← Book details Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 48

Sashe 18

Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da Asiya ta zare jikinta ta tashi Gwamna yana kwance yana bacci mai daÉ—i.
Ji take kamar an zuba mata yaji a gaba saboda zafi amma haka ta daure ta ƙarisa cikin banɗaki, sai da ta dafe bango ta ɗan huta kafin ta samu ƙarfin haɗa ruwan zafi ta shiga ciki. Bata kawo wannan abu zai faru da wurwuri haka ba, ta sa a ranta sai ya warke sarai ƙila ma sai sun komai Nigeria. Sai dai Alhamdulillah yanzu kam ta zama cikakkiyar matar aure. Bayan ta yi wanka ta ɗauro alwala ta fito. Tana tunanin za ta iya ko sallah raka'ah biyu ne amma sai ta ji ta kasa saboda zogi da ta ke ji a gabanta duk da yanzu da ɗan sauƙi. Da ƙyar ta iya daddafawa ta kai jakar kayan kwalliyar ta ta ɗauko da robar zuma da ta taho da shi wanda take haɗawa da mayukanta tana shafawa sannan kuma tana sha ita da Gwamna duk safiya.

Ta tsiyayi zumar a hannunta ta shafe gabanta da shi. Bayan ta gama ta rufe goran zumar ko iya maida shi inda ta ɗauko bata yi ba ta koma gado ta kwanta ta ƙudundunu cikin bargo.

Washegari da safe Gwamna ne ya fara tashi sannan ya tasheta. Tana haÉ—a ido da shi ta ji wani kunyarsa ya rufeta ta yi saurin rufe idonta da tafukan hannunta.

"Alhamdulillah! Yanzu kam gangan jikin da ruhin duk mallakin Saifuddeen Sa'ad Kachallah ne ko?"

Asiya ta juyar da kai gefe tana murmushi. Lokacin da ta tashi daga gadon ta ji sauƙin zogin da take ji ba kamar jiya da dare ba. Da ke ta yi wanka jiya alwala kawai ta ɗauro ta fito ta tada sallar Asuba lokacin Gwamna ya idar da tasa sallar.

Kwanakin da suka biyo baya sun kasance ranakun farinciki a tarihin rayuwar Asiya domin kullum cikin samun kulawa da soyayyar Gwamna Saifuddeen ta ke ciki. Abun daya ƙara faranta mata rai shine yadda yanzu Gwamna ya dage da sallar nafila da kuma azkar ba kaman farkon zuwansu garin ba. Ganin ya samu lafiya kawai Gwamna ya sallami Al'amin da Ɗayyibu akan su wuce Nigeria su zasu iso daga baya. Samarin biyu sun gane manufar Gwamna don haka ko da Asiya ta nemi dalilin tafiyar ta su kowa ya kawo dalilinsa na ƙarya. Ranan litinin Gwamna da Asiya suka raka su airport suna dawowa kuwa Gwamna ya buɗe babin honeymoon ɗinsa dan kuwa Asiya ta yi jinyar jikinta na kwana biyu. Sati ɗaya suka yi suna honeymoon Asiya ta tada zancen komawarsu Nigeria, na farko saboda research project ɗinta da take son submitting na biyu kuma saboda bikin Halimah Kachallah da Yaya Bello.
Gwamna bai musa ba amma yace su fara zuwa su gabatar da godiya a É—akin Allah sannan su kai gaisuwa kabarin fiyayyen halitta.

Ranan da suka dira a garin Madina ranan Yallaɓai ya rasu a chan ƙasar Germany inda yake jinya. Dai dai lokacin kuma zoben hannun Bilkisu yai wani haske sai kuma zoben ya ɓace ɓat.
Faɗa ta ke yiwa M Sani akan ya kasa sawa a withdrawing Asiya daga National institute. Masifa take masa amma babu laifinsa aciki saboda duk inda ya je da sunanta ya ke zuwa kuma an ƙi karɓan duk ƙorafin da ta kawo. Infact Asiya na ɗaya daga cikin ɗalibai masu tsananin ƙwazo a gaba ɗaya tarihin kafa makarantar dan haka ba za su koreta tana daf da ƙarɓan certificate ɗinta ba.

Ɓacewar zoben Bilkisu ya sa ta danna wani ƙara. Jikinta ɓari yake lokacin da ta ɗau waya ta fara neman numbar Malaminta.

"Boss lafiya?" M Sani ya tambaya a firgice

"Get out!" Ta daka masa tsawa

"Alkadarin jiki ya karye har sau biyu dan haka mai yiwa zoben hidima ya gudu kar a hallakashi gaba É—aya"

Abinda Shri ya faɗa mata kenan lokacin da ta kawo masa ƙorafinta. Mi zai sa alkadarin ya karye bayan mutum uku da aka haɗa zoben dan su suna raye?

Tana gama waya da Shri Chief of Staff ya kirata ta sanar da ita mutuwar Yallaɓai. Mutuwar zaune ta yi akan kujerarta tana tunanin mafita idan har aikin da aka yiwa Saifuddeen ya warware.

***

A chan Kachallah House kuwa Halimah da mahaifiyarta da kuma Hajiya Ummah sun duƙufa wajen shirye-shiryen biki tunda yanzu sauran kwanaki goma sha uku a ɗaura auren. A da Mommyn su ta ƙi haɗin kasancewa duk 'ya'yanta sun yi aure ne a babban gida ita kuma Halimah wanda za ta aura ba ɗan kowa bane sannan ba abinda yake da shi, abin takaicin ma wai dreban taxi ne kuma tsohon ɗan shaye-shaye. Babu yadda ta iya tunda babu wani da ya zo neman Halimar kuma gashi ta doshi shekaru arba'in.

Tun lokacin da Yaya Bello ya amince zai auri Halimah yai wa kansa karatun ta nitsu ya ce zai fara sana'a tunda Asiya tace zai daina tuƙata dan itama zata koyi tuƙi. Shi ya zaɓi aikin taxi dan ya fi gane harkan mota fiye da kasuwanci.

Allah Sarki Alhaji Sani sai da Baffansa ya sake masa maganar cire hannunsa da yai a hidimar bikin Halimah bai kyauta ba sannan hankalinsa ya karkato kan autar sa. Ya rasa gane dalilin hukuncin da ya zartar, lokacin da matarsa ta faɗa masa shi da kansa ya ce Halimah ta nemi wani waliyyin da zai mata jagora ba shi ba, abin ya girgiza shi matuƙa domin ya sha buri sosai akan bikinta.

A hankali kuma ya fara tuno wasu abubuwan da ya aikata a lokacin daya ke ƙarƙashin ɗaurin 'yarsa Bilkisu.

Bilkisu ta shiga ruɗu sosai har wani rashin lafiya ne ya sameta ta dinga jin jikinta na ɓari tana jin sanyi sosai na shigarta.
Da dare da ta samu nitsuwa ta wuce chan gidansu dan ta tabbatar ko akwai sauran hope ta wajen mahaifinta sai dai kash aikin gama ya gama. Lokacin da ta je ma ƙaramin meeting ake yi kan yadda bikin Halimah zai kasance.
Lokacin da ta shigo falon Babansu duk cikin 'yanuwanta babu wanda ya kulata. Saudah kan ma tsaki ta ja yayinda Rufaidah ta bita da harara.
Wannan chanjin fuska da ta gani kaÉ—ai ya sanyaya mata jiki. Ta dai zauna dan ta saurari abinda ake tattaunawa. Wai abin mamaki har za a haÉ—a meeting a gida bata da labari.

"To yanzu dai Anty Batulah za ta haÉ—a kuÉ—in gudummawa sai kowa ya buÉ—e aljihunsa ayiwa Auta kara"

Saudah ta yi magana tana hararan Bilkisu.

Cikin rashin fahimta Bilkisu tace " Halimah ce za ta yi aure?"

"Eh Allah yayi, Allah gatan bawa"

Saudah ta amsa tana gyatsina fuska.

Bilkisu ta shanye ɓacin ran da ya taso mata tace " wa za ta aura?"

Kaman jira dama Saudah take ta tambaya sai ta amsa da cewa " za ta zama Amaryar Muhammad Bello FaruÆ™ Baba"

Kusan sakan biyar Bilkisu ta ɗauka tana processing sunan kafin ta gano alaƙar sunan da matar da ta fi tsana a duniya.

"Baba kana zaune ana maganar haÉ—a maka zuri'a da useless family"

Alhaji Sani yai murmushi mai ciwo yace

"Kina baƙin ciki da zaɓinta ne?"

Bilkisu ta buÉ—e baki ta rufe ta rasa abun faÉ—a...

*THE RETURN*

15

Murna da farin ciki ne ya shiga zuciyoyin jama'a lokacin da suka ji cewa Gwamna yana tafe ranan jummu'a. Yawanci jama'a sun yi ittifaƙi ne akan cewa jinya ce ta saka Gwamna Saifuddeen ya ke yin halin ko in kula da talakawansa.

Lokacin da Asiya ta sake selfie ɗinta da Gwamna a shafinta na twitter ta kuma yi gajeren rubutu a ƙasan hoton kan kace kwabo hoton ya zaga ko'ina a cikin jahar, kowa na faɗin albarkacin bakinsa kan cewa akwai ƙanshin alkhairi a dawowar Gwamna. Sai dai duk da haka an samu wasu da suke ganin wannnan dawowar ne ma zai zamo mafi muni a tafiyar mulkin Gwamna SSK, sun yi amanna da cewa Gwamna ba jinya ya tafi ba, honeymoon ce irin ta turawa dan gashi yayi ɓulɓul ya ciko kamar ba shi da damuwar talakawa a ransa.

***

Hajiya Bilkisu Kachallah ta cigaba da kai kawo a ƙaton ɗakin cin abinci na manyan baƙi da ke cikin gidan Gwamnati, yadda ta ke tafiyar da komai zaka ce babu wani abu da ke damunta. Liyafa ce ta ke shiryawa saboda zuwan Gwamna, 'yanuwa mafi kusa kaɗai ta gayyata zuwa wannan liyafa.

Tana tsaye jikin kujera tana nunawa wani staff inda zai ajiye wani dessert da ta san Gwamna yana mugun so kunnenta ya jiyo abinda wani reporter ya faɗa. A fusace ta juya ta kalli TVn da ke manne da bango idonta yai tozali da hoton da ɗan jarida yake magana a kai. Hoton selfie ne na Asiya da Gwamna a cikin jirgi, "THE RETURN" Bilkisu ta karanta rubutun da ke ƙasan hoton.

"Excellency Ma, your Excellency Ma"

Bilkisu ta yi firgigit ta juyo ta kalli staff É—in da ke mata magana. Lokaci guda wasu abubuwa suka fara dawo mata ta yi saurin girgiza kai tare da barin dinning hall É—in.

Kafin ƙarfe uku na rana an kammala komai na shirye-shiryen liyafa har wasu ma daga cikin wanda aka gayyata sun fara isowa.
Tun ƙarfe uku saura mutane suka cika bakin airport ɗin riƙe da poster-poster na Gwamna da Amaryarsa Asiya.

Gidajen talabijin da na radio suma sun aiko wakilan su dan live ake so a kawo rahoton wa mutane.

Ƙarfe uku da minti biyar jirginsu Gwamna ya iso.

Gwamna da Asiya suka sauko daga cikin jirgi hannunsu sarƙe cikin na juna sai murmushi suke da ka gansu kasan akwai farinciki da soyayya mai ƙarfi dunƙule a zuciyar su. Haka suka dinga ɗagawa mutane hannu suna murmushi yayinda ake ta watsa musu ruwan hotuna.

A cikin mota Asiya ta lura hannun Gwamna yana ɓari hakan yasa ta ɗaura ɗaya hannunta akan nasa tace "ka kwantar da hankalinka Excellency, talakawa na tare da kai har yanzu, kuma da yardar Allah za ka sauke musu hakkinsu"
Ta ranƙwafo dai dai kumatunsa ta manna masa kiss tace "ina tare da kai Mijina"

Gwamna ya gyaÉ—a mata kai yana murmushi.
Chapter 18 · 0% Book details