← Book details Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 48

Sashe 25

Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kin san kusan awa É—aya kenan kina zaune a wajen nan baki ce komai ba. Ban damu da abinda Gwamna yace miki ba, ban damu da Project Tomatonion ba"

Wannan furucin yasa Asiya ta juyo a fusace, idan har Badawiyya bata yarda da shirin da take yi ba kenan aikin banza take.

"Kema baki yarda wannan shiri zai kawo cigaba wa jahar nan ba?"

Badawiyya ta zauna gefen gadon tana fuskantar Asiya da kyau.

"Na yarda da alfanun dake shirin ɗari bisa ɗari. Sai dai abinda na fi damuwa dashi shine lafiyar ki. A gabana likita yace akwai stress a jikin ki, na yi wani course a fannin ƙwaƙwalwa kuma bisa hasashena kina fama da both emotional and physical stress. Tun rasuwan Junior nake lura dake, kaman kin sawa kan ki cewa idan kika samu ciki kika haihu hakan zai sharewa Gwamna rashin Junior

"Ina so ki sani cewa ko 'ya'ya goma zaki haifa ba zai cire raÉ—aÉ—in mutuwar Junior a zuciyar Gwamna ba domin ba mutuwar kaÉ—e yake ji a jikinsa ba har da kasancewar hannun matarsa a wajen mutuwar yaron. Dan haka ki cire wannan tunani a ranki, zaki samu haihuwa a lokacin da Allah ya rubuta miki. Amma idan har kika cigaba da tafiya a haka to kwannan zaki yanki jiki ki faÉ—i ki mutu"

"Badawiyyah!" Asiya ta zaro ido waje

"Gaskiya nake faÉ—a miki. Lafiyarki ta fi komai mahimmanci domin idan babu lafiya babu wani buri naki da zaki cimma a karan kan ki ko a jahar nan"

Asiya ta sunkuyar da kanta tana sauke wani nannauyan ajiyar zuciya. Chan kuma ta É—ago tace
"Nagode Badawiyya, haƙiƙa ke ɗin 'yaruwa ce ta ƙwarai. Nagode sosai" ta faɗa a hankali, kamar kuma an tsikareta ta fara magana cikin fushi

"A zahiri na ɗauka Gwamna yana da ƙarfin zuciyar da zai iya juran kowanni yanayi domin a samu cimma nasara mai ɗaurewa, ban san cewa zuciyarsa tana da rauni ba. Ban san cewa zai bari Bilkisu ta dinga juya tunaninsa a kowanni lokaci ba"

"Kar ki ce na katse ki amma ranki shi daÉ—e Gwamna bashi da laifi, ko ince laifinsa É—aya ne da bai iya siyasa ba"

"Amma Badawiyya..."

"Babu komai idan kika yi haƙuri zaki iya zama sandar jagoransa"

"Sandar jagora sai kace shi makaho ne" Asiya ta faÉ—a tana dariya
Badawiyya tace " a harkar siyasa shi makahone kece idanunsa"

"To ai gashi yana saka idanun nashi kuka"

Badawiyya ta ce "Shima zai ji a jikinsa ai"

GabaÉ—aya sai suka saka dariya...

***

A chan ofishin Bilkisu Kachallah kuwa Chief of Staff Mr Lamara Damana ne ke zaune yana jiran isowar Bilkisu office É—in domin lokacin da yazo ance masa ta fita. Dake sun yi waya yace yana hanya shiyasa ya zauna zaman jiranta.

"Boss akwai labari mai daÉ—i" abinda COS ya faÉ—a kenan dai dai lokacin da ta shigo office É—in.

"Labari me daÉ—i shine kace min 'yar matsiyatan nan ta mutu" Bilkisu ta faÉ—a tana zama akan kujerarta.

"Gwamna ya kashe Project Tomatonion, inaga a dena bawa Tanko Janwuya makamai for now kafin lokacin kamfen"

Wata shegiyar dariya Bilkisu ta fashe dashi.

"Wait a minute, Lamara Damana i highly respect you saboda basirar ka, amma ban san cewa ƙwaƙwalwarka ta mutu ba"

Daga yadda COS ya ɗaure fiska zaka fahimci ransa ya ɓaci da maganar Bilkisu Kachallah.

"Kana tunanin na ciro Tanko Janwuya ne daga kurkuku dan yazo yai barazana na kwana biyu yai shiru. We'll continue the supply kamar yadda muka tsara domin yanzu aka fara zubda jini a wannan jaha"

Cikin rashin fahimta COS yace " me kike nufi?"

Bilkisu ta kalleshi ido cikin ido tace "zan maida gwamnatin Gwamna Saifuddeen Kachallah gwamnatin mutuwa, gwamnatin talauci, gwamnatin Allah ya isa"

"Kina ganin Asiya zata zauna shiru idan kika yi ƙoƙarin yin hakan?"

"Asiya bata san Saifuddeen ba. Ni na san waye Saifuddeen. Saifuddeen cannot stand people dying under his government... because he's a coward"

" kar kiyi gaggawar faÉ—in haka. Saifuddeen ya chanja fiye da yadda kika san shi..."

"kwanan nan Saifuddeen zai yi murabus daga kan kujerar sa"

COS yai ƙaramar dariya yace "mi zai faru idan yaƙi yin murabus?"

Shiru Bilkisu tayi na tsawon mintuna har sai da COS yai tunanin bata da abin faɗa. Sai kuma ta miƙe daga kujerarta ta ƙariso gabansa ta matso daf da fiskarsa tace " Saifuddeen Kachallah zai ƙarisa rayuwarsa da shanyewar duka jikinsa"

COS ya zaro ido waje.

"Mr Lamara Damana na san baka taɓa jin labarin anyi paralysed Gwamna ba ko?"

Kan Lamara Damana ya kulle da wannan batu. Wani alfanu Bilkisu zata samu idan Saifuddeen ya bar kujerar Gwamna. Matar tsohon Gwamna ai bata da wani daraja.
Kamar ta karanta abinda ke ransa sai tace " ina son rubuta tarihi a jihar nan. Ina son zama Deputy Governor na wannan jaha. Na san kasan mi zai biyo baya idan hakan ya faru"

"Boss Lady ba lallai..."

"Ni Bilkisu Kachallah zan zamo Gwamna a jahar Congo. Ni Bilkisu Kachallah zan zamo mace ta farko da zata zama Gwamna a jahar Congo"

Kamar COS bai ji mi tace ba ta ƙara ɗaga muryarta tana faɗin " I am going to be the governor of this state Mr Damana, just wait and see"...

***

A dai-dai gidan kurkuku dreban Asiya yai parking mota. Asiya ta fito daga motar fiskarta sanye da baƙin nose mask, shigar baƙar jallabiya tayi da gyale kalar ruwan ƙasa ba abin da kake gani sai kyawawan idanunta wanda suka ƙanƙance saboda rashin bacci.

Babu abinda ya chanja a gidan kurkukun, yadda ta san shi haka nan yake. Warden Bisola ce ta raka ta É—akin Madam Chess a nan dai É—akin da suka zauna lokacin da tayi zaman kurkuku.

"Ke da zaki sa a kirani mu gaisa"

"Mommy ban isa na sa a kira ki ba, nan ma ai gida ne"

"Inaaa! Ke yanzu kina da 'yanci ba abinda zai haÉ—a ki da gidan nan"

Bayan sun gaisa Asiya ta ce " Mommy kai na ya kulle, ina buƙatar shawaran ki"

Madam Chess ce tace " let's play a game"

Asiya tayi murmushi tace " yanzu kam zaki sha mamaki Mommy dan nima na zama pro"

"Bari dai mu ga"

Sun kai kusan minti shabiyar suna game É—in amma kuma babu wanda yaci wani.
A minti ashirin da uku Madam Chess ta cinye Asiya a wasan.

"Checkmate your Excellency"

Asiya ta kama kai tana duba board É—in da kyau, tabbas an cinyeta a wasan

Madam Chess tayi murmushi tace "kin yi ƙoƙari ai, sai dai ki sani ba a sarki biyu a fada ɗaya"

"Mommy dan Allah ki min bayani na fahimta"

"Ki tashi mata daga fadar ta. Build your own palace, build your own empire. Ki gina tsauni tsananin ku wanda ko ta hau gajimare ba zata iya tsallakawa fadar ki ba."

"Na bar mata gidan Gwamnati kenan?"

Madam Chess ta ɗau kofin dake gefenta ta kurɓi maltina da aka kawo musu...

Asiya bata gama fahimtar maganganun Madam Chess ba sai da ta je gida suka tattauna maganar da Badawiyya. Inda suka yanke shawaran barin gidan Gwamnati su koma chan gidan Saifuddeen.

Koda ta yiwa Gwamna magana bai musa mata ba musamman data nuna masa tana so tayi amfani da filin dake bayan gidan ne wajen yin wani aiki.
Bai san wani irin aiki bane amma dai ya bata goyon baya É—ari-bisa-É—ari.

Tun kafin a gama kwashe kayan Asiya Bilkisu ta samu labarin Asiya zata koma É—aya gidan. Wannan yasa ta fara tunanin dalilin da zai sa Asiya ta bar gidan Gwamnati rana tsaka haka.

**

"My Governor lafiya?" M Sani ya tambaya ganin tunda Bilkisu ta gama amsa waya ta shiga tunani.

"Nothing, na ga kamar akwai nasara ne a shirin mu, yanzu aka ce min 'yar matsiyatan nan zata koma chan gidan Saifuddeen"

"Dole mu sa'ido akanta sosai dan dole akwai dalilin da zai sata barin gidan Gwamnati bayan a da ƙoƙarin fitar dake take daga gidan"

"Ba abinda zata iya yi a bayan idona, duka ma'aikatan gidan ni suke yiwa aiki"

*

A natse Asiya take yiwa Badawiyya bayani kan yadda tsarinsu zai kasance daga yanzu.

"Badawiyya yanzu ne za a fara yaƙi, yanzu ne za ki ɗau fansar abinda Madam Bintu ta miki, yanzu ne rayuwar mu zata shiga haɗari saboda idan muka fara wannan yaƙi babu gudu ba ja da baya"

"Na sani"

Asiya ta ɗauko ƙaton kwalban turarenta ta ajiye a tsakiyar table tace wannan itace Bilkisu Kachallah.
Ta ɗauko janbaki, eye pencil da wasu brushes tace "waɗannan sune muƙarrabanta da kuma ƙarfinta.
" Mr Lamara Damana shine na hannun damanta shine ke kawo mata duk wani information daga ofishin Gwamna. Tana amfani da kamfanin Madam Bintu wajen shigo da muggwan ƙwayoyi and ina zargin harda makamai ma. Wannan shine Alhaji Sani Kachallah shine mahaifinta kuma da sunan sa take tinƙaho. Wannan kuma Muhammad Sani ɗan yayarta wanda yake mata duk wani dirty work ɗinta"

"Who do we strike first?" Badawiyya ta tambaya idanunta cike da É—oki

Asiya ta kalli Badawiyya tace " idan aka kama Madam Bintu da evidence dake hannunmu Bilkisu Kachallah zata yi watsi da ita zata ma yi ƙoƙarin kasheta saboda kada ta tona mata asiri. Zamu yi amfani da wannan dama wajen samun wasu shaidu na Bilkisu daga bakin Madam Bintu"

"Amma ya zamu yi da Muhammad Sani? yaron fa yana Asibiti har yanzu"

" kar ki damu ai gobara biyu zamu kunna"

Badawiyya tayi murmushin jinjinawa...

***

Yayinda shirin Project Tomatonion ta sukurkurce cikin ƙanƙanin lokaci tun ma ba a mori shirin ba. Mutane nata Allah wadai da Gwamnatin Saifuddeen Kachallah saboda ta kasa cika alƙawari, ga uwa uba rikici da ke ƙoƙarin cinye kudancin jahar.

A cikin wannan yanayi ne kuma Asiya ta fara gudanar da shiri a gidan talabijin mai suna ASIYA'S GARDEN. Da farko youtube channel ta buɗe take ɗaura shirin a kai sai daga baya ta nemi a saka shirin a TV. Shiri ne da take yi dan encouraging urban farming. Ta nuna cewa ko a gidan haya kake zaune zaka iya fara shuka wasu abubuwa masu sauƙi kamar su timatir, Albasa, Alayyaho, dankali da sauransu. Ta nuna yadda za ayi amfani da bokiti, tayar mota da kuma buhu wajen fara yin shuka.
Chapter 25 · 0% Book details