← Book details Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 48

Sashe 4

Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Madam Chess na zaune akan katifarta tana lura da yadda Asiya ke ta sheshsheƙar kuka daga inda tayi sallah.
Bata yi niyyar yi mata magana ba amma kuma wani zuciyar na ingizata akan ta faÉ—a mata wani abu ko za ta dena tunanin ita kaÉ—ai ce ke da matsala a wannan gida.

"Kina kuka saboda kina amsa laifin da ba ki yi ba ko?"

Asiya ta yi shiru dan ƙarshen maganar kawai ta ji.

"At least na ki case É—in za a iya gano gaskiya nan bada jimawa ba a wanke sunanki"

Wannan karan Asiya miƙewa ta yi ta juya tana kallon Madam Chess duk dama hasken lamp ne a ɗakin dan babu wuta. Ta ɗauka matar kurma ce saboda tunda ta shigo ɗakin ba ta ji ko tari daga gareta ba balle magana.

"Wasu sukan ƙare rayuwarsu a nan gidan ba tare da sun aikata laifi ba, wasu kan mutu a haka, wasu kuma saboda wannan trauma ɗin har su mutu ba za su taɓa zama dai-dai ba.

"Kina ganin zaki shekara goma a kurkuku ne?"

Asiya ta buÉ—e baki zata yi magana amma ta rasa abin faÉ—a.

"Ki kwanta kiyi barci, kukan da kike ciwon kai da hawan jini zai sa miki ba zai chanja fate É—in ki ba"

Daga haka sai ta rufe littafin hannunta ta ajiye a gefe ta kwanta.

Asiya ta jima tana kallon Madam Chess kafin itama ta je ta kwanta a ƙaramar katifar da ke gefen katifar Lauratu...

3

Mai Matarba Sarkin Congo bai samu amsa kiran first lady Bilkisu Kachallah ba, sai ya aika mata da wakilinsa wato Galadiman gari. Wannan abu da yai ya sosa ran Bilkisu dan a ganinta indai Gwamna nada ikon ya kira sarki ya zo to itama tana da wannan damar.

Haushi yasa bata sanar da Galadima ainihin dalilin kiran Sarki da ta yi ba. Ta dinga tufka da warwara kan yadda zata ɓullowa wannan lamari ƙarshe ta yanke hukuncin tana dawowa daga tafiyar da zata yi zata je fadan da kanta ta faɗawa Mai Martaba abinda take so...

Gwamna yana zaune a falonsa yana duba wasu takardu ya ji sallamar mace. Saura kaɗan ya kira Asya saboda ji yai kamar irin sallamarta. Ganin ƙanwar matarsa sai ya sake fuska yana murmushi.

"Yaya fushi sosai nake da kai, shikenan yanzu idan mun kira ka ba zaka É—auka ba kenan. Da dai na san Yayanmu ba haka yake ba"

"Sadiya kenan, na isa na share kiran ki"

Ya faÉ—a yana duba wayar sa sai gashi missed calls É—inta har uku.

"Kiyi haƙuri Wallahi wayar a silent take saboda ina aiki"

"Ba wani, tun kwana huÉ—u da suka wuce nake kiranka baka É—auka, yanzu ma Mahira na kira tace min kana gida shiyasa na zo"

Gwamna ya haɗa hannunsa biyu yace "Afuwan ƙanwata, kwana biyun nan aiki ya min yawa be"

Zama ta yi kujerar da ke opposite ɗinsa, ta ajiye jakarta a ƙasa sannan suka fara gaisawa. Duk cikin cousins ɗinta maza kai har matan ma Saifuddeen kaɗai ta yarda da shi kuma ta saba da shi har suke mutunci sosai duk da kuwa basa jituwa da matar sa.

"Yaya ba maganar siyasa ya kawoni ba, dan na san kai kanka ka san people are dissapointed in your Government"

Gwamna ya sauke ajiyar zuciya yana kauda kansa daga kallon Halima Kachallah.

"Maganar Anty Asiya na zo yi. Yaya Saif i've being going to Congo prison tunda aka kaita chan amma duk lokacin da naje sai a hanani ganinta. Mi yake faruwa ne wai?"

"Sadiyyyaah"

"Na san kai Gwamna ne but shikenan idan kai ba zaka je ka dubata ba sai muma ba za a bari mu ganta ba. This is cruel gaskiya. Ni yanzu zuwan da nayi na zo ka rubutamin permission ne a barni na ganta duk lokacin da na je dubata"

Nana ce ta shigo falon da gudu kamar wacce aka korota.

"Daddy Yaya Bello yace na kawo maka key"
Maimakon ta bashi key ɗin a hannu sai ta jefar da shi ya faɗi gefen ƙafarsa.

"Haba Nana, idan kika same shi a ƙafa yanzu mi zaki ce"

"Anty Halima ba ki san ina buga basket ball ba, na san ba zai same shi ba ai"

Halima ta riƙe baki tana mamakin wannan kalar rashin tarbiyyan.

Gwamna ya É—auke zancen da cewa "Nana kira min shi Bellon"

Har ta fice daga falon Halima bata dena mamakin Nana ba. To dai ita ance mata tunda ta dawo daga Rehab center ta chanja amma gaskiya bata ga chanji ba indai wannan ake kira da chanji.

Minti uku sai ga Yaya Bello ya shigo. Halima na ganinsa ta fara murmushi tana faÉ—in "Yayanmu"

Yaya Bello ya zauna a ƙasa yana gaisheda Gwamna.

"Bello na ga ka aiko da key É—in mota na miye kenan?"

"Allah ya ja zamanin ka, zan koma ƙauye ne, dama Asiya ce ta ɗaukeni aiki kuma bata nan"

"Ayi haka kuma. Ya kamata ka zauna ka dinga kai su Sumayya makaranta"

Yaya Bello ya sosa kai yace " Mai girma ai Sumayya ta koma cikin makaranta da zama "

Kunyar kansa ya ji kan rashin sanin halin da ƙannen matarsa suke ciki.

"Ka riƙe key ɗin, akwai aikin da zaka min nan bada jimawa ba"

Gwamna ya sa hannu ya ɗau key ɗin ya miƙawa Yaya Bello.

"Yayanmu idan aiki kake nema zan baka aikin tuƙi, dama kwana biyun nan idan ina tuƙi sai na dinga jin ciwon kai"

Yaya Bello yace "to ai ni Dreba ne ba Likita ba. Dreba na maganin ciwon kai ne?"

Mi Halima zata yi banda dariya. Gwamna ma sai da ya É—an murmusa.

Lokacin da Yaya Bello ya miƙe zai tafi Halima tace " Dan Allah ka jirani idan na gama da Gwamna zamu kaiwa 'yar uwarka ziyara"

"Da gaske?" Yaya Bello ya faɗa cike da ɗoki. Yayi kewar ƙanwarsa ba kaɗan ba.

"Allah" Halima ta kwaikwayi maganarsa

Bayan tafiyarsa Halima ta kalli Gwamna ta ce " Your excellency ka rubutamin permit É—in"

Gwamna ya ce ina zuwa.

Shigewarsa ɗaki keda wuya Alhaji Abdullahi ya shigo falon sai wani ƙanshi yake ta zubawa.

"Haly dubu" ya faÉ—a ganin Halima zaune tana danna waya.

Firgigit Halima ta yi ta miƙe tsaye tana dafe ƙirjinta. Jikinta ya shiga ɓari saboda sunan daya kira ya tada tsohon gembo.

"Manyan mutane kenan, ke ba a ganinki ma yanzu sai an yanki ticket. Miye sirrin ne na ga kin yi wani fresh fa"

Alhaji Abdullahi ya faÉ—a yana kashe mata ido.

"Haly dubu lafiyanki?"

Ya faÉ—a yana matsowa kusa da ita.

"Don't touch me, don't touch me, don't touch me" ta fara faɗa da ƙarfi saida Alhaji Abdullahi ya ja baya a tsorace.

"Sadiya? Are you ok" Gwamna ya kira cike da damuwa.

Gyaɗa masa kai ta yi ta zauna tana haɗa hannayenta da suke ɓari.

Jiki a sanyaye Alhaji Abdullahi ya kalli Gwamna yace " it seems na zo a bad time, dama maganar bikin 'yarka ce, na zo na ƙara jaddada maka cewa sati mai zuwa ne, ba zan karɓi uzurinka ba, you have to be there"

"Of course, taya zan missing auren 'yata"

Alhaji Abdullahi ya kalli Halima yace " ni kam Halima yaushe zaki kawo mana angon ne, gashi duk 'ya'yanki suna ta tafiya gidajen mazajensu

Hawayene ya fara silalowa a idanun Halima Kachallah. Taya Abdullahi zai samu nasara a rayuwarsa bayan abubuwan daya aikata. Taya zai samu damar aurar da 'ya'yansa bayan ya ɓata mata rayuwa. Taya nashi 'ya'yan zasu samu miji amma ita ta rasa. Taya zai iya buɗan baki ya mata gori bayan ya barta da gembon da har yau tana jin raɗaɗinsa.

Shekaru ashirin da huÉ—u da suka wuce ba zata manta ba, koda shi ya manta. She was a kid, she was just 9years.

"Haly dubu" sunan daya ke kiranta kenan a lokacin har ta sake da shi a matsayin babban Yaya. Ba sau ɗaya bane, sau biyar, sau biyar ya mata abinda ko maƙiyinta ba za ta so aiwa 'yarsa haka ba a wannan shekarun.

Aljanu aka ɗauka suka shafeta aka dinga neman magani har Maiduguri kafin daga baya Hajiyan Saudiyya ta tafi da ita wani zuwan da ta yi, lokacin shi Abdullahi baya ƙasar ya tafi masters na shi. Sai da ta shekara biyar a Saudiyya kafin ta fara dawowa dai-dai.
Akwai lokutan da ta tsani maza gaba É—aya, akwai lokutan da ta ce ba za ta yi aure ba saboda ganin maza take tamkar Abdullahi.

Idan shi ya manta komai ita ba zata manta abinda ta fuskanta tana shekara tara ba.

Jakarta ta É—auka ta fice daga falon. Gwamna yana kiranta amma bata kulashi ba.

Bayan fitar ta. Gwamna ya harari Alhaji Abdullahi yace "Allah ya shiryeka, ban san yaushe zaka girma ba. Taya zaka faɗa mata irin wannan magana kasan halin da take ciki. Son ranta ne ta ƙi auren?, ko ka taɓa kawo mata miji tace maka bata so?"

Alhaji Abdullahi yai shiru yana jin zafin abinda ya aikata a shekarun ƙuruciyarsa. She was 9 or 10 ba zai iya tunawa ba yanzu, amma ya san laifin daya aikata, he violated her when she was just a child.

Fitowan da Halima Kachallah ta yi cikin kuka zuwa shigewarta mota duk akan idon Yaya Bello ne. Koda ta shiga motar kifa kanta tayi a steering tana kuka. Dadda ta sani kuma ta faɗawa Babansu amma a lokacin sai cewa yai idan Haliman ta ƙara girma zai sa Abdullahi ya aureta. By the time Halima ta gama sakandare matan Abdullahi biyu. Lokacin da Halima ta ƙare degree ɗinta na farko sai Dadda ta sake yiwa Babansu tuni akan alƙawarinsa amma daya tuntuɓi Halima da maganar cewa tayi idan aka aura mata Abdullahi kashe shi zata yi ta kashe kanta shiyasa aka rufe maganar. Har Dadda ta rasu rashin auren Haliman na damunta musamman idan ta tuna abinda Abdullahi ya mata wacce itama bata sani ba sai a lokacin da ake yawon neman magani bayan abin ya faru da kusan satuttuka ma.

Yaya Bello ya fara buga glass ɗin motar Halima hakan yasa ta ɗago a firgice. Ƙoƙarin goge hawayen ta yi sannan ta sauke masa glass ɗin ta ƙaƙaro murmushi tace "Yayanmu"

"Hajiya Halima kina lafiya kuwa?, miya sameki kike kuka?"
Chapter 4 · 0% Book details