu was brilliant" Colonel Modi yai maganar yana zama gefenta.
Asiya ta duƙar da kai ta cigaba da rubutu ba tareda ta ce wani abu ba.
" ba za ki haƙura da rubutun nan ki zo mu je ki ci abinci ba?"
Asiya ta É—ago idanunta ta kalli Colonel Modi tace "babu ruwanka da ni Colonel, ka yi harkanka na yi nawa please"
" Asiya kenan. Ki dena ɓatawa kan ki lokaci da auren mutumin da baya ra'ayinki. Ki yarda da ni na nuna miki kulawar da kika dace da shi"
Asiya ta buga littafinta da ƙarfi akan desk ta ce "Colonel wannan ya zamo na ƙarshe da za ka min magana makamancin wannan, idan ba haka ba zan ɗau mataki akan ka"
Bata jira amsar da zai bayar ba ta tattara sauran littattafanta da jaka ta fice daga É—akin taron...
Yau ta kama monday, kuma rana ce da suka kwana da sanin cewa guest lecturer na su na wannan mako ba kowa bane face matar Shugaban ƙasa, itama Alumna ce ta institute ɗin hakan yasa za su samu insight sosai akan karatun da su ke.
Kamar kullum a gaba-gaba Asiya ta zauna, duk da kuwa idan ka duba kaf ajin ita ce ƙarama a ciki. Ba ƙaramin sa'a ta taka ba wajen samun damar shiga wannan makaranta duk da kuwa bata cika requirements da ake buƙata ba. Babu abinda za ta ce da CY sai dai tace Allah ya datar da shi da gaskiya. Ba ta san ya aka yi ya iya boycotting protocol ba, amma koma ya aka yi ta tsinci kanta a nan, tana alfahari da wannan dama da ta samu.
Minti goma da zamansu matar Shugaban ƙasa ta iso ajin inda ta gabatar da lecture na minti arba'in sannan aka bada damar tambayoyi da kuma ƙarin gudummawa daga participant.
Sau uku Asiya na yiwa matar shugaban ƙasa tambaya wannan ya ja hankalin first lady zuwa kanta. Bayan an gama class ɗin first lady ta buƙaci ganawa da Asiya. Minti ishirin su ka ɗauka suna tattaunawa mai mahimmanci kuma Asiya zata iya cewa bayan Madam Chess hiranta da first lady na ɗaya daga cikin hirarrakin da suka zamo silar gyara mata alƙiblar data dosa na cimma burikanta.
***
Su shida ne zaune a round table suna tattauna wasu batutuwa. Kasancewar su manyan mutane shiyasa Asiya ta ke ba su girma wajen kasancewa ta ƙarshe a wajen magana. Ita kaɗai ce mace a group ɗin kuma ita ɗin ce dai ƙaramar cikinsu. Idan ka cire Colonel Modi dukkansu sun haifeta, kai Alhaji wakili kam yayi jika da ita.
Da gangan Colonel Modi ya kawo case study na Jahar Congo cikin tattaunawar da su ke ya tura tambayarsa ga Asiya bayan ya gama kawo ƙorafin matsalolin da jahar ke ciki na rashin tsaro da kuma faɗuwar tattalin arziƙi.
"Kina ga akwai yadda za ayi a farfaɗo da tattalin arziƙin jahar Congo musamman ƙarƙashin jagorancin Gwamna Saifuddeen Kachallah?"
Asiya ta ɗaura hannunta ɗaya akan table ta ce " Tabbas za a iya farfaɗo da tattalin arziƙin jahar idan aka maida hankali kan harkan noma. A baya Jahar Congo ta kasance ɗaya daga cikin jihohin da ake alfahari da su wajen noman shinkafa, shinkafa kaɗai ya bunƙasa arziƙin jahar har..."
"Hajiya Asiya Kachallah kina maganan kusan shekaru goma baya ne, muna magana ne akan gwamnatin Saifuddeen Kachallah wacce ta gaza biyan albashin wata huÉ—u na ma'aikatanta. Kina maganar noman shinkafa, nan nan taki na zamani Gwamnati ta gaza sakewa manoma ya kike ga za ayi nomar?"
Asiya ta yi shiru tana nazari.
"Kin yadda kenan shekaru uku da Saifuddeen zai yi gaba za a samu rugujewar tattalin arziƙi a jihar ku fiye da tunani"
"Ko kaÉ—an Colonel Modi" Asiya ta faÉ—a da confidence.
"Infact, shekaru uku ma su zuwa zasu zamo abin kwatance a duk faɗin ƙasar nan"
Colonel ya jingina bayansa da kujera ya ce " ba cika baki ba, we need plans"
"Project tomatonion" Asiya ta faÉ—a tana kallon 'yan group É—in É—aya bayan É—aya.
Kafin ta cigaba. " kafin na zo nan, na jima ina dogon bincike akan tarihin jahar Congo musamman gameda harkan noma. Na san mi ake nomawa shekaru ɗari baya. Na san yanayin ƙasa da yanayin ruwan sama da ake samu a yankunan jihar, na san minene arziƙin kowacce ƙaramar hukuma a cikin ƙananan hukumomi goma shatara da ake da su a jihar. Wannan ya bani damar ƙirƙiro project Tomatonion domin dawo da tattalin jihar nan ba da daɗewa ba Insha Allah"
Dukkansu su ka zuba ido suna kallonta.
"Anyi zamanin da jihar Congo tana fita da Albasa jihohin kudu, dama ƙasashen da ke kusa da mu irinsu Niger, Cameroon da Chad. Har a zamanin mulkin turawa, farar Albasa a jahar Congo daban ta ke da ta ko'ina. Zan farfaɗo da noman tumatir da albasa fiye da shekarun baya"
Asiya ta kalli Colonel Modi ta ce "ina fata ka gane cewa ba noman shinkafa kaɗai ne arziƙin Congo ba"
Alhaji ÆŠanfisa da Alhaji Wakili su ka shiga tafa wa Asiya cikin nuna jinjina gareta. Colonel kam bakinsa ne ya kafe ya rasa abin faÉ—a dan dama so yake ya kushe Gwamna Saifuddeen, ya aibanta shi, sai kuma aka samu akasin haka...
10
"Azzalumi, Macuci, Allah ya tsine maka, Azzalumi, Azzalumi..."
Gwamna Saifuddeen Kachallah ya farka a firgice ya danne kunnensa da ƙarfi yana faɗin "No, No, No i'm not"
Kusan minti biyu ya ɗauka tsaye yana maimaita abu ɗaya, yana cire hannayensa daga kunne yai saurin maida su saboda irin ihun da ake masa a cikin mafarki ya ke ji. Ya dena kwana cikin duhu dan haka ɗakin tar yake da haske, Da gudu ya ƙarisa wajen table ya ɗauki wata ƙaramar roba ya buɗe ya zaro ƙwayoyi huɗu ya jefa a baki ya haɗiye. Tsayawa yai a wajen yana maida numfashi. Cikin 'yan kwanakin nan baya iya bacci, sleeping pills da ya ke sha ya riga ya zama addicted da shi har ta kai baya iya ma baccin ko da ya sha, idan kuwa ya samu yai bacci to ire-iren mugayen mafarki da ya ke yi shi ke hana barcinsa tsawo.
Saifuddeen ya tsaya a tsakiyar É—akin yana kallon makeken gadon da ke shimfiÉ—e da duvet na alfarma amma bacci ya gagara a kai. Ina ma zai iya zama kamar Malam Habu mai share masa office, ya sani ba shi da gado kamar wannan amma a duk inda ya ke ya sani yana nan yana bacci hankali kwance.
"Excellency 'yata dana aurar kwanaki Allah ya azurtata da haihuwar É—a namiji"
"Masha Allah. Ya sunan yaro?"
"Ranka shi daɗe mai sunan ka ne. Saifuddeen amma Ameer ne laƙabinsa" Malam Habu ya faɗa fiskarsa ɗauke da murmushi.
Watanni goma da suka wuce kenan.
"SAIFUDDEEN, SAIFUDDEEN, SAIFUDDEEEEEN" Gwamna ya kira da ƙarfi kamar wani zautacce.
Gaskiya ya kamata a chanjawa jikan Malam Habu suna, kada shima ya zama Azzalumi kamar mai sunansa abinda ƙwaƙwalwarsa ke gaya masa kenan. A take kuma sai ya je ya ɗau wayarsa ya shiga lalubo lambar Malam Habu sai dai kuma idanunsa dishi-dishi ya ke gani dan haka har ya wuce Mal Habu cleaner kamar yadda ya saving numbar bai gane ba. Ya shafe kusan minti goma yana surfing contacts ɗinsa amma bai gani ba. Chan wata zuciyar ta ce masa ya ajiye wayar gobe idan ya je office sai ya masa maganar.
Kamar wani ƙaramin yaro Gwamna SSK ya takure jikinsa a gefen gado yana rawan sanyi. Ya kasa tashi ya kashe AC da ke ɗakin ya ma kasa komawa tsakiyar gado balle ya rufe jikinsa da bargo ko zai ji ɗumi.
A wannan yanayi daya kamata a ce ya kokawa Allah lamarinsa, ya nemi taimakon Ubangiji akan mulkinsa. Gaba ɗaya basirarsa ta tsaya ne a shan anti- depressant saboda ya samu sauƙin damuwarsa.
Bai samu bacci ba sai kusan Asuba. Hakan yasa shi makara sallar Asuba. Infact sai da Bilkisu ta zo ta tashe shi ƙarfe takwas na safe saboda akwai wani taro da za su je tare yau da ƙarfe tara.
A gurguje yai sallah yai wanka ya shirya ya fito yana murmushin da bata wuce fatar baki ba. Babu wanda ya san abunda ya same shi jiya da dare, babu wanda ya san kullum kukan talakawa ke hana shi bacci. Ita matarsa da ya kamata ace ta kwana tare da shi har ma ta lura da damuwarsa ta riga ta saka katanga tsakaninsu. Rayuwar da su ke ta Gwamna ne da Matar Gwamna ba wai mata da miji ko kuma 'yan uwa ba...
***
"Bikin cikar shekara É—aya da ake son yi, ni ina ga ya kamata a ajiye shi gefe Ranki shi daÉ—e"
Bilkisu Kachallah ta kalli
M Sani irin kallon kana da hankali kuwa?.