Sashe 41
Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mommy Dan Allah ki dena ɗagawa kan ki hankali. Rayuwar nan fa tanada ƙaranci. Ki yi haƙuri ki rungumi duk wata ƙaddarar da ta zo miki. Na sani kina son zama fitacciyar mace a rayuwarki but then not at the expense of your family da kuma imaninki"
Da farko kalamanta sun fara tasiri a ranta amma da ta zo wannan gaba sai muryar 'yarta ya rikiÉ—a ya koma mata na Asiya.
Tura Nana tayi da ƙarfi tana faɗin "abinda ta kitsa miki kenan a kwana biyun da kika yi da ita. To ahir ɗinki da yi mini irin wannan magana"
"Mommy Dan Allah ki fahimceni. I miss you, I miss us. Ya kamata ki dawo mana da farinciki gidanmu kamar yadda muke da"
"Ikon Allah. Yanzu kuma nice sheÉ—aniyar da na tarwatsa familyn mu. Dole ki faÉ—i haka tunda ke jinin Saifuddeen ce"
Ta miƙe tsaye tana huci.
"Idan kina so ki ga farin ciki a gidan nan to tabbas Saifuddeen ne ya bani kujerar sa"
Ta bankaÉ—e Nana dake tsugunne ta wuce É—akinta bayan ta ja doguwar tsaki.
Nana ta bi mahaifiyarta da kallo.
Gaskiya ba zata zauna a gidan nan ba idan tana jin irin waÉ—annan maganganu za ta iya komawa ruwa.
***
Ɗakin taron ya cika maƙil da manyan mutane. Ilahirin jama'ar wajen mata ne dan su suka ɗau kaso tamanin cikin ɗari.
A nan tsakiyar É—akin taro table É—in da Asiya ke zaune yake. Tana nan zaune da Badawiyya gefensu kuma matar tsohon Gwamnan Congo ne mai rasuwa wato Hajiya Sha'awanatu Bacchi, sai kuma wata tsohuwar minister wacce itama 'yar asalin jihar su ce.
Duk da Asiya bata bawa award É—in mahimmanci ba amma tabbas lokacin da suka shigo hall É—in da ake gudanar da taron wani fargaba ne ya shigeta.
Cikin matayen Gwamnoni da ake da shi a ƙasar aka zaƙulo guda biyar wanda sunanta ya faɗa ciki, wannan ma abin godiya ne koda bata ci kyautar ba.
Bayan an buɗe taro da addu'a tareda kaɗe-kaɗe da raye-raye da ake yi a lokutan taro, sai aka shiga gabatar da jadawalin shirin. Wata minister ta fito ta bada taƙaitaccen tarihin kowacce cikin mata biyar da aka zaɓo. Dukka huɗun sun yiwa Asiya fintinkau wajen shekaru da gwagwgwarmaya na rayuwa amma duk da haka itama ba baya ba wajen jajircewa a lamurran jiharta.
Duk da kwaɗayin award ɗin da ta ji a ranta Asiya ta sawa ranta salama da cewa cikin matar Gwamnar Lagos da na Maiduguri ɗayarsu ce za ta lashe kyautar. Sai dai kuma Alƙalami ya bushe dan kuwa tana tsaka da tafawa First lady matar Shugaban ƙasa da ta gama jawabi ta ji ana shirin kiran wadda ta lashe award ɗin.
"And the award goes to.....The youngest wife, the journalist, entrepreneur, beautiful Hajiya Asiya FaruÆ™ Kachallah. Wife to the governor of Congo state"
Asiya tasa hannu biyu ta rufe fiskarta. Badawiyya dake gefe ta miƙe tsaye tana ihu tana tafi.
"Asiya ki tashi"
Tafin da ake ya ƙaru yayinda idanuwan mutane suka zame mata torchlight har ta kai stage inda First lady ke tsaye. Suka yi musabaha da ita sannan ta damƙa mata award ɗin.
Asiya ta É—aga award É—in sama tana murmushi. Masu Camera suka shiga É—aukan hotuna...
30
Saifuddeen ya ɗauko remote ya kashe TVn da ke office ɗinsa. Wani shauƙi da kuma kunya ya shige shi. Adadin mutanen da Project Tomatonion ya amfanar ba za su irgu ba. Rector na Kwalejin Agric takanas ya zo ofishinsa yana yi mishi godiya. Ashe suna zaune ne akan dukiya basu sani ba. Ada sun bar gonakin makarantar da kayan aiki sun lalace ba tareda ana amfani da su wajen samun kuɗin shiga ba amma just tunatarwa da kuma tallafi da Asiya ta basu ya basu damar yin amfani da makarantar wajen samun kuɗin shiga. Duk wani ɗalibi yana ɗaukan karatun theory na awa huɗu ne a rana yayinda sauran lokacin yake ƙaresu tsakanin gonan makaranta ko Lab. Su kansu ɗaliban daga baya shiga gona su yi aiki ya fi musu zaman aji ɗaukan darasi.
Shi baima san Asiya ta commissioning Congo Yogho ba sai da Director na gidan gonar jihar ya kira shi yana sanya masa albarka. Har ofishinsa aka kawo masa samfurin yoghurt da ma'aikatar gidan gona ta fitar a ƙarƙashin ƙaramin kamfani da ta buɗe na Congo Yogho.
Ya sake Hamdala a ransa da Asiya bata dakatar da project ɗin gaba ɗaya saboda shi ba. Dalilin project ɗinta hanyoyin samun kuɗin shiga a jihar sun ƙaru, yanayin kasuwanci ya sake bunƙasa. Jiya kafin ta tafi Abuja take masa maganar ƙaddamar da gonan zuma da take so a fara a jihar. Dan ta haɗa hannu da ƙwararru da zasu koyawa matasa yadda ake kiwon zuma a kuma sarrafa shi cikin sauƙi.
Yai wani murmushin shauƙi yana fatan Allah ya dawo masa da ita lafiya...
*
"A shirye nake na ɓata komai idan har ba zan samu abinda nake so ba. Sai muga ya za ta yi da ɓangaren tsaro kuma, tunda ance ta kawo abinci jihar Congo, bari muga ko zata iya kawo zaman lafiya"
Kalaman Bilkisu kenan bayan ta gama kallon award É—in da aka bawa Asiya.
Ta jawo waya ta kira numbar mutumim da ya ƙwaƙule mata idon mahaifin Asiya...
***
Kwanaki biyar suka ƙara a kan yadda suka shirya dawowa jihar su sai dai dole ce ta sa suka ƙara kwanakin dan hanyoyin shiga jihar Congo babu kwanciyar hankali. Fashi da makami da kuma kidnapping sun dawo tamkar sabon yayi a wajen.
Batun murnan samun award na Asiya ya juye ya koma kuka da baƙin cikin kashe-kashe da ake yi babu gaira babu dalili.
Hakanan kawai Tanko Janwuya ya samu sabon ƙarfi da ƙarin makamai. A ɓangare ɗaya Bilkisu Kachallah na bashi tallafi, a ɗaya ɓangaren Alhaji Umaru Kwom yana bada na shi.
Ranan da Asiya za ta dawo dole sai jirgin sama ta hawo dan babu halin ta biyo mota hanyoyin duka babu kyau infact curfew aka saka a jihar na 6am to 6pm.
Ko hutawa ba ta yi ba Asiya ta fara aiwatar da abinda ta shirya. Wannan ya ƙara rura wutan fitinan da ake ciki.
Duk inda ka leƙa sai dai kaga ana tattaunawa kan batun sunayen manyan mutane da aka fitar wanda keda hannu wajen cin hanci da rashawa sannan kuma wasunsu suke da hulɗa da safarar muggan makamai.
Ba ta ga ta zama ba dan tun da aka saki takardun take samun kiraye-kirayen waya.
Dai-dai zata fita daga gidan motar Mr Lamara Damana ta shigo.
"Miyasa kika fidda takardun nan, you are destroying this state. Idan ta wannan ɓangaren kika fito kusan sai an kama kowanni ɗan siyasa a jihar nan. Dukkanmu muna cikin harkan nan"
"You left me no choice. Mutane nawa aka kashe cikin kwana biyar? Ka san adadin mutanen da aka kidnapping?"
" ba ni da hannu a wannan, wannan aikin Bilkisu ne and you know it"
"Idan baka so ka faɗi kai kaɗai, kana da damar jan ƙafarta ku faɗo tare"
"Zan yi biyayya. Zan taimakawa Saifuddeen ya sake zama Gwamna. Zamu miƙa kaso sittin na kuɗaɗen jiha da muka sace"
"Mr Lamara Damana, ka gayawa Alƙali wannan ba ni ba"
Ja baya yayi taga-taga kamar zai faɗi. Yana iya yin komai dan ya samu duniya shiyasa ya zo neman mafaka a wajen Asiya. Duk da yana ƙoƙarin cin nasara a shari'ar da ake da shi da matar tsohon Gwamna amma wannan shari'a idan aka farata baya tunanin zai samu nasara.
"Ka ga yarinyar nan da kake gani, tafi Bilkisu hatsari, be careful with her"
Ya tuno gargaɗin Yallaɓai akan Asiya.
Idan komai ya lafa zai ɗau mataki akan Asiya, zai walaƙantata, zai kowa mata darasin da har ta mutu ba zata manta da shi ba. Saifuddeen shine tinƙahonta, zai kassara Saifuddeen fiye da tunaninta. Amma yanzu...amma yanzu.
Gwiwowi biyu ya zube ƙasa, Asiya ta ɗan ja baya da sauri dan kamar ma shirin riƙe mata ƙafa yake.
"Ki taimakeni" ya faɗa da muryar ƙasƙanci
Asiya ta rintse ido tareda sauke ajiyar zuciya...
***
"Hukumar EFCC dai ta kama tsohon Chief of staff na Gwamna wato Mr Lamara Damana ne a yayin da yake son fecewa daga jihar bayan wata majiya ta bankaÉ—o manya-manyan laifukansa. Ko tsohon chief of staff É—in zai amince da kashe tsohon Gwamna marigayi Alhaji Saminu Bacchi?"
Da ita da Gwamna babu wanda ya motsa daga inda suke zaune suna ganin labarun da ake gabatarwa.
Asiya ce ta katse shirun da cewa " Idan aka fara shari'ar nan sunan Bilkisu zai fito"
Ta jima tana kallonsa kafin ta É—auke kai ganin ba shi da alamar cewa komai, kamar ma maganarta bai masa tasiri ba.
Miƙewa ta yi za ta tashi ta ɗauke kofin shayi da ta gama sha ya dakatar da ita da cewa "Har yanzu babu abinda ya tsaya na abinda Tanko Janwuya yake yi. People are dying"
"Idan na ce maka Bilkisu nada hannu akan abinda Tanko janwuya yake zaka yarda?"
Zaro ido yai waje yana kallonta cikin rashin gaskatawa.
"Idan kana so ka kashe matsalar Tanko Janwuya ka fara kama Bilkisu"
Ta yi ƙwafa ta ɗau kofi ta bar masa falon.
Ta tsani halin ko in kula da yake idan aka zo maganar Bilkisu. Kamar shi fa bai yadda Bilkisu za ta yi abubuwan da take yi ba...
Maganar rashin tsaro ya É—agawa mutane hankali sama da bankaÉ—e-bankaÉ—e da aka yi na manyan mutane da suka saci kuÉ—in jiha.
Kasuwanci da dama sun tsaya chak saboda matsalar tsaro. Wannan karan yafi kowanni lokaci muni.
Ita kanta Asiya ta É—auka kama ire-irensu Mr Lamara da Mr Paul zai tsayar da komai amma gaskiyar Mr Lamara da yace mata Bilkisu Kachallah ce matsalar tsaron jihar. Duk wani tunani tayi na yadda za ta kawo maslaha a matsalar amma ta kasa.
Wata Safiya bayan ta idar da sallar walaha ta ɗan kwanta tayi wani mafarki akan Alhaji Sani Kachallah. Mutuwarsa a cikin mafarkin ya firgitata matuƙa wannan ne ma yasa ta shirya tafiya zuwa gidan kurkuku.
Yadda babu tsaro a jihar ƙarfi da yaji ta koma tafiya da masu tsaronta, Gwamna yace bai yadda ta fita ita ɗaya kamar yadda take a da ba.