← Book details Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 48

Sashe 27

Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asiya da Badawiyya na tsaka da magana suka jiyo ƙaran siren daya karaɗe gidan.

Wannan yasa Asiya ta bircike ta rasa ma mi zata yi. Wanka zata yi a'a a haka zata fita ta tari Gwamna ko kuma dai ta chanja kaya kawai tunda tayi wanka da safe.

"To ni dai barin tafi dan na san tunda His Excellency ya dawo na tashi a aiki"

ba ta jira amsar da Asiya zata bayar ba ta miƙe ta bar ɗakin.

Jin tsayuwar motoci yasa Asiya ta yi haramar shiga banÉ—aki kawai tayi wanka kar ya shigo ya sameta a haka.

Ba ƙaramin kewarsa tayi ba shiyasa ta masa tanadi na musamman...

Tun da su Jummai suka jiyo jiniya suka fito harabar gidan da gudu. Dukkansu sun jima basu ga Gwamna ba.
Ita Sumayya a hostel take kwana sai dai ba a sati biyu bata leƙo gidan yayarta ba, ita kuma Jummai boarding school na Federal Government Girls College Congo aka sakata, tana JSS two dan kafin a kaitan sai da Asiya ta sa aka mata lesson na kusan wata huɗu.

Wannan karan dukkansu biyun suna hutu shiyasa suka zo yiwa Asiya hutun sati biyu kafin su wuce ƙauye.

Tun kafin Gwamna ya fito daga mota Jummai ke ta waƙar gaisuwar da zata masa a ranta.
Tunda Gwamna ya fito yake ta sake murmushi har ya iso inda suke tsaye.

Sumayya ta risina tace " Uncle Barka da dawowa"

"Good afternoon Eselensy Gomna Sir, how yuwa joney"

Sumayya ta tintsire da dariya.
Ba Sumayya kaÉ—ai ba su kansu escort É—in Gwamna sai da suka É—an dara.

Gwamna yai murmushi tareda shafa kanta yace "kin yi ƙoƙari Nana, ki cigaba da ƙoƙari kin ji"

" Insha Allah Uncle Gomna" Jummai tayi maganar tana hararan Sumayya

Chan ƙasan ransa wani kewa da shauƙin 'ya'yansa ya kama shi. Yaso ace yaje ya duba Mahirah da Nana tun waccan watan amma bai samu dama ba.
In dai har gyaran da yai alƙawarin yiwa jiharsa yake son yi to tabbas dole ne ya rage tafiye-tafiye. To amma kuma 'ya'yansa ma suna da hakki akan sa.
Dole ya ware sati guda ya je ya duba Mahirah a Sudan sannan yaje ya duba Nana a US.
Da wannan tunanin Gwamna Saifuddeen ya shiga gida.

Ɗakinsa ya fara shiga wanda ƙanshin da yai arba dashi a falo ya tabbatar masa ba ƙaramin tanadi aka masa ba.
Ganin bata É—akinsa ya sa shi cire babban rigar sa ya ajiye akan gado, ya cire takalminsa ya saka room slippers ya fito daga É—akin ya nufi É—akin Asiya.

Ƙoƙarin fitowa daga banɗaki Asiya take taji ƙaran buɗe ƙofan ɗakinta.
Shikenan har ya iso bata shirya ba, ta furzar da iska ta baki sannan ta buɗe ƙofar banɗakin.

Kallon-kallon suka tsaya yiwa junan su kowa da abinda ke ransa, amma abu É—aya suka haÉ—u akai wato kewa.

Gwamna ya sake mata wani murmushi wanda ya fidda fararen haƙoransa.
Yadda yai murmushin ya ƙara bayyana tsananin gajiyar dake tattare da shi.

Ware mata hannayensa yayi yana cigaba da yi mata murmushi.

Itama murmushin ta sake masa sannan ta ƙarisa ta shige jikinsa ta ƙanƙame ƙugunsa da kyau.

"I miss you" ya faɗa yana kissing wuyanta, kafin ta bashi amsa ya lalumo bakinta ya haɗe da nasa. Kaman jira take yi ta ƙara shiga jikinsa sosai tareda tallafo kansa tana kissing ɗinsa sosai...

Rabon da su kasance da juna wane sati uku. Wannan ya haifar da wani kewa da shauƙi na musamman a tarayyarsu ta yau. Tanadin da ta masa yayi aiki domin in between kisses yake ta maimaita kalmar 'I Love You Asya'

Tare suka yi wanka amma shi ya rigata fitowa saboda wankan tsarki da tayi yasa take ta busar da gashin kanta da blow dryer.

Towel ne kawai a ƙugunsa lokacin daya zauna bakin gado yana ƙara goge kansa da ƙaramin towel. Idonsa ne ya faɗa kan wani ƙaton brown envelope dake kan side drawer, bai san ya aka yi zuciyarsa ta ingiza shi da buɗe envelop ɗin ba, dan a tunaninsa a ciki ne surprise ɗin da ta ce zata bashi yake. Idan kuwa ya kasance ticket ne na jirgi zuwa Sudan zai fi kowa farin ciki da hakan.

Sai dai kuma yana É—aga envelope É—in ya ji ta da nauyi sosai, kamar ba zai buÉ—e ba sai kuma wata zuciyar tace ya buÉ—e.
Takardar farko daya ci karo dashi ya sa shi miƙewa tsaye zumbur. Hannunsa yana rawa ya fara bin takardun da kallo a tsanake.

Jin alamar ana shirin buɗe ƙofa yai saurin maida takardun ya ajiye envelop ɗin.

Yi yai kamar bai ga komai ba ya dai-dai ta fiskarsa.

A haka ya daure har ta gama shafa masa mai ya miƙe yace zai je chan ɗakinsa ya sanya kaya.

Itama É—in kaya kawai ta saka ta É—an gyara fiskarta kaÉ—an tunda abinci zasu ci. Floral Abaya da ta saka kalar ruwan goro ya mata kyau sosai. Ta feshe jikinta da turaruka sannan ta fita.

A falonsa ta same shi yayi tagumi, duk wani walwala data saka shi mintina kaÉ—an da suka wuce babu shi a fiskarsa.

"My love lafiya kayi tagumi" tayi maganar tana cire hannunsa

Maimakon ya bata amsa sai kawai ya miƙe ya wuce ɗan ƙaramin dinning dake haɗe da falon.

Jikinta yai sanyi laƙwas, ɗazu-ɗazun nan yake maƙale da ita kamar zai cinyeta amma yanzu kuma ya sauya.

"Mijina akwai abinda ke damunka ne? Maganar ma'aikata da za a É—auka ne?"

Bai amsa mata ba ya fara ƙoƙarin serving abinci da kansa tayi saurin karɓe serving spoon ɗin ta fara ɗiba masa jikinta a sanyaye.

Sai data gama zuba masa abincin ta tausasa muryarta tace " Dan Allah kayi haƙuri da koma minene ke damunka, idan ma nice na ɓata maka rai ka yafe min. Na sani ba ka ji daɗin yadda na cire ka daga project da nake yi ba, na yi hakan ne domin na san akwai ayyuka a gabanka sannan baka yadda cewa project ɗin zai kawo alkhairi a jihar nan ba. Kuɗin dana samu na endorsing foundation na Reverend Buba kuma Wallahi grant (tallafi) ne na samu daga turai, dama na jima ina nema in case babu kuɗin da za a funding project ɗin sai Allah yasa kuma suka bani a dai-dai lokacin da kace a katse project ɗin gaba ɗaya"

Hawaye suka taru a idonta dan har ga Allah taimako take son yi ba wai bijire masa ba.

Yana sauraron bayanan ta amma abinda yake son ji ɗin bata faɗa ba. Shi maganar project ɗinta bai dame shi ba musamman daya kasance mutane sun rungumi loan daga hannun Reverend tun lokacin da Mai Martaba ya fito yace shima ya karɓi bashin iri da takin zamani daga hannun Reverend.

Abinda ya gani a É—akinta yake so tayi magana a kai, dalilinta na son kashe masa mahaifi yake son ji, dalilinta na son tozarta danginsa yake son ji.

"My love please forgive me" Asiya ta faÉ—a tana É—aura hannunta akan nasa

Ajiye cokalin hannunsa yai ya kalleta da kyau sannan yace " yaushe kike da niyyar faÉ—a min? Ko so kike sai kin kai shi kurkuku zaki fito ki faÉ—a min komai?"

Ta É—an zaro ido waje cikin rashin fahimta.

"Ko kuma dai so kike baƙin ciki ya kashe min shi"

"Your Excellency ban gane maganar ka ba"

"Na ga takardun da ke É—akin ki. Na san abinda kike shiryawa a bayan idona"

"Ya Subhanallah! Ba abinda kake tunani bane"

"Mi nake tunani Asya? Minene dalilin da zai sa ki nemo shaidu akan abubuwan da Baba ya aikata shekaru kusan ishirin da suka wuce. Tell me Asya, mi kike shirin yi?"

Asiya ta haɗiye yawu da ƙyar tana tunanin ta ina zata fara masa bayani. Shaɗaf ta manta bata ɓoye takardun ba lokacin da Badawiyya ta fita

"Ina jin ki" ya katse mata tunani

"Wallahi ba abinda kake tunani bane. Yes na jima ina tara shaidu akan mutanen da suka saci kuÉ—in jiha, ina so ne nayi amfani da shaidar wajen yi musu barazana da hukumar EFCC dan su fito da wasu kuÉ—aÉ—en da suke dannewa sannan su barka ka yiwa jihar nan aiki"

"You are very stupid Asya. Mahaifina kike iƙirarin zaki turawa EFCC, it seems kin manta cewa duk abinda na zama a rayuwa to dalilin Baba ne. How could you"

"Sai me idan mahaifinka ne. Alƙawari ka ɗauka akan zaka yi shugabanci da gaskiya, amanan talakawa ka ɗauka Saifuddeen Sa'ad Kachallah kuma dole ne ka sauke da daɗi ko ba daɗi idan har kana son gamawa da duniya lafiya"

"Ba ni ke Gwamnati ba lokacin da Baba ya aikata laifukan nan, that was in the 90's Asya"

"Alhaji Sani Kachallah ya cinye kuɗin kwangilar da aka bashi na yin tituna a ƙaramar hukumar Gandu da Taƙal da wasu ƙauyukan da ban ma san sunansu ba. And we are talking about millions of nairas your Excellency. Sannan ko shekara biyu ba ayi da bashi wannan kuɗin ba. Gaya min a Gwamnatin ka ne ko ba a Gwamnatin ka bane?"

Tabbas ya bada kwangilar kuma tabbas ba ayi aikin ba, kuma har yau bai bi ta kai ba. Ya bada kwangilar ne lokacin da baya cikin hayyacinsa, ya bada kwangilar ne lokacin da ba zai iya banbance gaskiya da rashin gaskiya ba.

"Why are you doing this Asya, ki bari na gama Gwamnatin nan lafiya. Kin sani dana tona asirin Baba gara na ajiye kujerata"

Hawaye ne suka fara zubo mata dan yau kan ta gama tabbatarwa kanta cewa ita kaɗai ce ke kiɗa da rawanta Gwamna Saifuddeen baya biye da ita a tsarin data shirya na yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma ɗaukaka darajar jahar su.

Abu É—aya ne bata sani ba, shin dama tun asali bashi da niyyar yiwa jihar nan hidima ne ko kuma dai har yanzu influence na Bilkisu ne ke jikinsa?...

22
Chapter 27 · 0% Book details