← Book details Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 48

Sashe 32

Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asiya tayi dariya tana girgiza kai.

Bayan sun nitsu Asiya ta zayyana mata abinda ke tafe da ita da kuma ƙaryar da ta yiwa Alhaji Sani.

Hajiya Umma ta yi wata 'yar dariya irin tasu ta manya sannan tace "Shahidah kenan, ai sam Alhaji bai yarda da batun ki ba, ya kira ni ya shaida min komai kuma na gaya masa ba muyi zancen zuwa Gambia da ke ba"

Asiya ta rufe fiska cike da kunya.

"Kwantar da hankalinki, kafin ki zo na kira shi Saifuddeen É—in kuma ya amince zai bimu zuwa Gambia goben sai dai ban gaya masa dalilin tafiyar tamu ba"

"Kiyi haƙuri Hajiya kawai dai..."

"Miye na ban haƙuri kuma, ai abun a miki godiya ne, ni rabon na tuna da cewa iyayen mahaifiyar Saifuddeen mutanen Gambia ne ai na manta"

Haka Hajiya Umma tayi ta saka wa Asiya albarka da addu'ar samun zuri'a masu albarka

*

Ƙaran shigowan text yasa Asiya ta sake towel ɗin da take goge kanta da shi ta ɗauki wayar tana karanta amsar saƙon da ta tura, saƙon bai mata daɗi ba dan zama tayi dirshen kan kujera tana sauke ajiyar zuciya. Wai yanzu tsakaninta da Saifuddeen ne ya dawo haka.

Tunda dai ya bata izinin tafiya ai shikenan. Ta sake karanta text É—in a karo na biyu nan da nan ta ji hawaye ya zubo mata. Anya kuwa zata iya wannan abin.

"Ki je duk inda kike so ni Saifuddeen ba zan iya hana ki ba"

Ko dai ta fasa zuwa bikin nan ne, ko dai ta amince tabi su zuwa Gambia ne goben. Tambayoyin da ta ke yiwa kanta kenan har sai da kiran Agent Dahlia ya katseta.

*

Tunda aka yi masa maganar tafiya Gambia jikinsa ya bashi akwai alaƙar tafiyar da 'yanuwan mahaifiyarsa sai dai bai nuna wa Hajiya Umma hakan ba.

Da dare bayan ya gama duk wani abinda zai yi ya je gaishe da Alhaji Sani ko zai samu wani batu gameda tafiyar tasu amma har ya masa sallama ya tafi Alhaji Sani bai gaya masa dalilin tafiyar su ba. Abin ma ya bashi dariya wai da girmansa ana ɓoye masa inda zasu je kamar wani ƙaramin yaro.

Lokacin daya shiga gida a falo ya tarar da Bilkisu tana waya tana zuba masifa kaman zata tashi sama. Haka ya É—auke ido ya wuce sashinsa kaman bai ganta ba duk da kuwa yaji maganar da take yi.

A wani ɓangare kuma yana tunanin dalilin daya sa matar shugaban ƙasa ta gayyaci Asiya bikin 'yarta ba Bilkisu ba. A iya saninsa Asiya bata da haɗi da first lady. Daga baya kuma sai ya tuna cewa ai First lady ta koyar da ita lokacin da taje course a National Institute of Policy and Strategic Studies Kuru.

Bai gama kimtsawa ba Bilkisu ta shigo É—akinsa.

"Wani munafurcin ne yasa aka inviting Asiya zuwa bikin 'yar shugaban ƙasa. That invitation was mine"

Murmushin takaici yai dan duk cikin abubuwan da ke faruwa babu wanda ya ci mata tuwo a ƙwarya sai maganar bikin 'yar shugaban ƙasa. Lallai a gaishe da Bilkisu.

"Saifuddeen magana nake fa, na san kai ne ka ƙisa wannan munafurcin"

"Idan kina da matsayi a wajen first lady bana tunanin zata hana ki katin gayyata"

"Ya isa!" Ta ja tsaki ta fice daga É—akin

Wannan shine abinda suka zamo, wannan shine abinda kasancewarsa Gwamna ya haifar. Kafin ya zama Gwamna rayuwar aurensu akwai tarin matsaloli amma ya ƙwammaci rayuwar aurensu kafin ya zama Gwamna da yanzu. Wannan mata data daka masa tsawa, ta ja masa tsaki itace matar da yai rayuwar aure da ita na shekaru shatara.

Abin mamaki da takaici shine bayan shekaru shatara da aure har yanzu babu fahimta mai tsabta tsakaninsu.

Gwamna ya girgiza kai kawai ya maida hankalinsa ga kayan bacci daya ke shirin sakawa yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa.

***

Lokacin da suka sauka a babban filin jirgin ƙasar Gambia wato Banjul international Airport tuni akwai mototoci biyu dake jiransu.

Alhaji Malick Burama shine ya jagoranci tafiyar ta su. Shi É—in wani tsohon abokin kasuwancin Alhaji Sani ne dake Gambia. Alhaji Malick É—in ne ma ya shirya zama tsakanin Alhaji Sani Kachallah da iyalen marigayi Ousmana Jallow.
Cikin shekaru kusan hamsin Ahalin marigayi Ousmana Jallow sun kasance daga cikin masu faɗa a ji a cikin ƙasar, saboda kasancewarsu manyan 'yan kasuwa da kuma 'yan siyasa.
An haÉ—a zaman ne a katafaren gidan marigayi Alhaji Ousmana wanda yanzu an maida shi kamar gidan gona da ahalinsa ke ziyarta idan sun zo hutu.

Tunda suka iso gidan suka ci karo da dandazon motoci. Sanarwa ce aka yi cikin ƙanƙanin lokaci amma duk wani mai alaƙa da Alhaji Ousmana Jallow sai daya halarci wannan zama wanda yafi kama da taron biki.

A cikin mota dai dai zasu fita Alhaji Sani ya riƙo hannun Gwamna Saifuddeen yace " nan ne gidan kakanninka Saifu, nan ne tushen mahaifiyarka. Ka yafe min bisa tsawon lokaci da muka ɗauka ba tareda na kawo ka ba, ni kaina ba zan iya faɗin dalilin da ya sa na gagara yin haka ba duk da kuwa na jima ina son yin hakan"

Hawaye suka cika fal a idanunsa take yaji wani sabon shauƙi da soyayyar Babansa yana ƙara shigarsa. Ya san abinda ya kawosu kenan amma jin hakan daga bakin Alhaji Sani ya ƙara daɗaɗa masa rai.

Wasu mutane biyu ne suka zo suka shiga da su wani falo inda aka shirya za a gana da manyan gidan kafin a yiwa sauran 'yanuwa dake ta baya wajen wani hall da aka shirya taron bayani.

Tun kafin a fara bayani wani tsoho wanda a ƙalla zai yi shekara casa'in ya zo ya rungume Saifuddeen yana kuka, da yaren Fulatanci yake faɗin da gaske wannan ne jikan ɗanuwansa Ali Jallow. Da ƙyar aka samu aka raba su dan kusan kowa a wajen hawaye ya fara.

Bayan an nitsun ne kuma aka buÉ—e zaman da addu'a sannan aka fara gabatar da kai. Alhaji Sani ya gabatar da kansa da kuma Hajiya Umma a matsayin yayyen mahaifin Saifuddeen wato Sa'ad Kachallah wanda ya auri 'yarsu Aisha Ali Jallow kusan shekaru hamsin da suka wuce.

Tsohon nan da ya ke kuka ya saka kabbara yana É—aga hannu tareda godiya ga Allah.
Bayan an nitsu tsohon ya gabatar da kan sa a matsayin Alhaji Muhammadou Jallow yaya ga Ali Jallow, ya nuna É—anuwansa wanda ke zaune gefensa shima yana hawayen yace "wannan shine Yayanmu gaba É—aya sunansa Audoulaye Jallow" ya cigaba da nuna wasu 'yan uwan na su na kusa da su.

Basu san da haihuwar Saifuddeen ba, su abinda aka gaya musu shine Aisha da ɗan data haifa sun mutu. Wannan shine gaskiyar da suka riƙe shekara da shekaru.

Shekaru ishirin da biyar da rasuwan Ali mahaifinsu ya fara jinya, a lokacin ne kuma yake yawan sunbatu da cewa a nemo masa jinin Ali, a nemo masa 'ya'yan Ali. Basu fahimci mi yake nufi ba sai suka ɗauki hakan a matsayin tsufa ne kawai da kewar Alin daya dawo masa sabo. Duk da ya jaddada musu lallai a nemo masa ɗan Ali basu wani ɗau abin da mahimmanci ba a haka har Allah ya ɗau ransa. Sun ma manta da zancen shaɗaf sai da Boubacar Jallow zai rasu yake faɗin abinda ya aikata tareda nuna musu wasiƙar da aka turo lokacin haihuwar Saifuddeen. Boubacar shi yai wa Aisha sammu sannan shi ya sa aka kashe Sa'ad Kachallah.

Alhaji Sani ya zaro ido waje dan ya san ƙaninsa a hatsarin mota ya mutu. Alhaji Muhammadou bai tsaya da maganar sa ba ya cigaba da faɗin Boubacar ya kashe Sa'ad ne dan ya auri Aisha, sannan ya mata asiri ne dan ta dawo gida amma hakan bai yiwu ba.
Tunda mahaifinsa Alhaji Aoudulaye ya ji wannan zance ya fara jinya. Mun sa a ranmu da zaran ya samu lafiya zamu zo Nigeria mu nemi ɗan Aisha Allah mai ikonsa kwana uku da aka dawo da shi daga ƙasar Jamus muka samu kiran Alhaji Burama akan sirikin Aisha na son zama da mu akan ɗan da ta bari.

Alhaji Aoudulaye ya sake fashewa da kuka tunowa da yai da yadda Boubacar ya ƙare rayuwarsa cikin garari da son zuciya saboda abinda ya aikata. Ko kusa bai yi ƙarshe mai kyau ba. Ta inda Allah ya kama shi yadda ya zo haka ya tafi bai taɓa haihuwa ba, to inama zai haihun tunda ba auren yai ba.

Saifuddeen ya tashi ya matsa jikin Alhaji Aoudulaye ya rungumeshi yana kuka.
Cikin kuka Alhaji Aoudulaye yake faÉ—in Saifuddeen ya yafe musu.

Haka nan aka dinga jajantawa juna ana kuma taya juna murna.

A wajen liyafa da aka shirya kuwa 'yanuwa kaman zasu cinye Saifuddeen musamman ma 'yanuwan mahaifiyarsa mata (cousins) wanda suka taso tare.

Mutane dayawa na faÉ—in irin tsananin kamannin Saifuddeen da mahaifiyarsa wanda suka santa da kyau har cewa suke hatta murmushinsa irin nata ne.

Faɗin irin farin cikin da Gwamna Saifuddeen ya tsinci kansa a ciki ma ɓata lokaci ne. Wani ƙishirwa ne da ya ke fama da shi shekara da shekaru Allah ya kora masa ƙishin a rana guda ba tareda ya shirya ba. Duk da mahaifiyarsa da kakanninsa basa raye amma ya ga yayye da ƙannen kakanninsa tareda tarin 'yanuwan mahaifiyarsa wannan kaɗai ya wadatar da shi.
He was so happy da har ya manta duk wani fushi daya ke da matan na sa biyu dukkansu ya tura musu hotunan da ya yai da 'yanuwan mahaifiyarsa tareda tura gajeran saƙo a ƙasa.
Daga wajen Asiya ya samu reply mai daÉ—i inda ta masa fatan alkhairi da addu'o'i. Ita kuwa uwargida yi tayi kamar bata ga mi ya turo ba balle har ma ta maida masa wani martani gameda abinda ya turo. Bai yi mamaki ba duba da irin rabuwar da suka yi jiya.

***

Babu yadda za ayi ta bari a tozarta Alhaji Sani a wannan yanayi. Yace mata zai gabatar da kansa ga hukuma idan yai hakan zai samu sassauci a idon mutane da kuma ɓangaren shari'a.

"Wannan cin zarafi ne ai?" Asiya ta faÉ—a tana sake duba jaridar dake hannunta da kyau.

"Samfurin jaridar da za a fitar gobe kenan"

"CY? " ta kira sunansa da sigar tambaya, mamaki da damuwa duka lokaci guda.
Chapter 32 · 0% Book details