Sashe 30
Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Sani Kachallah ya kasa zaune ya kasa tsaye tunda ya gama waya da Bilkisu tace masa tana hanya.
Jiya da dare ya wuni ne yana ta saƙa da warwara kan kalaman Bilkisu, a matsayin sa na tsohon ɗan siyasa ya fahimci kalaman Bilkisu sarai, kalaman na nuni ne da shimfiɗar Kamfen, duka kalamanta babu inda tayi izina da sunan Saifuddeen komai ta faɗa tana alaƙantawa ne da kanta. Idan kuwa haka ne tana nufin ita zata fito takara a zaɓe mai zuwa kenan.
Yana tsaye yana kaikawo cikin zuciyarsa aka buɗe ƙofar ɗakinsa. Yabi ƙofar da kallo har Bilkisu ta ƙaraso kusa da shi tana murmushi.
"Baba irin wannan kira da sassafe haka, hope all is well?"
Nuni ya mata da hannu akan ta zauna akan kujera, shima ya zauna suna fuskantar juna. Ita kanta sai da jikinta yai sanyi da irin kallon tuhuma da Baban nata ke binta da shi.
"Bilkisu kin san dai na san wacece ke kuma na san duk abinda zaki iya yi"
Ya ɗan yi shiru dan maganar daya ke son yi tana da matuƙar nauyi a baki
"Kina tunanin kashe Saifuddeen ne ko kuma zaki sa shi yai resigning da kan shi?"
"Baba mi ya kawo wannan maganar kuma?"
"Gaskiya zaki faÉ—a min Bilkisu, gaskiya nake son ji daga bakin ki. I know you, i know you can do anything just to get what you want.
"Kin jima kina sha'awar kujerar Saifuddeen, kin jima kina son yin abinda zaki fi Saifuddeen. Na roƙe ki Bilkisu don't walk this part. Saifu mijin ki ne, ɗanuwanki kuma uban 'ya'yan ki"
"And so what Baba, so fucking what dan na so Saifuddeen a baya har na haifa masa yara uku. Kai da shi duka babu wanda ya damu da abinda ni nake so"
"Baba baka taɓa ganina a macen da take da hazaƙa da basirar da zata shiga siyasa ba. A kullum Saifuddeen shine ɗan gaban goshinka shine zai gaji harkokin ka na siyasa kuma ka sani cewa Saifuddeen is a coward, bai da jarumta ko kaɗan"
"Mi kike shirin yi Bilkisu?"
Alhaji Sani ya tambaya a firgice
"Yanzu lokaci na ne, zan yi amfani da baiwa da hazaƙar da Allah ya bani wajen gina ambition ɗina na zama fitacciyar 'yar siyasa a ƙasar nan. I will be the next governor of this state Baba. Zan yi abinda Saifuddeen ba zai taɓa yi ba har ya ƙare rayuwarsa"
"Bilkisu kin haukace ne. Kashe min Saifu za ki yi?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye
"Kisa? Baba ka kwantar da hankalin ka, Saifuddeen na raye a doron ƙasa za a rantsar dani gwamnan jihar Congo"
"Ba zan yafe miki ba idan wani abu ya samu Saifu, kuma ki sani ba zan taɓa bari ki hau kujerar nan ba"
Bilkisu ta miƙe tsaye ta ɗau jakan ta tace "Baba Allah ya bawa kowa sa'a"
Bayan tafiyar Bilkisu Alhaji Sani ya shiga tashin hankali mai tsanani, ya rasa ma ina zai sa kansa.
*
Asiya tana karyawa ita da ƙannenta wayarta ya fara ƙara. Tana ɗaukar wayar ta ga sunan Alhaji S Kachallah, tun wani lokaci da ta kira shi ta masa ya jiki lokacin daya dawo daga Germany bayan yaje an duba lafiyarsa ta saving numbarsa a wayarta.
Ba ta yi mamakin ganin kiransa ba kasancewar yana da masaniyar tana shirin maka shi kotu.
Bayan sun gaisa ya nemi ganinta a Kachallah house nan da awa É—aya, ta amsa da toh.
Asibiti take son zuwa dan taje ta gaida Rufaidah Kachallah sannan su wuce gidan Halima dan tunda yaran suka yi hutu basu je gidan Yaya Bello ba. Itama Asiyar rabon ta da gidan Haliman ta manta.
Bayan sun gama karyawa tace da su Sumayya Direba zai kaisu gidan Halima ita zata wuce Kachallah house idan ta gama zata same su a chan.
Ta riga su Sumayyan ma fita daga gida dan har lokacin data É—auko key É—in mota ta fito basu gama shiryawa ba.
Har falon Alhaji Sani mai aikin matarsa ta mata jagora sannan ta kawo mata kayan marmari da tarkacen ciye-ciye.
Kusan minti biyar da zuwanta Alhajin ya shigo falon.
Asiya ta yi saurin risinawa tana gaishe shi.
Bayan ya gyara zamansa yace da ita "ya kike jin labarin iyayen ki?"
"Suna lafiya Baba"
"To Allah ya ƙara musu nisan kwana"
Ta amsa da Amin. Shiru ne ya biyo bayan hakan gaba ɗaya Asiya ta ƙagu ta ji dalilin kiranta da yai. Kafin tazo ba abinda bata saƙa a ranta ba, har tunani tayi ko cewa zai yi ya saka Saifuddeen ya rabu da ita.
Gyaran murya yai sannan ya katse shirun da cewa "Miyasa kike son turani kurkuku?"
Asiya ta É—ago ido ta kalleshi da sauri dan tambayar ta mata bazata.
"Ki saki ranki ki faɗa min gaskiya, idan hujjojin ki suna da ƙarfi zan miƙa kaina gaban alƙali ba sai kin sha wahala ba"
Bata gama gane zancen sa ba amma idan gaskiya yake nema zata faÉ—a masa ko da ba zai yiwa kunnuwansa daÉ—i ba
"Baba ka gafarceni idan akwai rashin kunya a maganganun da zan yi"
"Kar ki damu, dama ina neman wanda zai gayamin gaskiya ba tareda ya ji kunyata ba"
Asiya ta É—an gyara zamanta sannan ta fara bayani
"Baba ban fara bincike a kan ka saboda ina so na kawar da kai daga jikin mijina ba sai dan ina so na taimaka masa wajen yin jagoranci na gaskiya. Akwai abubuwa dayawa daya kamata ayi a jihar nan amma budget yana kasawa saboda mutane dake cinye kuɗin tun kafin a gudanar da komai. Kuɗin nan kuɗin talakawan jihar nan ne kuma duk wanda ya cinyesu ya ci haram, na fara da kai ne saboda in har Gwamna zai yi gaskiya to daga jikinsa zai fara yaƙi da masu cin hanci da rashawa. Kaine na farko a list ɗina kuma indai aka yi nasara akan ka to babu wanda ba zai shiga hannu ba.
"Ni ina ganin taimakon ka ma za ayi a yi maka hukunci daga nan duniya a rage maka zunuban mutane da kake ta tarawa kanka sama da shekaru ishirin. A ƙalla Baba zaka kai shekara saba'in da biyar koma fiye a duniya kana tunanin nan gaba zaka ƙara shekaru kamar su ne? Mutuwa rigar kowa ce kuma tabbas zata riske ka ko ba daɗe ko ba jimawa. Akwai kwanciyar ƙabari akwai tsayuwa a gaban Allah, shin kana so ka mutu da hakkin dubban mutanene? Shin Baba kana tunanin duk wannan matsayi da kake da shi a nan gida duniya zai ƙwaceka daga azabar Allah. Ko asirin ka bai tonu anan duniya ba akwai ranan da duk wani sirri zai fito fili."
Hawaye ne suka fara zubowa a idanun Alhaji Sani hakan yasa Asiya ta dakatar da maganganunta.
Kusan minti uku babu wanda yace komai. Chan kuma Asiya ta motsa baki a hankali ta furta " ka ji tsoron Allah ka taimakawa Saifuddeen ya gudanar da mulkinsa bisa adalci"...
***
Bilkisu kam ko kaɗan bata damu da halin da mahaifinta zai shiga ba bayan ta fitar masa da maitanta fili. Abinda ta sa a ranta shine idan komai ya tafi dai-dai har ta hau kujerar Gwamna zata damƙa masa sarautar Congo wannan kuma ta sani zai zamo masa compensation bisa abinda zata yiwa Saifuddeen.
Bayan ta samu zama a office ɗinta ta tambayi Sakatariyarta ko an aiko mata saƙo daga ofishin matar shugaban ƙasa amma tace ba abinda aka turo.
Auren 'yar shugaban ƙasa nan da sati mai zuwa, kuma ta ci burin amfani da wannan dama wajen samun wani kusanci na musamman da matar Shugaban ƙasa. Tana buƙatan support na manyan mutane musamman yanzu da abubuwa ke shirin kwaɓe mata.
Ta É—au waya ta danna numbar first lady É—in dan ta tayata murnan bikin da za ayi amma har ta tsinke ba a É—auka ba. Ta ajiye wayar a ranta tana faÉ—in da zaran anyi kwana biyu maganar M Sani ta lafa zata je har Abujan ta yiwa first lady barka.
*
A ɓangaren Gwamna kuwa ya cigaba da gudanar da harkokinsa cikin ɗarɗar domin bai gama yarda cewa Asiya ta haƙura da case ɗin Baban sa ba. Gani yake ko da wani lokaci zai ga hoton Babansa a talabijin ana saka masa ankwa a hannu.
Da wannan tunanin ya wuce gaisuwa ƙauyukan da aka kai hari kwanan baya.
**
Ita kuwa Asiya jiki a sanyaye ta dawo gida ko gidan Halima bata wuce ba. Maganganun Alhaji Sani sun saka jikinta sanyi.
"Ina so ki ɗauka min alƙawurra guda uku Asiya Shahidah, idan kika yi wannan nayi alƙawari ni da kaina zan kai kaina kotu"
Sosai ta É—auko nitsuwarta ta É—aura akan shi yayinda zuciyarta ke fargaban abinda Alhajin zai faÉ—a
"Na farko ina so ki kare kujerar Saifuddeen, akwai masu harin kujerarsa cikin makusantar sa na jini. Ki taimaka masa ya ƙarisa wa'adinsa bisa adalci.
"Alƙawari na biyu shine ina so ki saka Gwamna ya cire Mr Lamara a matsayin Chief of Staff nasa sannan duk abinda zaki yi ki tabbatar an kama Mr Lamara nan bada jimawa ba domin na tabbata shine ya nemo takardun da kike da shi. Matuƙar Mr Lamara yana nan ba lallai ke ko Saifuddeen ku cimma wani buri naku ba"
"Na uku" ya tsaya da maganan saboda wani abu daya toshe masa maƙoshi. Kusan minti biyu ya ɗauka kafin ya cigaba
"Ina so ki je Gambia ki sada Saifuddeen da 'yanuwan mahaifiyarsa. Na jima ina son yin hakan amma sai wani abu ya zo ya tare, a yanzu babu gatan da zan iya yi masa daya wuce wannan"...
Asiya ta riƙe kai tana furzar da iska saboda ƙirjinta daya cunkushe. Babu ko ɗaya cikin alƙawurran da ta ɗauka daya ke da sauƙi. Haka nan maganganan Alhaji Sani kusan yana mata ishara ne da Bilkisu Kachallah, tabbas hiran da Bilkisu ta yi jiya da 'yan jarida kamfen take a fakaice.
Gaba É—aya ta rasa walwalarta dan har yamma da su Sumayya suka dawo suna mata hiran wai Halima na da ciki bata sake jikin ta ba.
Yamma lis kusan gab Magariba Badawiyya ta iso gidan zuwan Badawiyyan ne ma ya sanyaya mata rai dan ta san ko da shawara É—aya ce zata samu a wajenta.